Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 45

Tana Shiga bangarenta tun a Palo siddika dake Mata sannu da zuwa tana karban handbag dinta ta fahimci maganintane ke aikinsa Dan Haka wani dadi ya mamayeta tana Jin kwanakin duka na Sa’artane Dan kuwa yanzu rayuwar Jin Dadi da kwanciyar hankali takeyi a gidan tunda masifar gaban Ms Na’iman ta isheta da Bata lokacinta
Dan Haka daki takaita ta kwanta ta fito tareda janyo Mata dakin ta wuce kitchen tana cewa”

Faduwar wani tashin wani.

Kwananta biyu Bata tako ko kofar fita Dana bangarentaba tana fama da kanta sai data cika kwanan biyu cif tadawo daidai ta nufa Sashen Anne ta gaidata Kamar Dole ta fito Takoma bangarenta tana wayoyinta da Zinat data dagawa hankali akan ita ta tafi Ta binciko musu sbd zaman Nan a baibai bazai kaisu koinaba sai gurin baqin ciki da bacin Rai sbd suna Bata lokaci cikin Yana da uwar cikin suna sake samun qarfi tunda ciki zaina cigaba da girma.


Qarfe 5 na asuba jirginsu ya sauka a Murtala Muhammed International airport dake Lagos,

Sanye take da Moja majka Abaya maroon Mai shaking material
Kanta nade cikin Marron veil qarami na Abayar sai black Gucci suede loafers a qafarta da qaramar Bottega veneta small shoulder bag Dake rataye a kafadarta,fuskarta tayi haske sosai ta yanda ko kafin idonka ya sauka a cikinta zakasan tana daukeda juna biyu dayayi Mata kyau matuqa,

Bata qara wata qiba ba hakama Bata rameba shiyasa cikin ya fito sosai iya watanninsa…

Wani numfashi ta sauke lokacinda ta shaqi iskar Nigeria ta lumshe ido cikin gajiya da Yar yunwar Dake damunta ta fito Ana biyeda ita da luggages dinta.

Tana fitowa Wanda idonta yafara sauka akansa ne tsaye Yana waya cikin black Rugby’s Riga da wando da jacket Mai girma datakai Masa har gwiwa…

Duk da Yana sanyeda face mask black da hular sanyi,
kallo daya tayi Masa tagane shine duk koina nasa kusan a rufe yake Kuma Bata taba tunanin zai iya zuwa airport da kansa tarbonta ba
Da haka wani sanyi ne ya mamaye zuciyarta har batasan idonta Yana cikowa da hawayen kewarsa dataiba da farin cikin ganinsa…

Ahankali take takowa idonta cikin nasa daya zuba matasu cikin kallo Mai wuyar fassarawa,

Akan cikinta daya turo Ana ganinsa da kyau ya sauke idanuwansa kafin ya ware Mata hannuwansa ahankali Yana cewa”

Finally.

Ahankali tashige jikinsa tareda rungunmesa da sauri hawayenta suka sauko tana cewa”

Abbahhhh.

Hannunta ya Kama A Abdoul ya wuce gaba tareda kayanta aka shigar mota kafin ya bude motar Turakin da kansa ya bude Mata motar yana riqeda hannunta ta shiga kafin shima ya Shiga A Abdoul yaja motar suka bar airport din.

Hannunta na cikin nasa a sarke yake kallon cikinta Yana kallon fuskarta Dake glowing tana daukan idonsa da hankalinsa..

Wani malalacin murmushi ya saki Mara sauti ko kadan alokacinda idonsa yagama shawagi Kan cikinta Kuma maganar Abbanta ya fada Masa alokaci daya.

Dagowa tayi ta kallesa ganin murmushin daya sake,
a hankali ta bude Baki zatai magana ya Dan rufe Ido Yana girgiza Mata Kai alamar Bata buqatan magana.

Lumshe fararen idanuwanta tayi tareda Dora hannunta daya Kan hannuwansu dake sarqe cikin kulawa da son abun Dake ranta ta bude Baki ba sauti tace”

I love you Abbahh.

Wannan karon murmushinsa sai daya bada sauti kadan sbd shigarsa da kalmar Tayi da dagashi sai itane bazata hadiye yawun datake bakinta lokacinda tafada Masa wannan kalmar saiya shanyesu tas Dan kuwa sauran zaqin kalmar na cikinsu…Dan Haka sai kawai ya sake damqe hannunta cikin nasa cikin kulawa Yana Dan dauke Kai daga kallonta ya maida Kan wayarsa da aka sake Kira.

Lafiyayyan gidansa Dake Lagos din suka Isa Madam sarat Dake gidan tareda sabuwar Mai aiki daya da aka kawo Ruky sungama gyare koina a gidan sai qamshi da Sanyi ke tashi koina
Ga aikin breakfast dasuke Yi cikin qwarewa da mutsuwa…

Hannunta cikin nasa Suka shigo palon bayan A Abdoul ya miqawa Madam sarat akwatinan Lv0 na Laylan ya juya ya nufi sashensa dake gidan dan komawa baccin Dake cinsa.

Madam sarat kallo daya tayiwa hannuwansu dake sarqe ta dauke Kai tana neman Yar rudewa dai kafin ta Kama nutsuwarta sukai ciki da kayan itada ruky tana kyafta idonta Dan tabbatarda cikin Dake gaban Laylan da alama da Turakin ne tunda ga hannuwansu a sarqe…

To kodai Ms Na’ima ta rasu ne?

Da wannan rudadden tunanin Suka kai kayanta duka makeken bedroom dinsa daya Dake palonsa na sama Suka sauko.

MAMUH

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button