
Rahima ta sanya rigar barcinta kafin ta amsa “Na fada masa gaskiya yai accepting wai sai Kun Kai masa Iv.”
Maryam tace “Ko nifa bana amince dashi bane just tsokanarki nike da naga baki da niyyar fidda kowa, yanzun shi Wanda Hajiyar tayi magana ne a fagen?”
Wani irin murmushi da farin cikine suka bayyana a fuskarta, Maryam ta daki kafadarta da matashi tace “Lalle wannan ya samu karbuwa a zuciyarki, fada mini ya kike ji?”
Saida ta kwanta ta tasa kafadarta da matashi tace “Za kiyi mamaki Yaruwa domin nima cikinsa nike, ashe mutum Kan so Wanda bai taba gani ba, ni fa ko sunansa ban sani ba, labarinsa ma not in details naji amma na kagu na kosa in gansa inji yaya zanji ranar dana fara ganinsa?”
Tayi dariya “To ya zaki kwatanta abubuwan da kike ji yanzun da wanda kika ji game da marigayi.”
Ta tashi ta zauna “Ai sun Sha banban ‘yaruwa, son Rabiu a hankali ya riga shigata kwatankwacin mutum ta dora ruwan zafi bisa wuta, a hankali ya fara dumi, ya kai ga zafi har ya nuna alamun tafasa sai wutar ta mutu, to yadda ya fara zafi hakan ya rinka hucewa yana sanyi a hankali har ya zamto yanzun na hakura, dana tunasa adduar samun rahama nake ci gaba da yi masa kullum, wannan kuwa gaba daya ruwan ya dau zafi, kafin in ankara har ya tafaso ya fantsama koina, zuciyata na kuna, babban abinda ke firgitani addua nike lamarin na kara tsanani, ko yanzu ji nike kamar in rufe ido in gansa a gabana don inga wane irin mutum ne da yai saurin raunana min zuciya?”
Maryam ta gyara “Tirkashi! Babbar magana, Lalle lokaci yayi da ya dace in baki amsar tambayarki akan menene so?
To a iya fahimtata soyayya itace ni’imar mafi daukaka da Ubangiji yaiwa bayinsa baiwarsa, soyayya itace zuciyoyi dunkule ko a cure waje guda, abin nufi idan mutum yaso wani ko wata son nan kesa ko yaushe a kasance cikin tunanin masoyi, rashin damuwa da kowa sai shi/ita, mutum yakan zama bai jin son ji da ganin kowa sai masoyi kamar yadda kika kasance a halin yanzun.
Ba abinda so bai haifarwa, so na sa mutum yai hauka ya zauce, idan zuciyar bata samu abinda take so ba ta Kan fita hayyacinta, tayi rauni wani har sai an hada da addua kafin a sami komawa normal. So kansa mutum yanke hukuncin da bai Dana sani matukar ya shafi masoyin, a cikin lamarin so na hakika babu shakka, ba munafunci ba yaudara, ba karya balle zargi, so nasa masoyi tsananta addua ga Wanda yake so ko da sani ko basa saninsa ba.
Mutum Kan gane ya kamu da son wani/wata ce ta faduwar gaba a duk lokacinda aka ambaci sunan masoyi, ko gani a zahiri, hoto ko murya. Zaki yawaita son ambatonsa ko son kiji ana labarinsa ko hirarsa, zaki rinka jin son sirrinsa maana halinda yake ciki, jin dadin zancensa, tausayi, fadar gaskiya, nisantar karya in har son na gaskiya ne, haka nan zaki rinka yaba kyautarsa komin kankantarsa da son kema kiyi masa alkhairin komin yawansa, zaki so ki kula da al’amurransu ko yaushe, sannan uwa uba akwai kishi tsakanin masoya na gaskiya but ba irin kishin nan Mai haifar da zargi ba saboda da zaran Kun amince da so da kauna tsakaninku, girmamawa, yarda da aminci ne za suyi tasiri a zukatanku.
Ki kula ba kowanne so ne na hakika ba, majority mu kanyi kuskuren fassara shaawa da kalmar so, irin sa za kiga ko an Kai ga aure lokaci kalilan an fara samun problem musamman idan an riga an gusar da sha’awar, hakuri da juna sai yai karanci saboda ba a gina zaman kan tubalin so da kauna na gaskiya ba. Masoya na hakika Kan jure komi don su zauna da juna.
Maryam ta numfasa ta kalli Rahima kina fahimta kuwa?”
Ta amsa “kwarai kuwa, karance-karancenki ya amfana ta wannan bangaren, kinji bayaninki kamar wata marubuciya?”
Tace “Da kenan dana rinka mafarkin zama daya daga cikinsu..
Rahima tace “Ko yanzun kina iya farawa dauko alkalami da takarda ki gani, gashi kina tsaro min zance kamar kina karantawa ba?”
“Rufan asiri don Allah, ai na kwatanta naga ba ci dole na hakura, nan na Kara yarda da batun wani malaminmu cewa rubutu baiwa ce, duk Wanda Allsh yaiwa baiwar hikima da basira yaita gode masa kullum domin a cewarsa koda mutum ya sauke kundin karatu ba lale ya iya rubutu ba, don sai in Allah ya bashi hikimar ne zai rubuta a karanta a fahimta har a sami darasi ciki a amfana, Kinga shiga hurumin da Allah bai kaddaro maka bama shishshigi ne da karanbani in dai ba so kike in rinka satar basirar wasu ba.”
“Ah ah a Kan me, zauna matsayin da Allah ya aje ki,in kinyi hakan ma ai baki kyautawa kanki ba ko?”
Maryam ta kyalkyace da dariya “Ban ma ja da nisa ba kin sani, dana gwada naga bai yuwwa bane na hakura, na dai ci gaba da saye Ina karantawa Ina karuwa….
“Karuwa ta wani fannin ba, wani bangaren kam karatun kawai kike don jin dadin labari amma ba Kya daukar darasin komi. Da kina dauka da baki biyewa Hjy Siwaiba kunyi gaba ba, da baki bi nata Kun raba kan yaranku ba, zumunci fa kenan kuke neman yankewa tsakaninsu alhalin Ubangiji yace Duk Wanda ya yanke zumunci bai tare dashi gobe kiyoma, ban da haka, mijin Nan naku fa na iya mutuwa ya barku kowa ta kama gabanta zaman tsakaninku ya farraka, amma yaranku dole suyi zumunci da juna sabili da jininsu daya, ko Allah ya karbi ran daya daga cikinku takalihun yaran ya koma hannun dayanku dole, ko Kuma ma ya kasheku gaba dayanku, mijin naku ya auro wasu su o suci gajiyar yaran da kuke tinkahon Kun haifa, kinsan dai ba yadda Allah bai iya juya lamarinsa ba don haka ake son mu kasance masu hangen nesa, idan ka ciza ka hura, idan kace zaka biyewa zuciya sai ya kaimu ta baro tunda batavda Kashi, shyasa ake son mu rinka adduar Allah yasa mufi karfinta, Kar shaidan ya rinjayeta, ya karfafa mana imaninmu, Ni da zanga dayan marubutanmu ko dana nunaki cikin days daga cikin makarantarsu amma masu karatu suji dadin labari kawai ba daukar darasi balle ku amfana.”
Ta bude baki “Tafdijan Rahima yau kin gama dani tsaf…
“No ba haka bane ‘yaruwa, wajibine in taroki idan naga Zaki ksuce hanya in fada miki gaskiya komin dacinta, marubutan fa suna yi don gyaran tarbiyyarmu dana zuriyyarmu don al’ummanmu su samu nagarta mu gyara rayuwar duniya dana lahira.”
Maryam tayi kasake tana saurarenta, yes Rahima gaskiya take fada mata ba karya ko kadan, Ina amfanin badi ba rai?
Wajibi ta taho ta gyara halinta dana zamantakewarta da abokiyar zamanta ko tace makwabciyar ta inji Rahima,ko bata kyautata mata don komi ba tayi don samun ladan, shin sai nawa ma wani lalura ke tasowa daya daga cikinsu Wanda suke takamar shi ya ajiyesun bai nan bai kusa balle ya magance musu? Su jawa suka taimaki juna musamman lalurar rashin lafiya maigidan na can bai ma sani ba sai ya dawo yaji labari? Idan har Ubangiji zai jarabci bawansa ba mu san ta hanyar da jarabawar zata zo mana ba kuwa ya dace mu saduda mu zauna lafiya da juna muyi hakuri tunda ba wace ke zaune kan wata, babu mai korar wata sai in kaddara ta gitta Wanda ba a fata, kowacce da halinta take zaune kota bangaren mijin ne, to wahalar da Kai na menene?
Me zai hana suyi hakuri da juna har mai hadawa ya raba, ko tunanin mutuwa ya isa katsewa duk mai imani hanzari, rayuwar guda nawa take mutum ya tsaya Yana batawa kansa lokaci, duniyar guda nawa take, dubi yadda Allah ya dauke Rabiu farad daya aka raba Rahima da mijin da suke zaune lafiya, yaronta ya shiga maraici ko shi bai isa bawa tsoron Allah ba? Wannan duniyar da ba matabbata ba? Hawaye suka rinka gangarowa zuwa kuncinta.
Rahima ta gani ta gigizata cikin damuwa “Lafiya kuwa?”