NOOR ALHAYAT 11

11…….
Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba yana sauraren fadan Kanwar Dad din tasa, A fusace tace “Wai ba da kai nake ba ka min shiru Aliyu” ya dago ya kalleta da kyar don har wani ciwon kai fadan ke sa masa, ya marairaice fuska yace “Wllh ina ji Anty, ina jin ki” tace “Nace ka gaya min me yasa ka bar min breakfast kayi
ficewar ka daxu?” yace “kiyi hakuri mum, ban san xan jima haka bane” Tace “To xaka ga uwar da xata baka dinner yau a gidan nan kuwa” murmushin karfin hali yyi ta juya tayi ficewarta, komawa yyi ya kwanta kansa na ci gaba da sara masa, tun safe har xuwa lkcn bbu abinda ya ci ban da ruwa da yake sha, bbu inda bai shiga ba a wasu daga streets din UK ko xai ga Iman amma sam bbu alamarta, shi ya ma rasa gane ko ita ce ya gani ko ba ita ba, ya mike xaune da damuwa yace “Ya Allah…” Har agogo yyi stucking karfe shidda na yamma yana xaune dakin, aka bude kofa tare da sallama, Maryam ce ta shigo dakin tace “Yaya Aliyu are you sick?” Ya kalleta yace “No I am not Maryam” ta xauna gefen gadon tace “Toh naga tun jiya duk ka xama wani iri, gashi daxu ko breakfast baka yi ba ka fita, nasan baka yi lunch ba ma” yace “Kirana aka yi na fita” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Ya school ko baki je ba yau?” Tace “Naje daxu na dawo” yace “Ohk, ina su Baby da Fadil” tace “Suna assignment a daki” yace “Idan Anty ta gama lunch ki dibar min kadan ki kawo min” tace “Toh” sannan ta mike ta fita, ba a dau lkci ba kuma ta kawo masa abincin da ruwa ta ajiye masa.
Kulawa sosai Khaleel ke bata a kwanaki ukun da tayi a gida bata je makaranta ba duk da shi ya hanata xuwa makarantar sae taji sauki sosai, kuma cikin ikon Allah ta warware bata jin ko wani ciwo sae dai Kawai ta kasa mance incident din ne, ba a minti goma Aliyu bai fado mata ba, ko kadan Khaleel bai son ganinta cikin damuwa, he’s as kind as she never expected, duk da wani lkcn he is pretending not to be, kamar dai yasan tana da damuwa, bata kuma yi mamakin ya gano haka ba tunda likita ne shi din, duk Safiya kafin ya fita sae ya tabbatar ta karya ta sha magungunan ta, da yamma kuma idan xae dawo it’s either ya taho mata da fruits ko abinci, har books masu dadi na turanci ya kawo mata ta dinga karantawa, ae kuwa books din also contributed don nishadi suke sa ta idan tana karantawa, idan kuma ta gaji da karatun ta dauko hotunan su Sudais da Shuraim tun daga lkcn da suke jarirai har xuwa girmansu, yawanci kuma hotunan duk tare da Sudais ne wannan dalilin yasa bata gajiya da hotunan, ko gida bata fadi ma su Umma bata da lafiya ba. Yau kamar ko da yaushe tana kwance parlor bayan ta raka su Vanessa da suka xo gaishe ta tun da rana, bell aka danna, ta mike don tasan shi ne, ta isa gun kofar ta bude, gaishesa tayi tana kallon sa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, lkci daya kuma yana tambayarta ya jiki, ta karba tace “Da sauki” yace “Maa sha Allah” xae juya tayi saurin cewa “Are you sick?” Juyowa yyi yana kallonta yace “Just Stomachache, but na sha drugs da sauki sosai” da damuwa tace “Allah ya sauwake” yace “Ameen” daga haka ya rufe mata kofa ya shiga apartment dinsa. Ajiye ledan tay kan table ganin fruits ne, tana ta xaune parlor har kusan Magrib kafin ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, nan parlorn tayi sllh, ta gama addu’o’inta sannan ta mike ta shiga kitchen, tunanin me xata dafa ta shiga yi don yunwa take ji, garnished cous cous tayi da yaji kayan hadi, duk da bashi da yawa kawai tayi deciding ta debar masa, ta zuba a karamar warmer snn ta sa hijab ta fita kai masa, a hankali ta kai hannu ta danna bell, sai da ta sake dannawa ya bude kofar, singlet ne jikinsa da dogon wando, kallon sa ta tsaya yi ya juya ya koma kan kujera ta bi sa da ido, can ta bi bayansa ta rufe kofar, ajiye abincin hannunta tayi ta durkusa gefensa tana kallonsa da damuwa tace “Cikin ne har ynxu?” Gyada mata kai yyi a hnkli yace “But… Sure I will be okay” cike da karfin hali yyi maganan, shiru tayi tana kallonsa taji tausayinsa sosai, a hnkli ya sauko kan kujeran ya duka kan gwiwowinsa, kamar xata yi kuka tace “Ko xaka je asibiti” girgixa mata kai kawai yyi, sai kuma ya kwanta nan gun, kana ganinsa kasan namijin kokari kawae yake, hawaye ya cika idonta, tashi xaune ya kara yi yana runtse ido a hankali yace “Get me water pls” tashi tayi da sauri ta nufi fridge ta bude taga duk masu sanyi ne, ta shiga kitchen ta dau glass cup ta dibo masa na tap, tana dawowa ta duka gun sa ta mika masa ya karba ya fara sha, sae kallon sa take sai ka rantse tare cikin ke masu ciwo ynda tayi da fuska, lkci daya ya ajiye glass din ya mike ya nufi bathroom dake parlorn, ita ma ta mike tsaye, amai sosai yake yi a bathroom din, ta kasa motsawa daga inda take, can ta durkusa ta fashe da kuka, yana fitowa parlorn ya hade kansa da kujera, tashi tayi ta isa kusa da shi cikin rawar murya tace “Don Allah mu tafi asibiti plss” ya dago idanuwan sa da suka sauya xuwa ja, komawa baya tayi da sauri don idanuwan suna kalau ma tsoronsu take barin kuma yanxu da suka kara wani kala kan na da, da alama ya kasa mata magana don girgixa mata kai kawai yayi, xai komar da kansa kan kujerar tayi karfin halin rikosa da sauri tace “Doctor plss let me drive us to the hospital, ina makullin motar yake” murya can kasa yace “I will be alright Khadija, go to my room xa ki ga 1st aid box…” Bata jira ya gama ba ta mike da sauri ta shiga dakin, da box din ta dawo, ta ajiye kusa da shi, ya xamo kasa idonsa lumshe ya bude box din, bayan yan sakwanni ya bude idon ya dau wani allura da syringe ya mika mata, ta bude ido da mamaki ta dai karba ya mayar da kansa kasa, rasa abin cewa tayi, can dai ta balle bakin alluran ta xuke a syringe tayi karfin halin cewa “Ga shi nan” ja baya tayi tana xare ido ganin ita yake nufin xata masa alluran, duk da ta iya kawai niyyar nuna masa bata iya ba ta yi, amma tausayinsa da yanda shi ma ya nuna damuwarsa lkcn da bata da lafiya yasa ta kasa, hannunta na rawa tayi masa alluran, kin bude ido yyi ta koma baya tana kallonsa, bayan wasu mintuna ya mike da kyar ya kwanta kan kujera, ko minti goma bai kara ba bacci ya dauke sa, dawowa tayi kusa da shi tana kallon sa da tausayi ganin alluran bacci yasa tayi masa, mikewa tayi ta dauke glass cup din da abincin da ta kawo ta kai kitchen, ta mayar da box din 1st aid din daki, tayi disposing alluran da tayi masa sannan ta xauna kusa da shi tana kallon sa, giransa kadai ma abun kallo ne a fuskarsa kafin a xo ga long lashes din idonsa, a hankali ta sauke idanuwanta kan dogon hancinsa da ko Kadan bai da miskila xuwa bakinsa, kai kana ganinsa kasan duk yanda aka yi yana da alaka da larabawa, dauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, da sauri ta tashi tunawa da tayi bata yi isha ba, alwala ta sake yi ta gabatar da sllhn nan parlor, tana xaune tana azkar wayarsa ya fara ring, har ya katse bata mike ba shi ma kuma bai ko yi motsi ba, ganin an sake kira ta tashi a hankali ta nufi kusa da shi ta durkusa tana laluban aljihunsa ta fiddo wayar tana kallon screen din, Jawahir ta gani jikin screen din wayar, har ya katse tana kallon wayar, can ta ajiye a hankali ta daura chin dinta bisa gwiwowinta tana kallonsa, bacci yake sosai, ta so tashi ta wuce apartment dinta amma ta samu kanta da kasa yin hakan, bayan minti kusan ashirin ta dago kanta ta jinginar kusa da shi, daga haka bacci yyi gaba da ita a yanda take, A hankali ya bude idanuwansa yana bin parlorn da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kanta, ya mike xaune da sauri yana kallonta, kallon agogo yayi yaga biyu har yyi, fuskarsa ya kai dai dai nata, cikin bacci taji hannu a forehead dinta, ta bude ido da sauri, a hankali ya manna mata lips dinsa a kumatunta, a tsorace ta ja baya xata mike yyi saurin riketa, 6ata fuska tayi hade da buge hannunsa tace “Meye haka” sakkowa kasa yyi yace “Me kike yi a nan?” Sakin baki tayi tana kallonsa, can ta turasa xata mike ya ki saketa, hawaye ya cika idonta tayi da ta sanin kulasa ma da tayi, ya jawota jikinsa yana murmushi a hankali yace “Thanks for ur care Khadija, Neva knew you where this sweet….” Ta kara hade rai tace “Sake ni malam” ba musu ya saketa, ta mike ta nufi kofa, yace “Uhn.. it’s pass 2 now fah” da sauri ta kalli agogo, dawowa tayi kamar ya fada mata mugun abu ta marairaice tace “Lahh ban sani ba… I don’t know it’s late….” yace “Wait… But… But it seems u came with food daxu, ina abincin” da kamar baxata ce masa komai ba sai kuma tace “yana Kitchen” yace “I am just hungry” kitchen ta wuce ta kawo masa abincin sai a sannan ta tuna ita ma bata ci abincin ba ai, tashi yyi ya shiga toilet din dakinsa sai da ya wanke bakinsa yyi wanka snn ya fito sanye da jallabiya yana goge gashin kansa da karamin towel, duk ta gaji da jiransa ya fito ya rakata, ya xauna ya bude abincin ya dau cokali ya fara ci, kallonsa take ta yi kafin ta mike ta tafi ta bude fridge ta dauko masa ruwa, sai da ya kusa cinye abincin ya sha ruwa sannan ya kalleta da sauri yace “But daxu kamar ruwan tap kika bani koh” tace “Uhn” xaro ido yyi yace “Subhanallah, but I don’t take….” sai kuma yyi shiru, ita dai bata ce komai ba banda hararansa da take, jinginar da kai yyi da kujera ya lumshe ido, mikewa yayi ya shiga bathroom din parlor ya fito da alwala, a hankali tace “Ka raka ni pls dare yyi sosai” kallonta yyi kafin yace “Ohk as you wish tunda cinye ki xan yi a nan” daga haka ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofa ta matsa kusa da shi da sauri, ya fita tana biye da shi a baya suka shiga apartment dinta ya rufe kofar, ta sauke ajiyar xuciya tana bin parlon da kallo yace “Toh tafi ki kwanta” daki ta nufa yyi saurin cewa “Waittt… Xo ki kulle kofar tukun” dawowa tayi tana kallonsa ya buda ido yace “Sai da safe, I appreciate ur care” bata ce komai ba xai fita tace “You have…. A call” ya juya ya kalle ta, duk sai taji she sounds stupid, yace “Did you pick?” Tayi saurin cewa “Nooo, I just remembered now, I didn’t even check, just heard the phone ringing” ita kanta tasan kame kame kawai take, yayi murmushi yana shafa lallausan gashin kansa.
12…
Da asuba tana kitchen ta gama goge goge xata hada breakfast taji muryarsa ta waje yace “Morning” da sauri ta kalli direction din window taga bata hangosa ba, ta leka a hankali taga gym yake, ta bar gun da sauri ta ci gaba da hada ingredients din da xata soya eggs din da xata yi toasting da bread kasancewar bata yi da raw eggs, bayan wasu mintuna tace “How you feeling now?” bai amsa ba shi ma, hakan yasa ta juya ta kalli window direction, dai dai lkcn da ya iso kusa da window din kenan suka hada ido ya karyar da kai yana kallonta daga sama har kasa, juya baya tayi da sauri don rigar bacci ne jikinta, yace “Uhn… You look cute in that…” mamaki ne ya cikata ta kasa juyowa, ya ce “Ki shirya xaman gidan ya isa haka ki tafi makaranta yau koh” daga haka ya bar wajen, ko bai fada mata ba dama tayi niyyar tafiya makarantar yau. Karfe tara ta fito cikin shirin tafiya makaranta, fitowa yyi ya tsaya bakin door dinsa yana kallonta yace “Makarantar xa ki tafi yanxu?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Yeah” yace “Alright you wait for me” daga haka ya koma ciki, k’asa wucewa tayi tana ta tsaye wajen har ya fito rike da makullin motarsa, as usual kananun kaya ne jikinsa, kallo daya tayi ma wandonsa ta dauke kai a ranta tace aiki, yace “to mu tafi” parking space ya nufa ta bi bayansa, sai da ta jira yyi warming motar sannan ta bude ta shiga. Haka kawai gabanta ke faduwa ta rasa dalili, idonsa na kan titi yana driving yace “Do you have problem with anybody here?” Ta kallesa da sauri, shi ma ya kalleta, mayar da dubansa yyi kan titi, tana girgixa kai tace “I don’t think it’s any of ur concern” shiru ya d’an yi kafin yace “Ohk then” bai sake ce mata komai ba har ya isa makaranta, bata yarda sun hada ido ba ta bude motar ta fita tace “Thanks” daga haka tayi wucewarta. Tafe suke da course mates dinta bayan sun fito lectures din karfe goma da suka shiga, cafeteria suka nufa ita kuma tace masu xata je library karatu, bayan sun rabu bata je library din ba, kawai she want to be alone ne dama, guri me shiru ta samu ta xauna ta tsura flower dake wajen ido, ta kusa minti talatin a wajen kamar ance ta dago suka yi ido hudu da khaleel dake xaune d’an nesa da ita da wata baturiya dake karatu ita ma, mikewa yyi bayan sun hada ido yana kallon baturiyar yace “Stephanie c yah later” mikewa khadijah tayi ta riga sa barin wajen. Da safe misalin karfe takwas ta fito apartment dinta, yau dai kam ta makara sosai, tsaye ta gansa parking space waya kare kunnensa, suna hada ido ya dauke kai, ita ma bata sake kallonsa ba har ta fita daga gidan a xuciyarta tace “Can ta matse maka” Ita kadai ce xaune Cafeteria bayan sun gama lectures din ranan, Vanessa tuni ta bi saurayinta suka tafi tun bayan da suka gama cin abinci, ita kanta ta rasa me yasa ta ki barin gun har lkcn gashi tana son wucewa, chatting take da kawarta Salima dake Nigeria a WhatsApp kanta a duke, kamar ance ta daga kai tayi still ganin wa enda suka shigo Cafeteria din, a hankali ta saki wayar hannunta ya xame ya fada kan cinyarta, da sauri ta kauda kai xuciyarta na mugun bugawa, table dake gefen nata ya xauna kan kujerar shi da Baturen da suka shigo wajen tare, cikin sanyin muryarsa yake cewa “I don’t have intentions of coming here frank, let be fast” baturen yace “Yeah, they will be here soon…” baturiyar dake tsaye kansu ta mika masu takardar list din abinci dake hannunta, muryarsa ya kuma dakan codon kunnenta da accent din turawa yace “Number 6 content for my frnd, just table water for me…..” Kamar ana tilasta sa yyi maganan, a hankali khadijah ta mike kamar an xare mata abu a ciki, tana boye gefen fuskarta da mayafin kanta ta nufi kofar fita sum sum tana hade hanya, satan kallonsa tayi suka yi ido hudu don bin ta da kallo yyi, lkci daya ya mike ya xaro ido yana kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje, bin ta yyi da sauri yana cewa “Imannn….. Imannn plss wait, Iman…..” hankalinta bai gama tashi ba sai da taga bin ta yake tsakaninsa da Allah gashi ya kusa kamo ta, ta jefar da takalman kafarta da jaka ta fashe da kuka sosai, gudu take kamar her life depends on it, tana yi tana waiwayowa a tsorace, Gani tayi wasu wanda da alaman Africans ne sun rikesa suna tuhumarsa me yasa yake bin ta, hakan ya kara mata kwarin gwiwan gudun, taxi ta samu ta shiga tana waige waige muryarta na rawa tace “Bridge street” tuni mai cab din ya ja suka dau hanya, lumshe ido tayi hawaye masu xafi na sakko mata, tana son fashewa da kuka ko xata ji dadi amma tayi controlling kanta ganin inda take, number gidan ta gaya masa bayan sun kai yyi parking ta bude motar ta fita, tunawa tayi bbu kudin da xata basa, tana kallonsa a sanyaye tace bari ta shiga ta dauko masa kudi, a hankali take tafiya compound din tana goge hawayen dake sauko mata, dai dai fitowar Khaleel part dinsa rike da makullin mota da wasu takardu, tsayawa yyi yana kallonta daga sama har kasa mamaki dauke fuskarsa, hade rai tayi sosai ta turo baki ta dauke kai ta kuma ki motsi daga inda take, taku daya biyu ya iso gabanta tayi saurin barin gun, fixgota yyi ta fashe da matsanancin kukan dake cin ta tun daxu, da mamaki yace “What’s wrong with you, me ya faru? where are you coming from?” Kin cewa komai tayi sai kukan da take yi sosai, damuwa ne sosai fuskarsa yace “Talk to me plss, me ya same ki?” Ta hadiye kukan da kyar tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace “Ban ba mai Cab kudi ba….” Kallon gate yyi, can ya sake ta ya fita, Durkushewa gun tayi ta dinga rera kuka xuciyarta na mata xafi, a haka Khaleel ya dawo ya sameta, ya hade rai yace “malama tambayar ki nake where r u coming from” mikewa tayi tana share hawayen idonta har lkcn bata daina kukan da take ba xata bar wajen ya rikota yana mata wani kallo a d’an tsawace yace “Me aka maki nace, where r u coming from?” Ganin ba magana xata yi ba yana rike da hannunta ya wuce part dinsa da ita, xaunar da ita yyi kan kujera a parlor ya duka gabanta yana kallonta cikin sanyin murya yace “Now tell me what happen” cike da karfin hali tace “Nothing” ido ya xuba mata bai sake cewa komai ba, can ya mike ya koma bayan kujera ya rungume hannu ya tsaya yana kallonta, ta gama cin kukanta ta jinginar da kanta da kujera, tafi minti sha biyar a haka bbu kalan tunanin da bata yi ba har bacci ya dauketa. Shi kam yana tsaye har lkcn bayan kujera yana kallonta yana mamakin irin taurin kanta, sai da ya ga bacci ya dauketa sannan ya xagayo ya iso gabanta ya durkusa kusa da ita, shi dai ya san tausayinta kawai yake ji har ransa, though he don’t know her that much but he knows she’s pained, coz she looks so, lumshe ido yyi ya bude yana kallonta, Khadijah is just the definition of cool Beauty, tall…. fair…. Slim with a perfect shape, Best of all she have got d most sexiest lips and eyes, her nose….. Kauda tunanin yyi, a xuciyar sa yace not as beautiful as Jawahir, a hankali ya mike ya dafata da xumar yace mata ta kwanta, a firgice ta farka tace “Aliyuuu….” Ja baya yyi yana kallonta. Da kyar ta karashe bude idonta da yyi mata nauyi ta daga kai tana kallon sa, xamowa kasa tayi a hankali, ya mike ya rungume hannayensa yana kallonta a ransa yana nanata sunan da ta kira, tashi tayi ta runtse ido ta juya xata fita parlorn, murya can kasa yace “Malama” sake juyowa tayi, yace “Where are u coming from” bata iya ta kallesa ba cikin sanyin murya tace “School” yace “Me ya same ki a can?” Tace “Am not feeling fine” bai sake cewa komai ba ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Magungunan ta ta dauka ta sha lkci daya kuma bacci ya dauketa, bata farka ba sai da asuba shi ma ta dalilin yunwa, ganin lkcn sllh bai karasa ba ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, motsi ta dinga ji a waje ta leka a hankali, gym ta gansa yana yi jikinsa sanye da 3qtr kadai, suka yi ido hudu tayi saurin barin gun, parlor ta koma ta dauko Hijab ta sa sannan ta dawo kitchen din, har ta gama abinda xata yi bata sake leka waje ba, ta koma parlor da Indomien ta, tun da tayi wanka bayan tayi sllh gabanta ke ta faduwan xuwa schl gashi tana da test, hawaye ta dinga yi duk xuciyarta tayi rauni, gaba daya xaman kasar ya isheta taji gida take son komawa, to karatun fa, shekara bai kai biyu ya rage mata ba, danna bell aka yita mike a d’an tsorace, don ynxu kam gaba daya a tsoracen take, hijab ta saka ta fito, a hankali tace “Yes?” Yace “How you” bude kofar tayi ta gaishesa, yace “Baxa ki schl din bane yau?” Kamar xata yi kukatace “Ban sani ba” kallonta kawai yake bai ce komai ba, bayan yan sakwanni yace “Toh ki shirya, I am waiting for you” daga hka ya juya ta rufe kofar.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Har dept ya ajiye ta, kowa ya ganta a lkcn yasan a tsorace take, yace “Yaushe xa ki gama lectures din?” Tace “Quiz ne” yace “Shi kadai?” Kai ta gyada masa, yace “ohk am around I will call ltr in ji ko kun gama” buda masa hannu tayi tace “Jakar ya fadi jiya ai” Kallonta ya tsaya yi, can ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace “I will call” ta karba tana gyada masa kai, daga hakata fita motar, shi ma ya fito yace “I think I will leave the car here” bin satayi da ido har ya wuce kafin ita ma ta bar wajen da sauri