NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Rahima tayi kasake, gaskiya tayi mata yawa, ba shakka Hajiya ta santa tamkar tafin hannunta, lalle ta lakanceta tsaf fiye da yadda ta lakanci kanta, idan kuwa haka halin mutumin yake lalle ta samu abokin rayuwar aure irin Wanda take mafarkin samu tun tasowarta zata Kuma iya zama dashi saboda halayyensa ko bata son sa…

Tunanin So da tayi yasa ta juya ta kalli Hajiyar dake kallonta, tayi saurin dukar da Kai kass tace “Hajiya naji bayaninki Kuma nagode sai dai abin tunani, ya ayi kisan shi din Yana son wannan auren hadi yadda kike so?”

Tace “Amincewarki kawai nake jira, Ina son ji daga bakinki kin amimce da shi ko Yaya?”

Ta Kara sunkuyar da Kai tace “Amincewarki dashi shine nawa Hajiya don nayi imani ba zaki sani hanyar da zan wahala ko yin dana sani ba.”

Hajiya tace “Alhamdulillah kamar yadda amincewata ya zama naki shima din amincewata shine nasa, Amma kafin a fara wanzar da komi kije kiyi nafila ki karanta istikhara ki roki Allah zabinsa Kan al’amarin kamar na kwanaki bakwai, idan kin gama sai inji daga gareki. Nima zan tayaku, Allah ya taimakemu, ameen.”
Rahima tace “Wai a Nan garin yake ko danuwanki ne da ban sani ba?”
Ta boye murmushinta ” Me kike ci na baka na zuba, zaki San ko waye, karewa ma muna fatar kuyi zaman aure tare, kije dai bayan sati dayan zamu fahimci komi da yardar Allah.”
05/09/2020, 22:21 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami

15
Ta koma gida cike da mamakin Hajiyar, ta zayyanewa Umma dukkan yadda suka yi, Habiba tace “To Allah ya yaji shemu alkhairi ai zaman ya isa haka, muma za muyi adduar, Baffanku ma zaiji dadin labarin nan don da yadda zaiyi da tuni ya aurad dake ga duk wanda ya dace…

Kwanaki hudu bayan maganarsu da Hjy Kaltume ta fara sakankancewa sa ikon Allah, Al-Hakeem gwanin hikima da basira. Bayan adduoin data dukufa yi haka kawai take jin wani irin dadi da nishadi a ranta, zuciyarta ta fara kamuwa da kaunar mutumin da labarinsa kawai taji, ko sunansa Bata m sani ba abinda ta manta ta tambayi Hjyr kenan. Shin wanene wannan mutumin da kaunarsa ke neman mamaye mata ilahirin zuciyarta tun kafin suyi ido biyu dashi? Shin wanene mutumin da yake da kwatankwacin halayenta? Wanene wannan mutumin da take rokon Allah dare da Rana cewan ta hadata da irinsa tun tana budurwa? Shun wane irin gwagwarmarya ratuwa ya fuskanta da yasa Hjy ke jinjinawa?

Tun kafin ta gansa tausayunsa ya cikata har taji ta matsu ta kosa ta gansa ko hankalinta ya kwanta.”

Umman tasu ta sade tsaye tana magana bata ji ba har Saida ta buga kofar dakin da karfi tayi firgigit ta dago Kai…
“Meke damunki haka na dade tsaye Ina magana baki san Ina yi ba?”..

Ta tashi zaune “Umma tunanine kawai ya isheni….
“Kiyi taka tsan-tsan da tunane-tunane nan Rahima, yaro dai ya riga ya rasu, kafin shi maza nawa suka rasu suka nar matansu, ki sahalwa kanki kici gaba da duain Allah ta tabbatar mana da wannan da Hjy tayi batun,itama fa kenan data haifesa ta dangana har itace ke kawo miki wani mijin, don me ba Zaki hakura ba, ko sai kin jawowa kanki wata cutar?”…
Ta mike tsaf tace “Umma naji na daina, bari in shirya inje gidan Maryam, idan kunji shiru can Zan kwana “..
Umma tace “Shine nazo in tambayeki zaki biya ki dauki Abdul ne ku tafi tare?”
Ta girgiza Kai ” A kyalesa can Unma, damunmu za suyi idan suka hadu da Walida..
“Kuma fa gara ya saba da zaman can din ku rinka nesa da juna Kar ayi aurenku ya ishenmu da rigima.”
Ta kalleta “Kaji Umma da wani zance, sai kace an sa ranar auren daga magana, bamu ko San juna ba fa, idan muka hadu abin bai yuwwu ba fa?”
Tace “Ai Ni Ina ji a jikina wannan auren an gama daura shi da iznin Ubangiji.”.
Haka kawai taji sanyi a ranta ko meyasa oho.. Mhmmm ta suri Jakarta ta saka after dress ta lullubeta kanta suka yi sallama ta nufi gidan ‘yaruwa…

Bata sami damar ba ‘yaruwar nata labarin labarin dake cinta ba saboda ta taras da gidan nasu a hargitse, itada Uwargidanta basa ko ga maciji, karin abin haushi harda raba Kan ‘ya’yansu kowa harkarta take da diyanta. Ran Rahima ya baci,hankalinta yai matukar tashi, bata saurari Maryam don ita ta dorawa lefin abubuwan dake faruwa.
Maryam tace “Banyi tsammanin zaki ki fahimta ta ba Rahima, ki duba irin bautar dana yiwa matar Nan da yayanta tun zuwana gidannan tun kafin in haihu na kula da yaranta, Ina bata girmanta, yanzu kuwa na gaji don shiru ba tsoro bane gudun fitina nike yi, yanzun kuwa ban damu ba aje ayi tayi idan tace kule zance cas! Ba abinda zata nuna min, idan tana takama da miji ne nima dashi nike, idan yarane nima ina dasu to sai me? Haka siddan mace ta isheni ta gallabeni tamkar ita ta aje Ni?
“Hhmmmm inji Rahima “Maryam don Allah numfasa ki saurareni da kyau, ya za ayi ki taho ki taras da mace da mijinta da yara kice zaki nuna mata iko? Mijinta fa kika aure…
“Don na auri mijinta sai me, don ita kadai aka halilto shi ne, mijin mace hudu yake, don me idan ta yayo shararta bata zubewa a kansa sai nawa? To na gaji da rainin wayo, ya isa haka.”

Rahima tace “Ban ce bata da irin nata laifin ba don bai yiwwa ace koda yaushe mutum guda ne ke da laifi da duk magana ta tashi, dole ace tanada irin nata problem, kawai so nike ki fahimci bai kamata ki biye mata duk ku haukace koma ince ku kafirce gaba daya ba, haba ‘yaruwa a matsayinki na musulma ki tsiri gaba da ‘yaruwarki musulma, makwabciyarki Kuma?”

Ta kada Kai “To ya kike son inyi, ita ta fara, sau nawa Ina gaisheta tana shareni tun ina daurewa nace mu zuba mu gani, ko abinci na aika mata bata ci sai ta maido min ta wanke tukunya ta dora wani ta ci, naga bai dau wani mataki ba bayan ya gani da idonsa, nace tunda haka ne bari nima in maida martani tunda ni ba shegiya bace da ubana, ta hana yaranta shigowa dakina balle suyi wasa da yanuwansu, tun Ina damuwa na dake na fara ramuwar gayya Wanda tafi gayyar zafi inji hausawa.”

 "Kash! Inji Rahima, da baki biye mata ba, me zaisa ki bar shaidan ya samu gurbin gina katangarsa a zuciyarki, don me ba za kiyi aiki da ilmin da Allah ya hore miki ba ki nuna mata abubuwan da take yi tsagwaron jahilici ne?"

Ta tabe baki "Kishi da jahilar mace ko masifa, duk yadda kika so ki fahimtar da ita ba zata taba ganewa ba, kullum inda kika dosa daban inda ta dosa daban, kina gabas tana yamma, to yaushe zan bata lokacina a aikin banza."

Rahima tace “Da kike kiranta jahila ba gara ita dake ba? Laifinta ragagge ne don dama bata da sanin, ke kuwa kin sani kin take sanin laifi biyu kenan, to wai shi maigidan bai san abubuwan dake faruwa cikin gidansa tsakanin iyalinsa ba?”

“Kwarai ya sani Mana, cewa yayi in dominsa muke muje mu kashe kanmu ba ruwansa tunda yai kokarin sulhunta mu Abu ya faskara.”

Taja tsaki “You see, ya maisheku mahaukata wadanda basu San ciwon kansu ba, tun anan bai isa ku hankalto ba? Shi da kuke kishin dominsa bai damu ba Wai ma in mutuwa za kuyi ku mutu, eh lalle yace muku haka, in Kun kashe kanku ai bashi kuka yiwa asara ba illa iyaye, ‘ya’ya da ‘yanuwanku, baida asara Kona miyaun barci iyaka ya auri wasu ya zuba a rufe chapter dinku ku bar ‘ya’ya da abun kunya.”

 Maryam ta juyo "To naji ustaziyar zamani, zanyi nazari in kwatanta in gani, idan da canji in ci gaba, idan babu riba Zan watsar mu ci gaba da zaman doya da manjan don babu macen da zata takani in kyale."

Rahima tace” Allah ya ganar damu baki daya, Kinga da na taho da niyyar kwana amma na fasa don ba zan iya zama gidan da ake gaba ba “

Nan da nan ta marairaice “Don Allah yi hakuri na bari, muyi kwanciyarmu.”.
Ta nufi kofa “Ba zan tabbatar da kin bari ba sai munje har dakinta na gaisheta tukunna, mu dawo in baki labarin dalilin zuwana.”
Da kyar ta amince suka tafi, suka sallama ta amsa,suka shiga ciki.
Tayi mamakin ganin ‘yaruwar kishiyarta da suka shafe sati biyu suna gaba da juna, da ita kanta. Rahima ta gaisheta tamkar bata san me ke faruwa ba ta amsa, suka Dan jima suna kame-kamen magana, zuwa can Nafi’u yaron da Maryam ke goyo ya nufi gaban Tv ta ya dauko wata flower vase na glass, uwar tayi saurin tashi ta amsa ta bubbugeshi.
Hjy Suwaiba ta kalleta “Meye na dukan wannan Dan yaron kinada hankali kuwa?
Ta amsa “Ba kiga barnar da zai yi bane?”.
Hjy Suwaiba ta dauki vase din ta sake mikawa yaron “Idan ya fasa naki ne?
Maryam tayi shiru
Rahima tayi murmushi “Nima shi na gani yaro da kayan uwarsa.”.
Hjy Suwaiba tace “Kila so take in bar mata danta ko daman Walida ce tawa, ta rike kayan barnarta kin ganshi mummuna.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button