Yanzu dai tagama wannan shashancin mutafi ai muma lokacinmu yazo Dan idan muka tafi zamu bude namu asusun lissafin agurinsa tunda ga ciki
Kafin ki dawo saikin haihu tunda ba qasar yake zamaba Kuma kingama karatun ai dama Dan Haka muma Bismillahi.
Daga Sa’adahn har momy Babu Wanda yasake cewa komai,
Suna sauraron su umma Jamila nata musu fada kokuma fade da gorin dawainiyarsu dasuke Dan taimakawa tun lokacinda Sa’adahn na qarama da Abban baya wani zama har lokacinda yake jinyarsa sune suke Dan taimaka musu.
Har dare daga ita har momyn Basu huta da fadan umma Jamila ba Saida Haj Karima ta tsayar da zancen da cewan ai yanzu tunda Sa’adahn na hannunsu zasu qaru da Turakin.
Da wannan umma Jamila ta sarara musu har drivern Anne yazo ya dauki Sa’adah a gidan Suka tafi gida.
Tana Isa gida komai na dakinta halima ta gyara ko’ina sai qamshi da sanyin AC ke tashi Bata wani zauna ba ta shige ta kwanta sbd kunyar Anne takeji batasan Mai zatace Mata gameda cikin Nan da Allah yayi bayyanarsa gaban kowaba,
Takardar acikin hanbag dinta dasukaje asibitin tun wancan lokacin take Kuma tunda tadawo take boye hanbag dinma gabaki daya sai ranarda zata fita ta janyota ta fita da ita Kuma ranar ne tsautsayi yahau kanta har tayi murnar Babu Wanda yagani a jakar shiyasa takuma boye jakar sai yanzu Allah yanufa zancen zai fita,
Kunyar Anne datake ji shine na boye Mata itama Basu fada Mata ba bayan ta cancanta tasani sbd yanda ta daukesu tamkar jininta
Kuma tasan idan Annen tasani Babu yanda zatai tabari a cutatar da Laylan gashi rashin wayonsu yasa tasamu zancen daga sama gashi taqi cemata komai akan zancen
tamaqi tayarda zancen tayi kaman ba’ayiba.
Kwantawa tayi tareda neman numbern Laylah wadda yanzu laulayinta yafara yawa ba komai take iya ciba sai fruits datake Sha kaman me,
Ringing wayar taitayi baa dagaba Dole ta hakura ta qyaleta.
Washe gari jirgin safe zasubi Dan Haka tunda safe ta tashi ta shirya Kaya cikin qaramar suitcases guda biyu ta shirya tafito sbd driver na jiranta zai kaita gidansu Haj Karima dagacan zasu dauka su umma Jamila su wuce airport Abba daban zaiyi tafiyarsa ba taredasuba saiya gana sosai da Amininsa duk da kusan kullum tunda suka zo Abujan suna tare.
Anne cikin kulawa Tace Mata ki kula Sa’adah kinji,
Allah yadawo Dake lafiya duk da nasan Zaki kwana biyu sosai acan kafin kidawo.
Rumgume Annen tayi jikinta na sanyi tace”
Zanyi kewarki Anne,
Kuma Inshallah bazan Dade sosaiba Zan dawo.
Murmushi Anne tayi tana cewa”
Ba komai ki zauna da momynki tayi kewan zama Dake idan tagama ganinki da kyau Kya dawo,
Allah ya tsare.
Amin” tace tareda juyawa ta wuce halima na bayanta.
Harta Kai kofa tadawo ahankali ta tsaya gaban Annen cikin sanyi da nutsuwa tace”
Anne,
Anne Laylah ce take daukeda cikin,
Yanzu wata cikin na biyar……
Da wani irin mamaki Annen take kallon Sa’adah,
Wani murmushin manyanci ne ya subuce Mata sai kawai tace”
Ita Laylan?
Har wata biyar Kuma shine take zaune gida daya da Na’ima?
Shiru Sa’adah tayi tana Rasa abin cewa sbd yanzu Kam kowa yasan idan Na’ima Takoma yanzu ba shakka zataga ciki jikin Laylah, saidai rashin sanin mahaifin ciki shine saukin masifar.
Wuce driver na jira karkiyi latti.
Wucewa Sa’adah tayi tabar Anne zaune tareda Shiga mamakin duniya dama jinjina zurfin ciki irin na Laylah,
Tabbas tasan Na’ima zata buga rikici na gaske idan tasamu maganar cikin mijinsu a jikin ‘yar datakewa kallon Yar riqonta…
Tuno lokutan datake waya da Turaki tanajin mace tayi kusan lokuta da dama,
Kenan Laylah ce….
Kasa tunanin komai tayi kawai sbd daga Turakin har Laylan sun tsundumata mamaki harma batasan Mai zatace ba,
Me zata fadawa mutanen data gama tanadin gyaran Amarya agurinsu da sauran shaaninsu…
Abu daya ta yanke a ranta shine dauko Laylah kafin Na’ima Takoma.
*Zaune suke a lafiyayyan palon Turaki Dake cikin gidan
Yana zaune 2seater sanyeda skyblue yadi Mai tsananin taushi daya sake bayyanarda kwarjininsa
Gabaki daya turaren Bois elite ne ke sanyaya palon da qamshin ga sanyin AC daya Gama Kama koina hankalinsu akwance,
hankalinsa na Kan wayarsa yana kallon sakon LAYLAH yashigo na wasu kisses data turo Masa.
Ya Dan dauke Kai Yana Kama kansa cikin basarwa sbd Abban Laylan dasuke tare Yana zaune shima suna magana.
Dan gyara murya kadan yayi sbd neman sarkewar Dake da emojis din datake sake turowa
Yadauki wayar ya kashe gabaki daya sbd zata iya rikitasa ya Rasa meyake fada gaban Mahmoud dayake basarwa sbd karya gano waye.
Cikin nutsuwa Abba ya kalli Turakin bayan yagama kashe wayarsa ya aje gefe da sautin bayyanarda zallar gadiyarsa a natse yace”
Turaki Babu abinda Zan saka maka dashi sai godiya kawai,
Kayiwa Allah,
Kayiwa abota,
Kayiwa zumuncinka da Zainab,
Kakuma yiwa marayin Allah Dan Haka Banda bakin godiya daga Kai har Anne Ina muku fatar samun sakamakon gidan Aljanna.
Cikin basar da zancen ya Dan kalli Abban yana cewa”
Inaga ai mun rufe wannan maganar right¿
Numfashi Abban ya sauke ahankali da Jin nauyin abinda zai fada
Yadai Daure tunda ba boyo tsakaninsu da Aminin nasa ya dago ya kallesa yace”
Sai maganar Laylah…..
Sai alokacin Turakin ya dago a hankali ya kalli Abban Jin sunanta.
Gyara zama Abban yayi Yana cigaba da cewa”
Nasan Bai kamata ba nashiga zancen tunda ikonta a hannunka yake yanzu Amma tunda kamar alfarmace tun farko kayimin ka amince da Aurenta
Yanzuma Ina riqon Alfarmar karka duba tarayyata dakai idan har bakada raayin auren zaka iya sawwake Mata tadawo gida ko ahakan kayi matuqar kokari da taimakawa sosai wlh……..
Tunda yafara hada shimfida da LAYLAH Bai sake kallon cikin idon Mahmoud ba sai yanzu daya dago ya zuba Masa manyan fararen idanuwansa akansa batareda ya bude Baki yace Masa kala ba,
Abban yasan Turaki farin sani,
Babu halinsa da Bai saniba sai Wanda yaqara daga bayan Nan saidai duk da hakan idon da Turakin ya zuba Masa bazai iya cewa na menene ba
Dan Haka ya Dan muskuta Yana gyara zama jiran mgna ta fito daga bakin Turakin Dan Yama kasa qarasa sauran zancensa…
Ahankali Turakin ya dauke ido daga kan Abban Yana saukewa Kan Tv Dake aiki batareda ya iya cewa komaiba,.
Shi kansa Abban shiru yayi sbd yasan maganar na buqatan nazari Dan Haka ya kalli Turakin murya a mace yace”
Inaga gobe Zan wuce Nima A Abdoul yagama min booking ticket da komai…
Tafiyar safe zanyi saidai idan naji daga gareka.
Har lokacin Turaki Bai iya cewa komaiba sai gyada Kai da yayi Ahankali cikin nutsuwa.
A Abdoul ne yatafi maida Abbansu Laylan daga can ya wuce gida shima sbd dare yayi Daman.
Tunda Mahmoud yatafi Yana zaune inda ya barsa qafarsa daya Kan daya idanuwansa sun sauya sosai ya rufesu ahankali ya bude saiga Ms Na’ima tashigo sanyeda doguwar Riga idonta a hargitse sbd kwanakin gabaki daya Bata cikin nutsuwar zuciya.
Zama tayi gefensa cikin kokarin danne baqin cikin dake cin ranta tace”
Turaki gobe Zan wuce Lagos acan jirgin da zanbi zai tashi komawa zanyi,
Ga Laylah anbarota ba kowa nasan tana cikin kadaici….
Batareda ya waiwayo ya kalletaba Kai tsaye a karon farko tsawon shekarun aurensu dazai fara hanata tafita yace”
Ba yanzu Zaki komaba ki zauna anan tukuna.
Da mamaki ta kallesa tana juyowa gabaki daya suka fuskanci juna
Tace”
Nariga nayi komai na tafiya zakace bazanjeba?
Babu ruwanka da dukkanin tafiye tafiyena sai yanzu Kuma,
Kayi hkr sbd nariga na shirya tafiyata Banga zamanda nakeyiba anan nabaro yarinya ita kadai acan Dan Haka Ni tafiya zanyi….