Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 42

Tunda gida zasu dunguma su tafi ba har Sa’adah da momyn tunda Mahmoud din zai dawo ai zasuje can ayi magana
Wlh bazata Sabu ba ko kadan,
Zainab bazai yiyu su saka Mata ido tabar yarinya tayi watsi da dangin uwarta ba,

Waccar samun wahala wato Laylan sun samu ta fita rayuwarsu tunda Ms Na’ima ance ta tafi da ita sunsan aikin wahala kawai ya Isa ya juyar da sauran qanqanuwar lafiyar qwaqwalwarta.

Sa’adah Bata gida ta fita karban wani sako a school Dan hakan ma suke zaune palon Anne da tuni ankaisu palon Sa’adah din
Dayake kusan bankwana Suka taho yi tareda Jin idan tareda Sa’adahn zasu tafi tunda abbansu dai dawowa zaiyi Dan Haka suka dasa sabon zaman jira,

Anne sakawa Tai halima takaisu palon Sa’adah Dan su sake yanda yakamata kafin dawowan Sa’adah din.

Tun Rana suke jiran dawowarta har kusan yamma batadawoba
Momy tayita Kiran wayarta Bata dagawa
Anne ma tayita Kira itama Bata dagawa.

Momy ce tafara Shiga damuwa sai Anne sbd magrib da aka fara Kira sbd tun dawowar Sa’adah hannunta Bata tana fita takai dareba a waje da sunan makaranta saidai idan biki ta fita kokuma tare suka fita sukai daren
Dan Haka take tasan ba lafiya ba.

Hankalinsu tashi yayi sosai Anne tafara kiran wayoyi tana tambaya ko Sa’adahn na can,

Momy tsabar tsoro da damuwa bin Anne kawai take da Ido tana jiran Jin labari Mai ma’ana Amma Babu inda ba’a buga wayaba da ake tunanin samunta acan saidai Bata can din.

Tashin hankalin dasuke ciki zuwa yanzu yagama girmama sbd har qarfe Taran dare ba labari Mai.

Kokarin Kiran M Kabir tsohon Secretary din Turaki tayi ta sanar Masa abinda yake faruwa yace Mata gashinan zuwa yanzu.

Kafin ya iso gidan yafara shigarda missing complaint sai gashi tun kafin ya isa gida aka sanar Masa ansamu accident tunda Rana na wata motar data buge motar wata budurwa.

Bai Isa gida ba Saida yaje ya tabbatarda Sa’adah ce,

Ita din ce saidai Kam tanajin jiki sbd ta bugu sosai qafafunta da hannunta dama kanta duk bandage ne
Qarin baqin cikin abin Wai Wanda sukai hakan sun tafiyarsu ba’a kamasu…. Saidai baya tunanin guduwa sukai yafi tunanin koma su waye sunada kudi sun biyane Ana barsu sun tafiyarsu ake cewa sun gudu.

Su Anne yakira ya sanar musu halinda ake ciki
Take jikin Momy ya mutu sbd yanda takeji azuciyarta gameda lamarin tasan akwai masifar da zata sameta…

Suna Isa asibitin kallo daya Momy tayiwa Sa’adah takasa riqe kanta wasu hawaye masu tsananin zafi suka balle Mata ta share tana kokarin Kame kanta sbd Anne data bayyanarda damuwarta Mai tsanani a fili Kan al’amarin,

Haj Karima kuwa cewa tayi sai an Nemo wainda sukai wannan hadarin Dan bazai yiyuba ace sun gudu ba dalili bane.

Cikin gaggawa aka sauya Mata daki raga emergency din dasuka sameta.

Suna cikin wannan tashin hankalin su Turaki Suka sauka Nigeria tsakar Daren.

Gida aka kaisa direct bayan ankai Abba lafiyayyar masaukinsa.

Dole Momy ce aka Bari ta kwana a asibitin su Anne Suka koma gida
Haj Karima ma ta wuce gida.

Washe gari tunda Turaki da kansa yakai Abban asibiti
Yakuma qi sanarda Laylah abin daya samu Sa’adah.

Sauyawa Sa’adah asibiti akai washe garin aka maidata asibitin dasuke zuwa..

Bayan sun fito yashiga mota ya zauna ya Dan dago tareda kallon A Abdoul dake gaban motar zaune cikin kamewa da murya Mai daukeda girman kamewarsa yace”

Abincika komai akan wannan abun daya faru sbd ance ko kwanaki mota tayi kanta,
A bincika komai inason sani.

Gyada Kai A Abdoul yayi Yana cewa”

Inshallah.

Barin asibitin sukai Suka nufi gurin wasu baqinsa dazai gani Dana abbansu Laylan yabar Masa Mota daya da drivern dazai maidasa masauki idan yagama.

Dr faruk daya dubata last time shine yanzu ma take hannunsa Dan Haka ya kalli Anne da zata wuce gida yace”

Anne akwai wasu result dinta na farko da basa cikin folder dinta inaga last time dasu kukaje gida Muna buqatansu Dan result dinta na yanzu munason duba wani abun.

Ok ba damuwa inaga suna cikin handbag dinta da akazo asibitin da ita last time din zansa aduba sai akawo Inshallah.

Ok, sai abada da wuri Muna jira Dan treatment dinta zai tsaya saimunga wancan result din.

Anne na Isa gida dakin Sa’adah tafara wucewa direct tafara duba handbags dinta daya bayan daya.

Kasa ganin komai tayi Dan Haka ta nufi drawers tafara dubawa Suma.

Nanma bataga komaiba dan haka ta nufi wardrobe dinta ta bude tafara dubawa.

Handbag dinta daya tagani kicin kayanta a boye Dan Haka ta janyo tareda budewa ba Bata lokaci taga takardun asibitin aciki..

Ta kwaso ta fito dasu gabaki daya tasaka a handbag dinta kafin ta nufi bedroom dinta.

Sai dare suka tafi Kai abincin dare asibitin itada halima.

A dakin Suka tadda Abba da momy sai Haj Karima da zuwanta kenan itama tareda umma Da tuni ta iso garin yau Dan Shiga al’amarin tunda Turaki na qasar yagansu ya Sansu amatsayin dangin uwar matarsa.

Cikin girmamawa sukewa Anne barka da zuwa tana amsawa cikin yabawa karamcinsu,

Takardun Datazo dasu ta kalli halima tace”

Halima bawa Dr faruk takardun gasunan.

Dr faruk karba yayi ya fice daga dakin Dan dama yagama abinda zaiyiwa Sa’adahn data farka Amma Bata iya magana ko kadan sbd azabar ciwon da kanta keyi.

Minti hudu da fitar Dr faruk ya dawo dakin daukeda folder din Sa’adah ya Ciro wata takarda yana kallon Anne dake kallonsa ganin ya dawo
Kowama kallonsa yakeyi suna jiran Jin Mai zaice ya miqawa Anne takardar Yana cewa”

Wannan inaga ba nata bane Dan a cikin namu gwaje gwajen bamu samu ciki a jikinta ba…..

Tsit sukai gabaki daya dakin suna kallonsa,

Anne da Momy da Abba dasukasan batada aure da mamaki da suke kallonsa,

Umma Jamila kuwa cikin kasa boye halin data shiga tayi saurin cewa”

Takardar ciki ta nuna ita ko me?

Miqawa Anne takardar yakuma Yi ganin tana Masa kallon buqatan qarin ya kalli sauran Yan dakin yaga duka iyayen Sa’adahn ne ya maida kallonsa kan Anne cikin nutsuwa yace”

Takardar pregnancy test ne tareda scanning Amma banajin nata ne sbd ba’a qasar Nan akaisa ba,
A America ne,Los Angeles….

Anne najin hakan ta karba takardar da sauri ta karance tsaf taga abinda yake ciki da sauri ta dago ta kalli Sa’adah Dake zaune tanajinsu Bata iya cewa komai sai rufe Ido datai cikin yanayi na rashin abin Yi.

Qamshin Bois elite ne yafara shigowa dakin Abba da Anne dasukan asalin waye Mai wannan qamshin Suka kalla kofa kafin shigowarsa
Tukuna ya shigo A Abdoul na bayansa
Dukkaninsu suka waiwayo suka kallesa yaqaraso cikin tsananin kwarjininsa daya Hana su umma Jamila tada hayaniyar murnar batun ciki da ake lokacin….

Haj Karima ce tayi qarfin halin gaidasa tana maida kallonta Kan Anne Baki washe tace”

Barka da arziki,
Ashe ciwon dai harda juna biyu ajikinta,
Allah ya raba lafiya yasa anbude hanyar tara zuria kenan…

Kujerar da A Abdoul ya gyara Masa ya zauna Yana kallon Abba dake neman rudewa da zancen da ake…

Anne ganin Kar rashin fahimtar tayi yawa ta bude Baki tana dauke kallonta daga kan Turaki daya Gama cika musu Ido dakin da kwarjini tace”

Ba sunan Sa’adah ne ajiki ba, takardar ba tata bace sbd ba komai ajikin Sa’adah.

Miqawa Turaki takardar tayi tana cewa”

Duba kagani ko zaka gane sakamakon waye.

Karba yayi tareda Dan kallon takardar akan sunan Mrs AB TURAKI idonsa yafara sauka kafin ya kalla date din jike jikin takardar.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button