
13
Akai-akai take zuwa gaida tsohuwar sarakuwarta, duk sati ta Kai Abdul yai mata hutun karshen mako, su da kansu dangin uban suka raba yadda yaron zai rinka ziyaryar ko'ina don ya saba da sauran 'yanuwansa.
Ko yaushe Rahima ta ziyarci Hajiya saita yi mata fadan kin yin aure, a gida ma tun iyayen nayi sun gaji sun saka mata ido, yaruwarta Maryam ma na irin nata kokarin don ta ciwo kanta su zama matan abokai duk tayi kunnin uwar shegu.
Wannan satin Abdul gidan takwaransa yai weekend, ya daukosa ya maido gidan Hjy don mamansa nan zata taho daukarsa kasancewar Zuwaira bata gari. Tunda suka shiga gidan Abdul ke manne da Haseeb yaki yarda ya sauka daga cinyarsa balle yaje wajen kakar Saida tayi masa dabara aka samu da kyar mairo mai aikinta ta goyasa suka nufi wake sannan ya gaisa da mahaifiyarta..
Hajiya tace “Yaron Nan ya shaku da Kai Kwarai da gaske.”..
Ya amsa “Haka kowa ke Fadi, gashi yana jin maganata ko rigimar banzan sa ya fara yaki sauraren kowa Ina masa magana zai daina.”
Tayi shuru cikin tunani kafin ta furta “Daman Rabi’u yace danka ne dole yaji maganarka.”
Yace “Dalili kenan da in har ya gama nursery mamansa bata yi aure ba zan karbi dans kawai tunda daman an bar mata shi bisa yarjejeniyar zamu amshi abinmu ne idan zata sake aure to tunda ba alamun hakan gara mu karbeshi kawai.”
Ta zaro ido ” Zaka tayar mata da hankali, da wanne zata ji, yaron nan shi take gani tana jin sanyi, idan an nuna mata fun karfi a kansa zaku dau hakkin yarinyar Nan.”
Ya bata fuska “Ai munyi mata Kara Hajiya, Ni ke, ‘yanuwanta ita kanta da sauran jamaa sun san haka sai dai in za aki gaskiya.”
Ta daga masa hannu “Naji, naji meye hujjarka na son amsar sa?”
Ya gyara zama “Hujjata ya dawo cikin ‘yanuwansa ya zauna gaba days ba a rinka yawo da hankalinsa ba, Kuma ke da kike wannan magana da zaran ita iwar tasa ta sami miji ba dawo mana dashi za a ayi ba?”
Ta dade Bata ce dashi komi ba zuwa can tace “Hakane na amince da batunka amma Ina ganin da abinda za ayi a magance wannan matsalar ta bangarenmu da na uwar yaron saurara:
Ni a hakikanin gaskiya tunda Allah ya amshi ran danuwanka nike tunanin baka shawarar auren Rahima....
Bai bari ta karisa bs ya buga kirji ya zabura kamar zai tashi tsaye ya koma ya tsugunna jikinsa ba inda baya rawa, ya kama kansa da hannu biyu ya rinka jinjina maganar a ransa, nan take idanunsa suka rikide suka canza launi maimakon farare sol, ya bude baki yai magana kalmar ta kasa fitowa ya koma ya zauna yaraf saboda matukar sanyin da jikinsa yayi sai kace Wanda ya kwana ya yini Yana aikin wahala ba ci ba Sha.
Ta dauki tsawon lokaci kafin ta kallesa da kyau tace “Maganar da nai maka na auren ne ya firgita ka har ka fita hayyacinka?”
Yaja dogon numfashi ya saki ajiyar zuciya, sannan ya dago Kai a hankali ya kalli mahaifiyarta yace “Hajiya idan ma auren zan kara in rasa wace zan aura sai matar kanina da ya rasu, ki tuna yadda muke dashi fa, idan anyi hakan ba a kyauta ba.”
Ta danyi murmushi saboda tayi niyyar hada auren nan ikon Allah ne kadai zai hana yuwwarsa. Tace “Ni kuwa a nawa tunanin yadda kuke da danuwan naka ne zaisa ka amince a kulla wannan abu don kaji dadin rike amanar da ya damka maka?”
Ya girgiza Kai “Kayya ba sai na kaiga hakan ba duk inda take zanyi kokarin taimaka mata gwargwadon zarafina, yaro kuwa dama namu duk da haka ba Zan tauye mata hakkinta matsayinta na uwa ba dole zamu bata damar kulawa da al’amuran danta a duk lokacin da bukata ta taso.”
Hjy tasha mur “To ka ga ni shawarar dana yanke kenan kaje kayi nazari, na baka sati guda kacal bayan haka ka taho ka fada min abinda ka yankewa zuciyarka, yi ko tsallake maganata?”
Da jin zancenta yasan ba zata kara saurarensa ba,bai hana ya durkusa yana rokonta Allah da Annabinsa ta bar wannan batun da baida ko dadin ji.
. Tace ” Ka daina yi min magiya, Wai ma tsaya tunda ka girms kasan ciwon kanka na taba tursasaka kayi min abinda nike so ko kuwa na taba baka shawarar da ba kaga amfaninta a rayuwarka ba?
Yace “Ah ah!
Tace “To kaje ka dawo bayan sati guda Ina saurarenka, na riga na gama maganata.”
Yayi shiruuu ya rasa me zai sake ce Mata in har zata sauraresa kenan, yafi kowa sanin halin mahaifiyarsa kaifi daya ce ita, idan ta tsaya akan abu babu daga kafar ba ja da baya don haka Kar ma yace zai sake bata baki, ta riga ta kudurtawa ranta sai abinda Allah yayi kenan.
05/09/2020, 12:14 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by jami
14
Hjy Kaltume bata tsaya nan ba, aikawa tayi makarantar da Rahima ke koyarwa tace direba ya daukota yace tana nemanta.
Ba a jima ba ya hangeta ta fito tare da wasu malaman bayan an tashi, ya tareta ya durkusa ya gaisheta ta kallesa cikin mamaki “Bala lafiya?”
Ya amsa “Lafiya kalau Hajiyar ce ke nemanki da gaggawa.”
Alamun damuwa ya bayyana a fuskarta, kace kuma lfy? Bata taba min haka ba ka tabbata ba matsala Bala?”
Yace “A sanina ba komi.”
To shikenan mu hanzarta Amma sai mun tsaya in shiga gida in Fadi Kar Umma taga ban dawo da wuri ba su damu.”.
Yace “Ai tun hanyata ta zuwa na shiga na fadowa Umman uzurun Hajiyar kamar yadda ta umurceni.”
Jikinta dai yai sanyi, ta shiga sake-saken zucci har suka isa. Ta shiga cikin gidan da sassarfa, ta isko Hajiyar a tsakar gida tana alwala, ta saki ajiyar zuciya don a zatonta ko rashin lafiya ce, Hajiyar taga alamun a firgice take, ta danyi dariya tace “Maraba lale Rahima, yi hakuri ‘yan nan ban so firgita ki ba, zo ga buta kiyi alwala.”
Saboda jin nauyinta tace “Na riga nayi, a zahiri kuwa tana period.
Kai tsaye ta shige dakin, Hajiyar ta miko mata kulolun abinci tace “Ci abinci kafin inyi Sallah.”
Ta zuba abincin amma ta kasa cin ko loma guda sabida tsananin tunani.
Ta kosa ta kare adduoin da take yi bayan idar da Sallah.
Zuwa wani lokaci ta Kai makura kagara da son jin dalilin nemanta, da kyar ta amsa gaisuwar Mairo data shigo daidai lokacin.
Hjy Kaltume ta aje tasbaha bayan shafa adduarta ta juyo tana fuskantar Rahima tare da kallon plate din abinci ta danyi murmushi ” Ba ki ci abincin ba lafiya?”
“Na koshi ne.’
“Ko dai kin razana da sakona ne?”
Ta gyada kai “Gaskiya na dan firgita tunda baki taba min irin wannan Kiran ujula ba.”
“Karki damu alkhairin.”
Rahima tace ” Hajiya meke faruwa?”
Hajiya tace “Kafin kiji komi Ina son sanin shin ya kika daukeni lokacin da kike auren marigayi da yanzun?”
Tayi wani da fuska “Hjy ban fahimce ki ba.”
Hajiya tace “Abin nufi wane matsayi kika bani a zuciyarki.”
Ta saki fuska tace “Baki da wani matsayi a gareni daya wuce na uwa tun a da da Kuma yanzun saboda kin rike tamkar ‘yar da kika haifa a cikinki, baki taba nuna min rashin kauna ko na dakika guda ba, akwai lokutta da dama dana kan tuna korafin marigayi kan cewa kamar kin fi sona dashi, na kance don baki da diya mace ce shiyasa kike kaunata amma a zahiri kishin yadda muka shaku yake.”
Hajiya tace “Alhamdulillah naji dadin wadannan kalamai, Ina so ki sani har gobe ina kaunarki Rahima, kauna fisabilillah irin Wanda Allah ke dasawa mutum, halayenki suka karfafa kaunarki a zuciyata. Itace Kuma tasa nayi tunanin sama miki miji Wanda banyi hakan ba Saida nayi nazari sosai na tabbatar idan Allah ya hada zuciyoyinku anyi auren nan zaku dace da juna matuka.
Rahima tayi wani irin gingirin tace " Miji Hajiya? Gaskiya ban shirya sake aure yanzu ba don ban samu Wanda ya kwanta min a rai kamar Rabiu."
Hajiya Kaltume tace “Na fahimci haka, wanda na sama miki zai kwanta miki a rai ne idan kuka shaku da juna, ina tabbatar miki zaku sami ingantacciyar rayuwar auren da zai ba kowa sha’awa. Nasan haka ne kuwa saboda sanin halayyanku kusan daya ne, na lakanci ke yarinyace data san ya kamata, kinsan girman na gaba, kina da hakuri da juriya da dauriyyar kowacce irin matsala ta taso miki, kinada tawali’u , kinsan yadda ya dace ki zauna da wanda ke matsayin mijinki cikin ladabi da biyayya, kin iya mutunta mutum cikin kowanne yanayi, kinada tausayi da jin maganar na gaba dake koda abinda zai gaya miki bai miki dadi ba. Rahima ke yarinyace mai yawan ibada, rayuwar duniya bata shagaltar dake barin bautar Ubangijinki ba, kina daure rashi, kiyi farin cikin samu komin kankantarsa, kinada yasan kyauta ba irinta almubazzaranci ba, da wuya inji kin Fadi karya komi rashin gaskiyarki, a yayinda gaskiyar ta zama Miki abin Fadi duk runtsin da kika shiga, baki da kyashi balle hassada ko munafunci. Kin zauna da mijinki damu tsakani da Allah.. Wadannan halayye naki sunzo daidai da namijin da nike so ki aura Rahima, zan iya cewa ma wasu abubuwan sunfi naki inganta kasancewarsa namiji, Kuma ya dandani wahalhalun rayuwa fiye dake amma duk da haka bai gaza ba.”