22*NOOR-AL-HAYAT* *CIGABA*
Daukar waya Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma m utan gidan a madadin breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida
, ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace “Gashi ku yi kudin mota, idan kin dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya” Umma ta girgixa kai tace “A’a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin mota” Yace “Shi kenan, Allah ya tsare” mikewa tayi ta fita dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d’an kayan da ta fara siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace “Umma ina xa mu?” Umma ta kasa kallonta tace “Xa mu d’an yi tafiya ne khadijah” daga haka ta kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa “Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita” ita dai bata tanka su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin gwamna… Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle kalle khadijah take tace “Umma where is this?” umma tace “Kaduna” Khadijah tace “Wow I’ve heard of Kaduna in school” Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take “Umma where is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere” Umma tace “look I don’t want to here ur mouth again” shiru khadijah tayi, daga karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace “Kulu mai waina” Matar tace “Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun wuce” Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace “Wancan gidan mai keke a gaban sa” Umma tayi murmushi tace “Kin ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai” daga haka suka juya khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace “Yaya” dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace “Aminatu” karasawa Umma tayi ta rungumeta tace “Rai kan ga rai yaya” cike da farin ciki Yakumbo tace “Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan naki?” Umma tace “Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a gaida ku” Yakumbo tace “Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin bikin, wacece wancan” Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma tace “Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad” Yakumbo ta rike haba tace “Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita kenan?” Umma tace “uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi sallah” Yakumbo tace “Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa” tabarma ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake watse tsakar gidan, Umma tace “yaya ina mutan gidan?” Yakumbo tace “Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin titi” shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa “Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube” Umma ta kalleta da sauri tace “Ina xa ku koma yaya?” Yakumbo tace “Oho dai har yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar mana da kaya waje” Umma tace “Ikon Allah” Yakumbo tace “Ai ke dai kawai sai du’a’i duniyar ta xama abinda ta xama” Yakumbo ta kalli khadijah da ta takure gu daya tace “ke yar nan tashi ki fita waje gun mai kanti ki siyo min farin maggi” Umma tace “Yaya ai bata san ko ina ba” Yakumbo tace “Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti” daga haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana kallon Yakumbo tace “How much own” yakumbo ta d’an bude ido tace “Eh??’ Umma tace ” twenty naira” khadijah ta juya ta fita, yakumbo tace “Sai na ji kamar yare tayi” Umma tayi murmushi tace “Turanci tayi” Yakumbo tace “Au tohhh abun na manya ne Ashe” ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace “Ina magin kuma me ya sa kika dade?” Khadijah tace “Umma I’ve forgotten the one she mentioned” Umma ta hade rai tace “Bani kudin” mika mata khadijah tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo mata da maggi star saba’in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta, la’asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace “Toh Amina xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d’an taimaka ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko yarinyar nan ki sa tayi” Umma tace “Toh yaya, amma fa har yanxu yaran basu dawo ba” Yakumbo tace “Rabu da gantalallu suna makwabta na sani, idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya” daga haka yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace “Umma the food is somehow” Umma ta hade rai tace “Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba” Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d’an karamin dakin yakumbo, har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa, Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace “Kije kantin da kika je daxu ki karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci” Karba khadijah tayi ta fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta, Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan…. sha dayan dare bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace “Ikon Allah, mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa” Umma tayi shiru bata ce komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace “Toh ni wannan ai ba matsala bace, don dai in rike marainiya, bakomai wllh” Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba yakumbo tace “Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye yaya” makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu. Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah, dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta samu ta bar gidan duk jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko muciya tace “Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima” Jikin khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce “Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki” Yakumbo tayi shiru tana kallonsu.
23Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace “Meye wannan din kika dauko?” Da kyar khadijah tace “Firewood, it’s too heavy, and it’s pricking me all over” a fusace Yakumbo tace “Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci” korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace “Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji” a hankali khadijah tace “Toh nagode” A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa “Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki” Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace “Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan” Yakumbo na huci tace “Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni… Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu” Salamatu tace “Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu….” Katse ta yakumbo tayi tace “Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita” Ladi tace “Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d’an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d’an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh” Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace “Kai amma fa kun kawo shawara, amma….” Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce “Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu” juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace “Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba” dariya Ladi tayi tace “Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita” Yakumbo tayi murmushi tace “Dadina da ku akwai shawara mai ma’ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba….” Ladi tace “Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka” yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace “Dari bibbiyu dai” daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace “Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta….” Ladi tace “Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta… Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba” hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa’a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace “Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako” Bibalo tace “Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya” daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace “Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda” tagumi tayi tace “Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa” Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace “Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa’a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A’a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta” Yakumbo tace “A’a mu je kawai mu gwada sa’ar mu” Bibalo tace “Toh ki sallame ni ni xan wuce” Yakumbo ta hade rai tace “In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki” Bibalo ta bude baki tace “Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki” mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa “Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba” dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace “Ya fi babu ai” daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace “Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?” Yakumbo ta hade rai tace “Idan an dauki yarinya ba” Abu tace “Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?” Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace “Warcen da ta fi minti ashirin tana d’an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba” yakumbo ta marairaice tace “Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari” Abu ta tabe baki tace “Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya” Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa “Toh bamu minti biyar kacal” tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace “Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba” tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace “Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?” Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace “Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma” khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace “Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba” yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya” daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa’a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace “Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?” Yakumbo ta tsuke fuska tace “A kan me?” Abu tace “A’a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace “Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?” Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu’ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace “Toh Allah ka bamu sa’a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba… Yakumbo tace “Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru” daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace “Wa ku ke nema?” Yakumbo ta mike tace “Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana” ya girgixa kai yace “Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo” Bakin yakumbo ya fara rawa tace “Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh” Mai gadin yace “Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn” daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa “Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi” Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.