NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

“Hawayen godiyar Allah ne da ya kubutar dani ya ganar dani ya hana min biyewa sharrin zuciya, wallahi ba domin zuwanki na na kuduri aniyar mugun zama za muci gaba da yi nida Suwaiba don nayi sakacin barin shaidan ya shiga zuciyata ya fara dora min tubalin gina katangar da zai ci gaba da dora bulo Yana zugani Ina hauka, yanzun nasihohinki sunsa duk nayi sanyi na saduda na hakura na barwa Allah dukkan lamurrana, nayi imanin tunda bana nufun kowa da sharri zai kareni idan an nufoni, zai Kuma yi min sakayya muddin aka zalunceni.”

Rahima tayi murmushi “Alhamdulillah tsarki ya tabbata ga sarkin sarakuna, munyi salati ga Manzonsa Masoyinsa Muhammad SAW, mun godewa Allah da ya baki ikon ruguje wannan ginin, Ubangiji ya Kara Mana kariya da kayangar karfe da shaidan la’ananne ya karemu daga dukkan sharrin abin ki. Abinda Nike son ki gane dukkanmu Nan masu laifi ne kullum cikin daukar zunubi muke amma Ubangiji ya Kan yafe mana idan mun roki gafararsa, wani zunubin ma ko bamu roka ba sai ya shafe mana kasancewarsa Mai tausayi da jinkan bayinsa, to kai waye da zaka ce ba zaka yi hakuri da wasu al’amurra dake faruwa da Kai ba, balle ka yafe, kana ajizi kaskantacce? Haba don Allah ki zage damtse ki bautawa Ubangijinki, ki kyautatawa mijinki, kiyi tarbiyyar ‘ya’yanki, kiyi zumumci domin Allah, ki kyautatawa iyaye da yanuwa kiga irin daukakar da Allah zai miki.”

Maryam taja numfashi ta rike hannyn Rahima “Wallahi naji na amince na dauka na Kuma gode da nasihohinki ‘yaruwa Allah ya saka miki da khairan. Yanzun kenan mun shafe chapter mutumin naki?”.
Ta zabura ta mike “Ina ai hankalin rabuwa yayi, Ina nan, Ina can, yanzun dai kiyi kwanciyarki don sulusin dare yayi, Sallah zanyi da adduoi na musamman in roki ya Azeez ya nuna min shi ko mafarki ne don hankalina ya kwanta.”

Maryam ta gyara kwanciya ” In Kun hadu Ina Mika gaisuwa da jinjina masa saboda ya sace min zuciyar kanwata ya Kuma tsamota daga duhun jahilcin rashin sanin menene so

Ta shifa toilet ta dauro alwala ta shumfiea sallaya ta fuskanci alkibla tare da natsuwa da kaskantar da Kai domin ganawa sa Mai rufan babu dogara, Mai amsa adduar bayinsa babu shamaki …

Ta dade tana zuba adduointa, ta rufe da salatin Manzon tsira, ata kwanta ba saida sallaci asubah kana tayi matashi da hannunta na dama ta bingire bisa sallayar.

Hanyace data kasu har uku, ta rasa wace zata bi, dama,hagu ko tsakiya? Ta yanke shawarar bin hanyar dake damanta, 'yar siririyar hanyar cike take da itatuwa da ciyayi Korra shataf, bata yi nisa ba sai gata gaban wani tafkeken kogi Mai shakare da  wasu garai-garain ruwa masu kalar sararin sama, nan ta gane baby hanyar wucewa kenan.

Ta juyo cikin hanzari da niyyar ta koma baya nan ta rikice dalilin hanyar ta rikide ta hade danyen ciyawa da itatuwa ga ruwa male-male ta ko’ Ina, daga saman bishiyoyin wasu irin kyawawan tsuntsaye ke kuka tamkar suna busa sarewa, sanyin tafkin nan ya fara ratsata, sanyi ya kadata ta shiga makyarkyata, hakan yasa ta waige-waigen da tunanin ratsawa ta cikin ruwan ta fita wannan wajen, tsoro ya kamata, nan take ta daga hannayenta sama ta fara rokon Maiduka ya kawo mata dauki..

Cikin ikonsa Allah sarkin sarauta sai taga wani mashahurin haske ta ko’ina, wani doki Mai fuka-fuki da ya ratso ta cikin hasken nan a guje ya sauko daf da ita. Jikin dokin ba irin dawakan data sani bane, wannan ilahirin jikinsa kalar azurfa ne, gashin bayansa gazar-gazar da kwarar idanunsa ne kawai bakin kirin.
Tsananin ganin wannan halitta daya cikata yasa bata lura da mutumin dake Kan dokin ba, bata ankara ba taji an dagta sama an dorata bisa dokin nan ya tashi sama suna tafiya tamkar wasu tsuntsaye, basu dade ba taga sun sauka daf da kofar wani farin gida gewaye da furanni, hancinta ya shaki wani hadadden kamshin data rasa inda yake fitowa, kamar tafiyar slow motion ta tsinci kanta cikin wani lambu cike da kayan marmari, ta mika hannu don ciro nunanniyar goba tsawonta bai Kai ga iccen ba, Mai dokin Nan ne ya matso yasa hannunsa ya ciro goban Nan har zai Mika Mata sai dokin yai haniniya ya kada fukafukinsa sai ya fasa bata Saida ya saka a bakinsa ya gutsura kana ya mika Mata sauran ta karba cikin mamaki, har zata Kai bakinta ta tuna bata san ko waye ba, ko kafin ta dago Kai ya haye dokin ya fara tafiya, ta daga masa hannu tana kiransa da muryar data shake, waigo wan da yayi yasa taga fuskarsa a zahiri … Ganin ko waye yasa ta nemi yar da rabin gwaibar da ya bata Amma abin mamaki taki faduwa kamar ansa gam an manne gwaibar a hannunta, cikin hanzari ta sake juyowa ko za tayi katarin sake ganin fuskar.. aka yi dace shima ya sake waigowan yana murmushi a gareta, kamar walkiya dokin da Mai dokin suka bace…

Alhamdulillah Hamdan Kaseeran…
A nan littafin RAHIMA na daya yazo karshe. Za mu ci gaba dana biyun insha Allah.
Ina godiya ga Masoyana a duk inda kuke ina muku adduar fatar alkhairi a gareku.

Nayi kuskure ban bada number waya ba a farkon wannan littafi, to ga masu son saye da nemana ta WhatsApp a neme ni a wannan num 08034243456 WhatsApp kawai plss🙏🏿

Masu son kirana Kuma a nemi a wannan num 07036391747

Kasancewar littafin RAHIMA na sayarwa ne masu son saye Acccnt number mu shine 0598537268
GT Bank.

07/09/2020, 21:32 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by Jami

17

  Ta farka cike da mamakin murdadden mafarkin da tayi, cikin gigita ta rinka karanto adduar shugaban ayoyin alqur'ani kana ta dora da adduar neman tsari daga mugun mafarki, tsorene ya hanata jin sautin muryar Maryam da take karatun qu'ani can gefe daya, ta kasa yin wani kwakwkwaran motsi, da kyar ta tashi ta nufi toilet ta sake dauro alwala ta gabatar da sallar dhuha sannan itama ta dauko qur'anin ta fara karatu .

Basu tashi Kan sallayarsu ba saida suka dauki dogon lokaci don sun saba tyn suna gida duk bayan sallar asubah sai sunyi karatun sa’annan su dora sa azkhar din safe don kwadayin dacewa da lokacin amsar addua.

Goma daidai sunyi wanka sun kintsa tsaf, Rahima ta kalli Maryam ‘Ba zanyi breakfast ba, gida zan koma yanzun nasan Umma na zuba idon ganin na koma da wuri.”

Ta kura mata ido “Akwai abinda ke damunki duk kin canza wayewar garin nan, ko baku hadu da surukin nawa a mafarki bane?”

Ta koma ta zauna jiki babu kwari kamar wace aka zare mata lakka tace “Ke dai bari ‘yaruwa, nayi adduoi na roki Allah yadda kika sani but Wanda na gani cikin mafarkina… Kai!!! Ta girgiza Kai, na firgita wallahi.”

Maryam ta kalleta “Shakka kike?”

Ta kada Kai “No mamaki nike ji da fargaban mafarkin nawa ya zama real.”
Maryam ta kalleta cikin damuwa “Kinata kwanare, shin wa kika gani ne?”
Rahima ta jinjina “Hhmmmm bana jin zaki amince da abinda zan fada miki.”

“Me zai hanani yarda after all Allah muka roka Ya amsa mana mene na al’ajabi? Ni wallahi ko waye na yarda na amince shi dinne zabin Allah.”

Ta kauda Kai tayi shiru na dakika kana tace.. Maryam Ya Haseeb fa na gani a mafarkina.”

Duk da dakewan da tayi itama taji mugun mamaki ta buga kirji “HASEEB! Ba dai Dr Haseeb wan Rabiu ba?”.
Hawaye suka ciko a idanunta yayinda ta amsa ” Shi din ne, me hakan ke nufi Maryam?”

Ta taso ta matso kusa da ita ta dafata cikin rarrashi “kwantar da hankalinki za kiyi mu saurari Hajiya muji nata manufar amma a hakikani mafarkinki gaskiya ne,zaiyi wuya aure bai shiga tsakaninku dashi ba Ina ganin tun farko shi Hajiyar ma ke nufi.”

Cikin sheshekar kuka ta dago "In hakura dame? Haba Ina! Idan har shi take nufi na fasa amsa batunta, ba Zan iya zama dashi matsayin miji ba."

 "Kina son zancen yai tsawo kenan, shikenan mu bari har zuwa sauran kwanaki ukun data diba miki mu gani, mu ci gaba da addua Allah ya tabbatar mana da khairan"

Hankalinta a tashe ta shiga tayi sallama da Hjy Suwaiba ta wuce gida.
Nan da Nan Umman ta gane akwai abinda ke damunta tana cikin matsala saboda tunda ta shigo ba walwala a tareda ita, abin mamaki ko Abdul bata tambaya ba.
Har zuwa karfe biyar na bayan la’asar babu canji a tareda Rahima hakan yasa a matsayinta na uwa Umma ta kira cikin daki ta yambayeta meke damunta.

Nan take ta musa cewa babu komi, Umman ta kalleta cikin damuwa tace “Shikenan tunda ban isa ki fada min matsalarki ba.”

Rahima ta saka mata kuka tace “Idan ma akwai matsala nina janyowa kaina Umma imda nayi aurena tuni da ban shiga kangin Nan ba, yanzun ya zanyi da Raina?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button