JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELSUncategorized

JIDDAHTUL KHAIR 37

Slowly Jiddah ke tafiya kamar bata son yi a compound dinsu Abuturrab, su Maimoon duk sun yi gaba tare da Umma, ita ce karshen shiga parlon, tsaye tayi bayan kujera ganin Abuturrab dake sakkowa cikin parlon waya kare a kunnensa, tayi bakin kokarin ganin bata kallesa ba, bayan ya shigo parlon ta xaga ta bayan kujera tayi wucewarta part din Ummi ya bi ta da kallo,

Bayan Jiddah ta gaisa da Ummi, Ummi tace “Ki tafi dakin Hajja suna can” Mikewa tayi tace “Toh” sannan ta fita xuwa dakin Hajja, Umma na xaune su Maimoon na ta bude akwatunan da aka jera a dakin, Hajja tace “Yanda kika san wata yar gwal xa a auro, haka aka hada lefen har da na Allah ya isa…” Akwatuna biyar ne set biyu each da kit, Umma ta dinga kallon uban kayan da aka hada na lefen bayan su Maimoon na ta budewa, Hajja tace “Aa kar ki ji komai Ramlah ai nace duk xan dibar ma kanninsa abinda ya sauwaka a ciki, mu ba 6arayi bane da xa mu kai masu wannan ubansun kayan, ni kaina xan cire atamfa me tsada daya da jaka, takalmin ma baxai min ba sbda me tsini ne kar in je in karye shi sa baxan dauka ba, amma duk wa ennan yan matan xan cire masu duk abinda Allah yayi wllh” Umma tace “Aa

Hajja ki bar masu kayansu kawai, Allah ya sanya alkhairi, ya bama yan baya haka” Hajja tace “Kaji wata magana irin ta ‘yan kasar nan, wllh wllh babu shegen da xai yi haka a Masar, sannan me yasa baki bari Ahmad ya hada ma Ramlah irin wannan lefen ba? Ba shi ma yana da dukiyar ba na samu labari?? to shine ni xaki ce jikana ya dauka ya kai ma su gaba daya sbda sata yake yi a sararin samaniya? Aa wllh duk xan bi in rage ni ba gantalalla bace” Umma bata kuma ce mata komai ba, ita dai Jiddah na xaune ta rakube jikin kujera tana bin akwatunan da kayan ciki da kallo. Abuturrab ne tsaye parlon step mum dinsa da duk ta firgice masa, yayi

kasa da murya yace “Toh ke ba dai kinsan duk abubuwan da kika xuba a ciki ba Aunty, komai kika ga yayi missing kar ki damu xan bada kudi ki siya wani ki saka” Aunty tace “Ni dai cewa nayi ka tafi ka xauna a dakin, idan aka ganka babu wanda xai ta6a komai cikin kayan, kafi kowa sanin Hajjan nan fa” Abuturrab ya girgixa kai yace “Aunty don girman Allah ki bari su yi ta daukan duk abinda suke so ni xan sake replacing, i just can’t go to that room” Aunty ta wani hade rai tana kallonsa tace “Wato ban isa da kai ba Aliyu, ban isa in sa ka abu kayi ba??” Yace “Toh shkkn, bari in je” Daga haka ya juya ya fita parlon, sai da ta bisa ta tabbatar ya shiga

dakin Hajja sannan ta koma parlonta, Ya d’an shafa kai bayan sun hada ido da Umma da ladabi yace “Ina yini” Banxa tayi masa, su Maimoon suka gaishe sa yace “Lafiya lau” Jiddah dai tunda ya shigo bata kalli inda yake ba idonta na kan akwatuna, Hajja dake ta fiddo kayan akwatunan tare da Safiyya ta mike tana kallonsa tace “Lafiya ka shigo kayi mana sandandan a kai Aliyu?” Yace “Takardan da na baki nake so in amsa yanxu” Hajja ta kalli Umma tace “Kinga jaraba ko, tun fa ban tafi Masar ba ya bani wasu shegun takardu da ban san isilinsu ba yanxu, shekaranjiya ya xo nace masa yayi hakuri ban san wani shirgin suka shigw ba amma har gidana xan sa aje a bude mu shiga mu bincika ko da rabon a gani, a haka muka rufe kess din da shi, to meye yanxu xai dawo ya tsaya min in basa takardu kamar wasu takardun jaraba, to gaskiya ban san isilinsu ba ka rabu da ni, ni bance

ka dauko takarda ka bani ba” Daga haka ta ci gaba da abinda take, Umma ko kallon direction din Abuturrab bata yi ba banda daure fuska da tayi, Hajja ta dauki wani gyale me kyau ta jefa ma Maimoon tace “Gwada wannan” Umma ta girgixa kai tace “Hajja nace ki bari don Allah, wannan bai dace ba…” Hajja ta mike ta katseta tace “Kinga baiwar Allah tashi kiyi

wucewarki in gama abinda nake, babu ruwanki da harkana, kin wani narka uban kiba kina bani oda kamar yar ki, nace ki tafi asibiti a dubaki kin ki, Da a Masar ne da tuni an kai asibiti wllh, to kuma ina ruwanki da abinda nake banda dai kawai kina kanwar uwar Aliyun uwa daya uba daya” Umma ta mike tace “Toh Allah ya sanya alkhairi na ga lefe sun yi kyau Maa sha Allah, Allah ya nuna na yan baya haka” Hajja tayi banxa da ita, Umma ta nufi kofa ta fita, Hajja tace “Banda kema cutar Aliyun xaki yi tunda ba ke kika haifesa ba kuma haushinsa kike ji kamar ki kashesa, wacece ita wannan yarinya da xa a kai ma lefe guda sha biyu komai na ciki kuma dozen dozen, ina kokarin ragewa kuma xaki kawo min raini, to wllh baxai sa6u

ba, Dukiyar Aliyu ba banxa ba…” Rungume hannu Abuturrab yyi yana kallon Hajja, ta dau atamfa daya me tsada ta jefa ma Jiddah tace “Yayi maki kyau ko a canxa?” Jiddah ta bude ido sosai tana kallon Hajja, ta dau jaka ta jefa ma Maimoon ma, a takaice dai sai da ta ajiye ma Jiddah atamfa, mayafi, da jaka da takalmi da kayan kwalliya, su Maimoon ta basu kayan kwalliya da mayafai kawai duk don sbda haushin abinda Umma tayi mata, Jiddah dai gabanta sai faduwa yake tana kallon kayan gabanta, Hajja ta nemi waje ta xauna tana kallonsu Maimoon tace “Toh ku kulle masu kayansu, Allah ya sa albarka a abinda suka rage” Maimoon da Safiyya duk suka rufe akwatunan, Sai a sannan Abuturrab ya juya ya fita daga dakin, sai bayan da ya fita Hajja ta nemi ledoji duk ta sa ma kowa abinda ta basa a ciki, Jiddah dai duk jikinta yayi sanyi ta ma kasa ta6a ledan da Hajja ta ajiye mata a gabanta, Hajja tace “Ki tafi kice ma Zubaida take ko wa, kice mata baxata bani ruwan xafin bane in shiga makota in samo?” Jiddah ta kalleta don bata san ko da wa take ba, Hajja tace “Da ke nake, tunda barinsu kika yi da rufe akwatin kin xauna kamar sarauniya, banda dai Allah ya rufa

maki asiri Usman ya rufa maki asiri ai da ke xa ayi ma kishiya yanxu, to kamar ya san da haka yasa aka sakeki” Mikewa Jiddah tayi ta nufi kofa ta fita, xaune ta tadda Abuturrab shi kadai a main parlor, duk da sun hada ido tayi wucewarta xuwa kitchen, bata tadda mai aikin a kitchen din ba, tayi ta tsayuwa daga karshe kuma ta fito, taki kallon inda Abuturrab yake ta wuce dakin Hajja, tana kallon Hajja tace “Hajja bata kitchen din” Hajja tace “Toh ta ci kanta, tafi da flask dina idan kin ga an daura ruwa ki juyo min ko bai yi xafi ba, tun daxu nake bin bakar matar ta ban ruwan xafi in sha shayi ta ki, Da a Masar ne wnn ruwan da aka tsuga yau ko wani gida kya ga butan tafasasshen shayi da kofuna kowa na ta sha” Jiddah bata ce komai ba ta dau flask din ta fita, har sannan Abuturrab na xaune

parlon, tayi wucewarta kitchen, ta bude tukunyar da ta gani kan gas taga ruwa ne amma bai tafasa ba, ta dau cup kenan xata fara xuba ruwan cikin flask aka bude kofar kitchen din, sosai taji gabanta ya fadi wanda hakan yasa bata san lkcn da ta saki flask din hannunta ba, da sauri ya karasa ya amshi cup din ruwan xafin hannunta shi ma kar ta sake, iyakar rikicewa ta rikice a lkcn, cikin rawar murya tace “Ina yini” jin bai amsa ba ta durkusa ta dau flask din ta ga ya fashe, sae a sannan ta kallesa hankali tashe tayi narai narai da ido tace “Na shiga uku flask din ya fashe, me xan ce mata?” Yace “Ni kike tambaya?” Ta goge hawayen da ya kawo idonta, yace “Toh yanxu da kika hadani da Umma da Every of my family sae aka yi yaya?” Bata tsaya basa amsa ba tabi gefensa rike da flask din xata fita kitchen din ya jawota, kallon mamaki tayi masa yace “Ki bani amsata” Tace “Ni bani da amsan da xan baka” ya dinga kallonta, taki yarda ta kallesa, ya karbi flask din hannunta ya fita ta bi sa da ido, Hajja ta dinga

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button