
Ta kada Kai “To ya kike son inyi, ita ta fara, sau nawa Ina gaisheta tana shareni tun ina daurewa nace mu zuba mu gani, ko abinci na aika mata bata ci sai ta maido min ta wanke tukunya ta dora wani ta ci, naga bai dau wani mataki ba bayan ya gani da idonsa, nace tunda haka ne bari nima in maida martani tunda ni ba shegiya bace da ubana, ta hana yaranta shigowa dakina balle suyi wasa da yanuwansu, tun Ina damuwa na dake na fara ramuwar gayya Wanda tafi gayyar zafi inji hausawa.”
"Kash! Inji Rahima, da baki biye mata ba, me zaisa ki bar shaidan ya samu gurbin gina katangarsa a zuciyarki, don me ba za kiyi aiki da ilmin da Allah ya hore miki ba ki nuna mata abubuwan da take yi tsagwaron jahilici ne?"
Ta tabe baki "Kishi da jahilar mace ko masifa, duk yadda kika so ki fahimtar da ita ba zata taba ganewa ba, kullum inda kika dosa daban inda ta dosa daban, kina gabas tana yamma, to yaushe zan bata lokacina a aikin banza."
Rahima tace “Da kike kiranta jahila ba gara ita dake ba? Laifinta ragagge ne don dama bata da sanin, ke kuwa kin sani kin take sanin laifi biyu kenan, to wai shi maigidan bai san abubuwan dake faruwa cikin gidansa tsakanin iyalinsa ba?”
“Kwarai ya sani Mana, cewa yayi in dominsa muke muje mu kashe kanmu ba ruwansa tunda yai kokarin sulhunta mu Abu ya faskara.”
Taja tsaki “You see, ya maisheku mahaukata wadanda basu San ciwon kansu ba, tun anan bai isa ku hankalto ba? Shi da kuke kishin dominsa bai damu ba Wai ma in mutuwa za kuyi ku mutu, eh lalle yace muku haka, in Kun kashe kanku ai bashi kuka yiwa asara ba illa iyaye, ‘ya’ya da ‘yanuwanku, baida asara Kona miyaun barci iyaka ya auri wasu ya zuba a rufe chapter dinku ku bar ‘ya’ya da abun kunya.”
Maryam ta juyo "To naji ustaziyar zamani, zanyi nazari in kwatanta in gani, idan da canji in ci gaba, idan babu riba Zan watsar mu ci gaba da zaman doya da manjan don babu macen da zata takani in kyale."
Rahima tace” Allah ya ganar damu baki daya, Kinga da na taho da niyyar kwana amma na fasa don ba zan iya zama gidan da ake gaba ba “
Nan da nan ta marairaice “Don Allah yi hakuri na bari, muyi kwanciyarmu.”.
Ta nufi kofa “Ba zan tabbatar da kin bari ba sai munje har dakinta na gaisheta tukunna, mu dawo in baki labarin dalilin zuwana.”
Da kyar ta amince suka tafi, suka sallama ta amsa,suka shiga ciki.
Tayi mamakin ganin ‘yaruwar kishiyarta da suka shafe sati biyu suna gaba da juna, da ita kanta. Rahima ta gaisheta tamkar bata san me ke faruwa ba ta amsa, suka Dan jima suna kame-kamen magana, zuwa can Nafi’u yaron da Maryam ke goyo ya nufi gaban Tv ta ya dauko wata flower vase na glass, uwar tayi saurin tashi ta amsa ta bubbugeshi.
Hjy Suwaiba ta kalleta “Meye na dukan wannan Dan yaron kinada hankali kuwa?
Ta amsa “Ba kiga barnar da zai yi bane?”.
Hjy Suwaiba ta dauki vase din ta sake mikawa yaron “Idan ya fasa naki ne?
Maryam tayi shiru
Rahima tayi murmushi “Nima shi na gani yaro da kayan uwarsa.”.
Hjy Suwaiba tace “Kila so take in bar mata danta ko daman Walida ce tawa, ta rike kayan barnarta kin ganshi mummuna.”
Maryam ta kalli Rahima “Kinji ta ko? Wallahi tunda aka haifeshi take tsangwamarsa Wai Walida ta fishi kyau ko Ina kyaun da katon hanci oho._
Hajiya Suwaiba tayi dariya ” munji ba komu muma da kayan gyara, naki a sa masa ‘yankunne da janbaki mu gani.”
“Ah ah Hjy gaskiya cun fuskar tayi yawa, ki dai rike taki mu rike namu.”
A haka suka ci gaba da wasa da dariya har kusan magriba sannan suka koma dakin Maryam suka yi Sallah. Suna idarwa Hjy Suwaiba ta aiko musu da kulolin abinci wai a kawowa Rahima, da gani abincin yafi karfin ita kadai dole suka ci tare da Maryam din ita ta fasa dora tukunya. Rahima ta kalleta tace ” Don Allah da kika shiga dakinta, kikai Mata magana gashi har kinci abincinta me ya rage a jikinki? Inda za a bude Miki file dinki yau kiga dimbin ladan da kika samu da ba zaki yards ki kara yin gaba ba koda wasa.”
“Wallahi Kuma Nima sai naji wani irin dadi a Raina, duk kuncin da nike ji a zuciyata ya yaye na yarda sai kaso abu ya dameka yake damunka din.”..
Rahima tace abinda har yanzun mu mata bamu gane ba kenan, mu ke creating ma kanmu problems din da zasu dawo su dame mu, namiji ba ruwansa, sai un har kunyi dace da Mai kula ne zai fahimci halinda kuke cikin, wani ko ya gani ba abinda ya damesa tunda yawancinsu sunfi son haka, su tara Mata cikin gida ayita adawa a kansu, ya fito Yana jin dadi da hura hanci ya rinka ikrarin sabida tsananin son da kuke masa kishi ya hanaku zaman lafiya. Wani shaidanin zaman lafiyar ce bai so, yana ganin kun hada kai sai ya kasa sukuni ya shiga zargi da fargaban shifa sai yadda kuka yi dashi kenan domin da wuya daya ta yarda a ci amanar guda shi kuwa bai son hakan, yafi son ya zama bakin ganga, ya buga nan, ya Fadi gaibu can, yai munafunci a nan sai kunada kyakkyawar kula zaku gane in ba haka ba sai kuga kowacce ta fito tana kuri da fankamar ita yafi so.
Idan anyi dace da irin mazan da suka san ciwon kansu sai kiga su zaman lafiyar suke matukar bukata a gidajensu, idan Allah yasa ya dace da matan kwarai sai sai ya kula dasu matuka ya rinka kyautata musu har kiji danginsa na fadin sun mallakeshi sun gama Mana dashi alhalin jin dadin zaman lafiya da kwanciyar hankalin da yake samu dasu ya haifar da hakan. Kin ganni nan Maryam bana shakkar zama da kowacce irin mace Allsh zai hadani da ita matsayin kishiya.”
Ta gatsina baki “Karki cika baki Rahima, me kika sani game da zama da kishiya, kowacce mace fa da nata salon munafunci da kisisinar data kware, idan an debe masu shige-shigen gidan bokaye da malamai don wata ba zata zauna dake da bakin hura wuta kadai ayi kishi ba.”
Tayi murmushi “Aunty Maryam kenan ai ba wani cika baki, in har hakane Kuma Ina iya ce miki yes na cika baki ne domin nima da nawa baiwar da Allah yai min, ba wani abu bane da ya wuce kakkarfar madogora.”
Ta kada Kai “Ko Zan San wane irin madogara ne?”
Ta girgiza Kai “Nima ki bini bashi zuwa nan gaba in har Allah ya kaddareni da auren kiga matsayins zamana a gidan mijin da wajen shi kansa mijin tukunna, yanzun dai muyi sallar isha’i ki bani amsar tambayata ta tuntuni don Ina jin ga wannan karon na fada kogin nan na so da kauna sai dai ko za ku iya tsamo ni?”
06/09/2020, 19:35 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by jami
16
Karfe tara na dare sun nutsa cikin hira, har Hjy Suwaiba ta shigo neman shawara wajen Rahima, sun tattauna kan problem din yaron kanwarta data haifa kurma, tayi musu sallama ta tafi da yake Alh a dakinta yake.
Har zasu rufe kofa, Alh. Abbas ya shigo suka gaisa da Rahima kana ya roketa data fita su gaisa da abokinsa da har lokacin yana magiyar son aurenta.
Ta shiga falon ta sallama fuska a murtuke ta gaisheshi, ya amsa yaci gaba da ‘yan dabarunsu na maza don ta saki ranta. Rahima ta zauna kamar wata mutum-mutumi,ta rinka mamakin lokacin da ta rayawa zuciyarta amincewa ta auri Alh. Abbas, Lalle da tayi wauta, yes a da can da bata San muhimmancin soyayya ba zata iya zama dashi but a yanzun Kam sai dai yayi hakuri, soyayyar wani ya riga ya fara shiga zucciyarta. Wani wa? Ta tambayi kanta, hhmmm wannan wauta nata da yawa yake, to Wai why take jin son bawan Allah nan da aka mata maganarsa?
Alh Suraj ya gaji ya gyara zama tumbinsa ya Kara bayyana cikin babbar rigarsa yace “Rahima ko don nace ba Zan amince kici gaba da aiki bane yasa ba Kya ra’ayina? Idan wannan ne na canza shawara wallahi, na amince kici gaba da aikinki, gidanki Kuma daban zan aje ki “
Ta gyada Kai “Ko kusa Kar tunaninka ya Kai can, aure ai nufin Allah ne, idan ya kaddaro ba makawa, mu dai ci gaba da adduar zabinsa.”
Yace “Lalle kin cika ‘yar boko, Baki ce eh ko ah ah ba duk da na fahimci komi, duk mai hankali zai gane inda kika dosa, sai dai na hakura, ban Kuma ji zafi ba saboda baki nuna kwadayin abin hannuna ba, nagode Zan tayaki addua, Ina rokon idan lokacin auren ta taho a kawo mun kati da goron gayyata, Zan m bada gudumuwata matsayin yayan amarya.”..
Tace “Godiya nike sosai Allah saka da khairan.”
Yace “Ba komi Rahima.”