NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Rahima ta rike haba. “Oh ni na shiga uku, Maryam hala kudin kanfen Alh Surajo ya Baki?”..
Umma ta kallesu “Wani ne Kuma haka?”

Maryam ta gyada Kai “Kyaleta Umma da ‘yar halas take magana, amma ba za aji mutuwar uwar sarki a bakina ba, ta fada miki ko waye shi.”

Baki dai shi kan yanka wuya, dole ta yaye Abdul din ranar jumma’a bayan an aikawa kakarsa. .
Kaji, zabbi,madara dasu bornvita da sauran tarkace banda sabbin tufafi aka tarkato, banda buhun shinkafa da jarkar Mai, matan Hayatu suke takewa Hjy Kaltume baya wajen zuwa diba Dan yaye, shima wan baban nasa kudi ya bashi matansa kuma crates din kwai.
Rahima na gida bata futa aiki ba saboda zazzabin da ciwon nono ya sa Mata, ganin bakin yasa ta tashi ta zauna.

Bayan an gaisa Abdul ya dare bisa cinyar kakarsa yana baje sabbin kayansa.
Umma nata zubawa su Hjy Kaltume godiya.
Hajiya tace “Duk aikin iyayensa tawa tukunyar farfesun na gida sai ya taho zai ci.
Umma ta kalli su Hayatu “Madallah Allah ya baku ladan zumunci.”
Yace “Ba komi Umma Abdul danmu ne koda Rabi’u na nan balle yanzun da kasa ta rufe idanunsa.”
Tun dai Rahima na dauriyyar Kar suga kwallan da take kokarin maidawa har ta bara sai nishin kukanta suka, hankalin kowa ya tashi din sun san ba shakka uban Dan ta tuna.

Ana haka Baffa ya shigo cikin sauri ya tsugunna suka gaisa da bakin kana ya fara rarrashun diyarsa cikin kalamai masu taushi har hankalinta ya koma jikinta ya kara yin godiya ya fita..
04/09/2020, 21:15 – Anty saliha: …ˆRAHIMA…doc by jami

12

  Sun dade suna taba hira tun Rahima bata saki jiki ba ta warware a nan ne Jamila ke ce Mata "Kiri-kiri kin guji gidanmu Rahima."

Haulatu ta kalli uwargidanta tace “Ke dai bari Yaya nima abinda ke zuciyata kenan.”
Rahima tayi murmushi tace “Aikine yai min yawa a school amma kuyi hakuri Ina nan zuwa.”

Hayatu ya kalli matansa cike da jin dadin ganin yadda suke tafiyar da al’amurransu yanzun sabanin da, yayi murmushi yace “Idan baki taho don komi ba Kya zo mana murnan tafiya sauke farali ko don Allah yayi bana za muyi arfa Ni da Jamila.”

Tace “Iye! Shine baku Fadi ba tun zuwanku, laifinki nan wannan Aunty amarya.”

Haulatu tace “Yi hakuri wallahi labarin dana kunso in fada miki suna da yawa ganinki haka yasa nayi sanyi, da gaske Ya Haseeb ya biyawa Maigidan da Uwargida kujerar hajj bana.”

Jamila ta amshe “Itama amaryar anyi mata alkawarin badi da ita insha Allahu.”

Umma ta kalli Hjy Kaltume tace “Masha Allah Kai Allah yai wa wannan yaro albarka, shi dai dukiyarsa ta dawainiya da jama’a ce, kunga hidimar da yake yiwa su Abdul kuwa?”
Hjy Kaltume tace “Don Allah ki bar wannan maganar Habiba, kula dasu ya zama dole.”
Rahima ta kalli su Hayatu tace “Naji dadin jin labarin nan, Allah ya nuna mana anje an dawi lafiya, shi Kuma Allah yai masa sakayya yasa muji na Aunty amarya haka badi idan muna raye.”

Daga nan sukayi sallamar tafiya, Rahima ta rakosu kofar gida tayi musu alkawarin ziyartarsu wani satin.

Bata tafin ba sai wajen sati na uku bayan tayi sarai ta koma tamkar bata taba wani shayarwa ba. Tana isa gidansu Hayatu ta kara tabbatar da ba abinda yafi zama lfy da kwanciyar hankali, yanayin gidan ya canza, maigidan ya Kara gyara ko’ina tsaf, mata da yara sunyi shar, shima yayi fes har kiba yayi ya fara teba. Ta kasa boye sha’ awarsu cikin hira tace musu “Nifa kun burgeni, Ina mamakin canzawarku, wani shahararren malami yai muku waazi ya shige ko Yaya?
Suka kalli juna suna murmushin fahimta kafin Jamila ta fara magana “Alamarun Allah ne, kinsan idan yaso mutum da shiriya, ba abinda myuke yanzun sai godiyar Allah da ya ganar damu.”
Haulatu ta karba “Wallahi mun fahimci ba abinda ke jawo tsiya irin tashin hankali da masifa.”
Hayatu yace “Nima kullum cikin godiyar Allah nike, da har fargabar shigowa gidana nike, dana doso kofar gidan sai gabana ya Fadi don ban San bala’in da zan shigo in taras ba, Ina kuwa shigowa abinda nike gudun zan taras, kiji harshensu na tashi kamar zasu dafa naman junansu, inyi -inyi su bari ko kallo ban ishesu ba sabida sun riga sun hau dokin shaidan Yana sukuwa dasu.
“To kuma meye na tashin tashina, kuskure ne munyumi, mun gane mun tuba mun dawi hanya. Jamila ta koro jawabin…
Haulatu tace “Rabu dashi dai Hajiya to waye bai kuskure?.
Rahima tayi dariya “Kwarai dukkan Dan Adam ajizi ne dole a samemu da aikata kura-kurai yau da kullum shiyasa ake son mutum ya rinka rokon Allah ya shiryar damu hanya madaidaiciya ya Kuma ganar damu ya bamu ikon bin tafarkin gaskiya, kana ya yafe Mana zunubanmu na biye da sarari, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.Amma Ina ganin fa tun farko laifinka ne Ya Hayatu.”..
Ya kalleta cikin mamaki “Kamar yaya? Alhalin kullum Ina kokarin yin adalci tsakaninsu, fitina ce kawai amma da suka ga ba riba sun sauke.”.
“Au Kuma haka zaka ce?” Suka tara Fadi
Rahima tace “Ni dai na fahimci bala’in son Yaya kuke shi ya jawo muku bakin kishin Nan.”

Ya sosa keys “Haka ake so? Ina ce in har son ne competition din kyautata min ya dace suyi ba rigima da juna dani kullum kaina dana aje su ba, tsaya kiji wani sirrin kanwata wallahi da sunci gaba da shirmensu ko da yanzun na Kara aure din har na kusa gama shirya komi, Kuma banyi niyyar hadasu gida guda ba, in. Koma can in tare hankalina kwance su kuwa suci tsiyarsu nan inga karyar kishi.”

“Allah ya tona maka asiri, ashe amanar mu kaso ci muna zaune tun baka da komi daka samu shine zaka dauko wata taci arzikin? Da wallahi kun gane kurenku data gwammace bata aureka ba.”
Rahima ta dafe kai tana dariya tace “Wai ni kaina Ya Hayatu ka yarda da batuna, Kuma na baka goyon baya muddin suka ci gaba da halinsu ka aikata abinda kace daga nan a ga wacce tafi sonka.”.

Suka taso kamar zasu cinyeta danya dyk da sun san wasa take, Saida ta basu hakuri tace ai ba sauran batun wata amarya tunda kun hada Kai Kunji ance zama lafiya yafi zama dan sarki, muddin za ayi hakurin zama da juna sai kuga Allah na taimakanku, wadata ya sameku, maigida yaji dadin kyautata muku, yaranku su tashi cikin ingantacciyar tarbiyya da kyakkyawar hadin Kai da zumunci da son junansu ga kwanciyar hankali da samun natsuwa.”..
Suka ce wallahi mun gane kanwarmu Allah ya ganar da sauran mata Ina alfanun mugun zama, mun gode da shawarwarinki, Allah ya kawo mana suruki nagari.”

Nan da nan ta bata fuska “Anya zaku same shi da wuri?”
Hayatu yace “To aure dai sunnar manzo ne nasan kinsan hakan, mu ba zamu so ki zauna ba aure bayan rasuwar Rabiu ba sai a rinka zargin wani abu.”

Ta nisa “Ai ba cewa nayi ba zanyi ba, Kai kasan zaman da mukayi da kaninka, Ina zan samu Mai kwatankwacin halayensa?”

Jamila tace “Su din dangin gujiya ce, sai an fasa ake sanin na kwarai, ki fasa ki gani Mana.”

“Na tabbata zata sami Mai gari kuwa, mu dai mun kosa mu sha buki.”

Tace "Tsokanata ma kuke, bari in shige gidanmu.

Ta koma gida tana tunanin hirarsu dasu Hayatu. Aure? Ita har tsoro kalmar ke bata ba don komi ba sai domin rashin cikakken kwanciyar hankalin zabin wanda zai zama abokin rayuwarta da tunanin yadda zata Kara sake koyo kaunar wani da namiji tunda har lokacin bata sami Wanda ma ya kwanta mata a rai ba ko jininsu ya hadu balle a kai ga batun aure..

Maganar abokin marigayin ma bata taso ba don a ganinta da zata aureshin ma taci amanar marigayin kenan duk da ba addini ne ya hana ba, a daya bangaren surutun jama'a fa kasancewarsa saurayi Wanda bai taba aure ba, ita kuwa harta haihu, shin zata iya daure  gutsuri tsoman daka iya yiwa auren dabaibayi? Ina batun danginsa,  shin zasu  karbeta ba tareda wata tsangwama ba,? Ajiye batunsa a gefe shine alkhairi,to Alh. Suraj fa dake da magoya baya irinsu Maryam harda Umma da ta fara shiga ciki, idan bata yi taka tsantsan ba sarkin yawa yafi sarkin karfi lalle suna iya taruwa sufi karfinta, ta tsaya tayi nazarin Alh Surajo lalle yes mutum kamili sai dai ba nan gizo  ke sakar ba ta kwatanta kaunarsa a zuciyarta abu ya faskara in ba hakuri zata yi ta auresa hakan Nan ba ta koyi so da kaunarsa yadda tayi na Rabiu amma idan tayi hakan shikenan bata da ranar jin dandanon zakin zumar soyayyar da Maryam ta kwadaita mata kenan? Oh oh Allah gani gareka, kayi min zabin abinda yafi zama alkhairi a rayuwata.

Wasa-wasa watanni sun Mika sunyi nisa har ana neman hada shekara da rasuwar mijinta, amma ba amo ba labari ba alamar zata fidda miji cikin masoyanta da suka kasa rabuwa da ita suyi fushi.
. Abdul karami har ya shiga nursery, mamansa kuwa ta Kara sadaukar da kanta ne a aikinta, lokacinta na yaran da take koyarwa ne Wanda Allah ya dorawa lalurori iri daban-daban, kullum tausayinsu karuwa yake, kusancinta dasu ya fiye mata komi don haka ta manta shaf da wani batun aure, tunanin zama da wani ya shafe ya goge a ranta.
04/09/2020, 23:29 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by Jami

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button