Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 44

*_Mamuhgee 44_*

Anne shiru tayi Bata sake tada maganar al’amarin takardar cikin ba sbd batasan wa zata Kama zancen dashiba,

Sa’adah dai batace komaiba sai cewa ba nata bane Haka kawai tace musu tabarsu a duhu,

Momy Bata damuba sbd tasan Babu abun daya hada sa’adahnta da wani zancen ciki Dan Haka itama tayi watsi da zancen tunda cikin Laylan Bai shafeta ba.

Abbansu ma share zancen yayi sbd Ganin Anne batace komaiba Kuma yasan tarbiyar yaransa daidai gwargwado duk da yajima baya taredasu

Amma tunda yanxu tarbiyarsu a hannun Anne take bashida ta cewa Akan maganar yabar zancen tunda yasan sunsan abinda suke.

Umma Jamila ce ta daga hankalinta Kan ayi maganar qarshe Sa’adah da kanta tace”

Ba’a son tada zancen ne sbd matar Turakin Ms Na’ima da ake gudun fitinarta.

Wata dariyar bin iska Umma Jamila tayi tana cewa”

Akwai Wanda ya Isa aji shakkarsa akan samu da qaruwa daya samemu na farin ciki,

Ita Ms Na’iman inace da Turakin take takama? To shine ake wani boye boyen karta sani.

Haj Karima dake Shan tea ahankali cikin nutsuwa da takama tace”

Sune sukasan wata Ms Na’ima

Mu abunda yake gabanmu mukeyi,

Ciki dai tunda Allah ne ya badashi ai Babu wata Na’imar dazata sakamu kame kamen rashin fadarsa.

Cikin sanyi Sa’adah Dake sin plantains ahankali tace”

Wlh tanada ban tsoro mama,

Komai zata iya,

Dan Allah abar maganar shine yafi zama alkhairi..

Tsoronta kike kenan? “” Cewar haj Karima tana kallon Sa’adahn a zube.

Ba boye boye tace”

Eh wlh Ina tsoronta mama,

Nasan komai zata iyane.

Umma Jamila ce ta kalli Momy dake saka kayanta cikin akwatinta sbd tafiyar da zasuyi Dan ansallamo Sa’adahn suna gidan Haj Karima daga Nan zasu wuce gabaki dayansu duk da sai Sa’adah Takoma gida ta dauko kayan da zatai tafiya dasu,

Cikin mamaki da takaici tacewa Momy”

Yanzu Zainab Haka Kina kallo Kika koyarda Sa’adah tsoron kishiya?

Sbd ke Taki zuciyar ta mutu gurin jinyar mijin daya zaba Taki kishiyar akanki da yarki shine Zaki kashewa yarinya zuciya da tsoron kishiya kina kallo harda bakinta take fadar tsoronta takeyi.

Rashin Jin dadin maganar da ake fadawan Momy yasa Sa’adah kallon Momy da batace komaiba ita sai shiru datai tana cigaba da shirya kayanta cikin akwati,

Ta maida kallonta Kan umma Jamila dake fada cikin takaici zatai magana Haj Karima ta katseta da cewa”

Yi mana shiru mutuniyar banza,

Shiyasa kika kasa gaba Kika kasa baya acikin gidan,

Kinkoma tamkar Yar riqo a gidan ma Matar gidan ba,

Tsabar rashin yanci a bangaren Mahaifiyarsa aka Baki Palo da daki

Bayan ita tanada makeken bangaren guda a gidan da zata aje irinki guda nawa,

Drivers ke janta da motacin Alfarma tana yawo a agarin Abuja da wajenta Amma ke kece kike tuqa kanki Dan kina ganin ansiya Miki tsadaddiyar mota bayan motocin Turakin da ake fita da ita cikinsu daya zata siya biyar din Taki harda canji Mai yawa…

Umma Jamila da Shirun Momy ke Bata ranta ko yaushe tace”

Ahaka me tasamu bare mu iyayenta muce ‘yarmu na auren Amb AB TURAKI,

Alhaji Qarami Babu shige da ficen da bayayi Dan yasamu ganin Turaki shida honourable kwangila sukeso kamar me ko manyan kudi zasu saukar musu Amma koyaushe yarinyar Nan cewa takeyi baya qasar

Ashe tsoron zuwa gurinsa take sbd kishiya,

Wlh Allah yayi wadaran naka ya lalace.

Yanzu dai tagama wannan shashancin mutafi ai muma lokacinmu yazo Dan idan muka tafi zamu bude namu asusun lissafin agurinsa tunda ga ciki

Kafin ki dawo saikin haihu tunda ba qasar yake zamaba Kuma kingama karatun ai dama Dan Haka muma Bismillahi.

Daga Sa’adahn har momy Babu Wanda yasake cewa komai,

Suna sauraron su umma Jamila nata musu fada kokuma fade da gorin dawainiyarsu dasuke Dan taimakawa tun lokacinda Sa’adahn na qarama da Abban baya wani zama har lokacinda yake jinyarsa sune suke Dan taimaka musu.

Har dare daga ita har momyn Basu huta da fadan umma Jamila ba Saida Haj Karima ta tsayar da zancen da cewan ai yanzu tunda Sa’adahn na hannunsu zasu qaru da Turakin.

Da wannan umma Jamila ta sarara musu har drivern Anne yazo ya dauki Sa’adah a gidan Suka tafi gida.

Tana Isa gida komai na dakinta halima ta gyara ko’ina sai qamshi da sanyin AC ke tashi Bata wani zauna ba ta shige ta kwanta sbd kunyar Anne takeji batasan Mai zatace Mata gameda cikin Nan da Allah yayi bayyanarsa gaban kowaba,

Takardar acikin hanbag dinta dasukaje asibitin tun wancan lokacin take Kuma tunda tadawo take boye hanbag dinma gabaki daya sai ranarda zata fita ta janyota ta fita da ita Kuma ranar ne tsautsayi yahau kanta har tayi murnar Babu Wanda yagani a jakar shiyasa takuma boye jakar sai yanzu Allah yanufa zancen zai fita,

Kunyar Anne datake ji shine na boye Mata itama Basu fada Mata ba bayan ta cancanta tasani sbd yanda ta daukesu tamkar jininta

Kuma tasan idan Annen tasani Babu yanda zatai tabari a cutatar da Laylan gashi rashin wayonsu yasa tasamu zancen daga sama gashi taqi cemata komai akan zancen

 tamaqi tayarda zancen tayi kaman ba’ayiba.

Kwantawa tayi tareda neman numbern Laylah wadda yanzu laulayinta yafara yawa ba komai take iya ciba sai fruits datake Sha kaman me,

Ringing wayar taitayi baa dagaba Dole ta hakura ta qyaleta.

Washe gari jirgin safe zasubi Dan Haka tunda safe ta tashi ta shirya Kaya cikin qaramar suitcases guda biyu ta shirya tafito sbd driver na jiranta zai kaita gidansu Haj Karima dagacan zasu dauka su umma Jamila su wuce airport Abba daban zaiyi tafiyarsa ba taredasuba saiya gana sosai da Amininsa duk da kusan kullum tunda suka zo Abujan suna tare.

Anne cikin kulawa Tace Mata ki kula Sa’adah kinji,

Allah yadawo Dake lafiya duk da nasan Zaki kwana biyu sosai acan kafin kidawo.

Rumgume Annen tayi jikinta na sanyi tace”

Zanyi kewarki Anne,

Kuma Inshallah bazan Dade sosaiba Zan dawo.

Murmushi Anne tayi tana cewa”

Ba komai ki zauna da momynki tayi kewan zama Dake idan tagama ganinki da kyau Kya dawo,

Allah ya tsare.

Amin” tace tareda juyawa ta wuce halima na bayanta.

Harta Kai kofa tadawo ahankali ta tsaya gaban Annen cikin sanyi da nutsuwa tace”

Anne,

Anne Laylah ce take daukeda cikin,

Yanzu wata cikin na biyar……

Da wani irin mamaki Annen take kallon Sa’adah,

Wani murmushin manyanci ne ya subuce Mata sai kawai tace”

Ita Laylan?

Har wata biyar Kuma shine take zaune gida daya da Na’ima?

Shiru Sa’adah tayi tana Rasa abin cewa sbd yanzu Kam kowa yasan idan Na’ima Takoma yanzu ba shakka zataga ciki jikin Laylah, saidai rashin sanin mahaifin ciki shine saukin masifar.

Wuce driver na jira karkiyi latti.

Wucewa Sa’adah tayi tabar Anne zaune tareda Shiga mamakin duniya dama jinjina zurfin ciki irin na Laylah,

Tabbas tasan Na’ima zata buga rikici na gaske idan tasamu maganar cikin mijinsu a jikin ‘yar datakewa kallon Yar riqonta…

Tuno lokutan datake waya da Turaki tanajin mace tayi kusan lokuta da dama,

Kenan Laylah ce….

Kasa tunanin komai tayi kawai sbd daga Turakin har Laylan sun tsundumata mamaki harma batasan Mai zatace ba,

Me zata fadawa mutanen data gama tanadin gyaran Amarya agurinsu da sauran shaaninsu…

Abu daya ta yanke a ranta shine dauko Laylah kafin Na’ima Takoma.

*****Zaune suke a lafiyayyan palon Turaki Dake cikin gidan

Yana zaune 2seater sanyeda skyblue yadi Mai tsananin taushi daya sake bayyanarda kwarjininsa

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button