NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Me zai hana suyi hakuri da juna har mai hadawa ya raba, ko tunanin mutuwa ya isa katsewa duk mai imani hanzari, rayuwar guda nawa take mutum ya tsaya Yana batawa kansa lokaci, duniyar guda nawa take, dubi yadda Allah ya dauke Rabiu farad daya aka raba Rahima da mijin da suke zaune lafiya, yaronta ya shiga maraici ko shi bai isa bawa tsoron Allah ba? Wannan duniyar da ba matabbata ba? Hawaye suka rinka gangarowa zuwa kuncinta.
Rahima ta gani ta gigizata cikin damuwa “Lafiya kuwa?”

“Hawayen godiyar Allah ne da ya kubutar dani ya ganar dani ya hana min biyewa sharrin zuciya, wallahi ba domin zuwanki na na kuduri aniyar mugun zama za muci gaba da yi nida Suwaiba don nayi sakacin barin shaidan ya shiga zuciyata ya fara dora min tubalin gina katangar da zai ci gaba da dora bulo Yana zugani Ina hauka, yanzun nasihohinki sunsa duk nayi sanyi na saduda na hakura na barwa Allah dukkan lamurrana, nayi imanin tunda bana nufun kowa da sharri zai kareni idan an nufoni, zai Kuma yi min sakayya muddin aka zalunceni.”

Rahima tayi murmushi “Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga sarkin sarakuna, munyi salati ga Manzonsa Masoyinsa Muhammad SAW, mun godewa Allah da ya baki ikon ruguje wannan ginin, Ubangiji ya Kara Mana kariya da kayangar karfe da shaidan la’ananne ya karemu daga dukkan sharrin abin ki. Abinda Nike son ki gane dukkanmu Nan masu laifi ne kullum cikin daukar zunubi muke amma Ubangiji ya Kan yafe mana idan mun roki gafararsa, wani zunubin ma ko bamu roka ba sai ya shafe mana kasancewarsa Mai tausayi da jinkan bayinsa, to kai waye da zaka ce ba zaka yi hakuri da wasu al’amurra dake faruwa da Kai ba, balle ka yafe, kana ajizi kaskantacce? Haba don Allah ki zage damtse ki bautawa Ubangijinki, ki kyautatawa mijinki, kiyi tarbiyyar ‘ya’yanki, kiyi zumumci domin Allah, ki kyautatawa iyaye da yanuwa kiga irin daukakar da Allah zai miki.”

Maryam taja numfashi ta rike hannyn Rahima “Wallahi naji na amince na dauka na Kuma gode da nasihohinki ‘yaruwa Allah ya saka miki da khairan. Yanzun kenan mun shafe chapter mutumin naki?”.
Ta zabura ta mike “Ina ai hankalin rabuwa yayi, Ina nan, Ina can, yanzun dai kiyi kwanciyarki don sulusin dare yayi, Sallah zanyi da adduoi na musamman in roki ya Azeez ya nuna min shi ko mafarki ne don hankalina ya kwanta.”

Maryam ta gyara kwanciya ” In Kun hadu Ina Mika gaisuwa da jinjina masa saboda ya sace min zuciyar kanwata ya Kuma tsamota daga duhun jahilcin rashin sanin menene so

Ta shifa toilet ta dauro alwala ta shumfiea sallaya ta fuskanci alkibla tare da natsuwa da kaskantar da Kai domin ganawa sa Mai rufan babu dogara, Mai amsa adduar bayinsa babu shamaki …

Ta dade tana zuba adduointa, ta rufe da salatin Manzon tsira, ata kwanta ba saida sallaci asubah kana tayi matashi da hannunta na dama ta bingire bisa sallayar.

Hanyace data kasu har uku, ta rasa wace zata bi, dama,hagu ko tsakiya? Ta yanke shawarar bin hanyar dake damanta, 'yar siririyar hanyar cike take da itatuwa da ciyayi Korra shataf, bata yi nisa ba sai gata gaban wani tafkeken kogi Mai shakare da  wasu garai-garain ruwa masu kalar sararin sama, nan ta gane baby hanyar wucewa kenan.

Ta juyo cikin hanzari da niyyar ta koma baya nan ta rikice dalilin hanyar ta rikide ta hade danyen ciyawa da itatuwa ga ruwa male-male ta ko’ Ina, daga saman bishiyoyin wasu irin kyawawan tsuntsaye ke kuka tamkar suna busa sarewa, sanyin tafkin nan ya fara ratsata, sanyi ya kadata ta shiga makyarkyata, hakan yasa ta waige-waigen da tunanin ratsawa ta cikin ruwan ta fita wannan wajen, tsoro ya kamata, nan take ta daga hannayenta sama ta fara rokon Maiduka ya kawo mata dauki..

Cikin ikonsa Allah sarkin sarauta sai taga wani mashahurin haske ta ko’ina, wani doki Mai fuka-fuki da ya ratso ta cikin hasken nan a guje ya sauko daf da ita. Jikin dokin ba irin dawakan data sani bane, wannan ilahirin jikinsa kalar azurfa ne, gashin bayansa gazar-gazar da kwarar idanunsa ne kawai bakin kirin.
Tsananin ganin wannan halitta daya cikata yasa bata lura da mutumin dake Kan dokin ba, bata ankara ba taji an dagta sama an dorata bisa dokin nan ya tashi sama suna tafiya tamkar wasu tsuntsaye, basu dade ba taga sun sauka daf da kofar wani farin gida gewaye da furanni, hancinta ya shaki wani hadadden kamshin data rasa inda yake fitowa, kamar tafiyar slow motion ta tsinci kanta cikin wani lambu cike da kayan marmari, ta mika hannu don ciro nunanniyar goba tsawonta bai Kai ga iccen ba, Mai dokin Nan ne ya matso yasa hannunsa ya ciro goban Nan har zai Mika Mata sai dokin yai haniniya ya kada fukafukinsa sai ya fasa bata Saida ya saka a bakinsa ya gutsura kana ya mika Mata sauran ta karba cikin mamaki, har zata Kai bakinta ta tuna bata san ko waye ba, ko kafin ta dago Kai ya haye dokin ya fara tafiya, ta daga masa hannu tana kiransa da muryar data shake, waigo wan da yayi yasa taga fuskarsa a zahiri … Ganin ko waye yasa ta nemi yar da rabin gwaibar da ya bata Amma abin mamaki taki faduwa kamar ansa gam an manne gwaibar a hannunta, cikin hanzari ta sake juyowa ko za tayi katarin sake ganin fuskar.. aka yi dace shima ya sake waigowan yana murmushi a gareta, kamar walkiya dokin da Mai dokin suka bace…

Alhamdulillah Hamdan Kaseeran…
A nan littafin RAHIMA na daya yazo karshe. Za mu ci gaba dana biyun insha Allah.
Ina godiya ga Masoyana a duk inda kuke ina muku adduar fatar alkhairi a gareku.

Nayi kuskure ban bada number waya ba a farkon wannan littafi, to ga masu son saye da nemana ta WhatsApp a neme ni a wannan num 08034243456 WhatsApp kawai plss

Masu son kirana Kuma a nemi a wannan num 07036391747

06/09/2020, 19:50 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by Jami

16
Karfe tara na dare sun nutsa cikin hira, har Hjy Suwaiba ta shigo neman shawara wajen Rahima, sun tattauna kan problem din yaron kanwarta data haifa kurma, tayi musu sallama ta tafi da yake Alh a dakinta yake.
Har zasu rufe kofa, Alh. Abbas ya shigo suka gaisa da Rahima kana ya roketa data fita su gaisa da abokinsa da har lokacin yana magiyar son aurenta.
Ta shiga falon ta sallama fuska a murtuke ta gaisheshi, ya amsa yaci gaba da ‘yan dabarunsu na maza don ta saki ranta. Rahima ta zauna kamar wata mutum-mutumi,ta rinka mamakin lokacin da ta rayawa zuciyarta amincewa ta auri Alh. Abbas, Lalle da tayi wauta, yes a da can da bata San muhimmancin soyayya ba zata iya zama dashi but a yanzun Kam sai dai yayi hakuri, soyayyar wani ya riga ya fara shiga zucciyarta. Wani wa? Ta tambayi kanta, hhmmm wannan wauta nata da yawa yake, to Wai why take jin son bawan Allah nan da aka mata maganarsa?

Alh Suraj ya gaji ya gyara zama tumbinsa ya Kara bayyana cikin babbar rigarsa yace “Rahima ko don nace ba Zan amince kici gaba da aiki bane yasa ba Kya ra’ayina? Idan wannan ne na canza shawara wallahi, na amince kici gaba da aikinki, gidanki Kuma daban zan aje ki “

Ta gyada Kai “Ko kusa Kar tunaninka ya Kai can, aure ai nufin Allah ne, idan ya kaddaro ba makawa, mu dai ci gaba da adduar zabinsa.”
Yace “Lalle kin cika ‘yar boko, Baki ce eh ko ah ah ba duk da na fahimci komi, duk mai hankali zai gane inda kika dosa, sai dai na hakura, ban Kuma ji zafi ba saboda baki nuna kwadayin abin hannuna ba, nagode Zan tayaki addua, Ina rokon idan lokacin auren ta taho a kawo mun kati da goron gayyata, Zan m bada gudumuwata matsayin yayan amarya.”..
Tace “Godiya nike sosai Allah saka da khairan.”
Yace “Ba komi Rahima.”

Goma da mintoci har Maryam ta fara barci Rahima ta tashe ta “Barci tun yanzun?”
“Yes tunda ranar hutun kenan da Alhajin ba nan yake ba.”
“Kina nufun idan yana nan ba Kya hutawan?”
Ta amsa “kusan hakan ne kina wasa da Alhajin nan da kike gani, wallahi duk ta sangarce, daidai da spoon bai iya dauka da hannunsa ya Kai baki idan ina kusa.”
.”Su soyayya masu gari.”
Maryam ta gyara kwancita “Karki zargeni, ke din wa yasan abunsa za kiyi nan gaba, ya kuka kare da Alh Suraj?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button