NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Umma ta Kara rudewa “Ya za ayi in baki amsa tunda ban san damuwar taki ba?”

Da yake sun saba basu boye Mata komi ta zayyane mata labarin mafarkinta da yadda suka yi da Maryam”

Ta dade bata iya magana saboda zancen ya daketa itama amma ta daure ta kalli ‘yarta “To in banda shirmenki mene na tada hankali harda koke-koke? Aure ba nufin Allah bane, matar mutum kabarinsa, kin taba ganin mijin da bai auri matar da ba tasa ba? Idan Allah ya kaddaro Haseeb mijinki ne babu Wanda ya isa ya hana, don haka ki natsu ki barwa Allah muga abinda zaiyi tukunna.”

Tasa handkerchief ta share hawayen dake fitowa tace “Ba abinda ke damuna irin alkawarin dana daukarwa Hajiya na amince da zabinta ba tare da tunanin wai shi take nufi ba, haba Umma ya za ayi wannan danyen aikin?”

Umma ta kalleta “Ta yaro kyau take bata karko, tashi jeki share hawayenki, Zan nemi Hajiyar mu tattauna mai yuwwa in har hakanne.”

Tace "Don Allah Umma idan zaki, ki kwashe kayan Abdul ki Kai musu na hakura dashi, don ina ganin ita kanta Hajiyar sabida shi ta yanke hukuncin Nan, watau Kar in auri wani can daban in tafi dashi."

Ta bude baki tana mamakin kalaman diyarta, lakle sai sunyi da gaske, tace “To Ina Kuma ruwan Abdul da za ayi masa mai gaba daya, ki bari zan maidashi gidansu idan lokaci yayi Kuma don Allah kar in sake jin kin zargi Hajiya kinsan ba zata cuceki ba, ko alama bai dace kiyi furucin da kika yi ba.”

Ta kwana ta yini cikin zulumi da fargaba abinda zau faru. Gaba daya komi yai mara dif, brain dinta ya hargitse, zuciyarta ta kasa sarrafa komi sai tunanin yadda akayi ta amince da so da kaunar wanda bata taba gani ba, to ai yanzun ta daina ikrarin haka, shin ba Ya Haseeb ne ta tsunduma cikin kogin soyayyarsa ba?
Satin data dauka tana adduoi suka cika amma ta kekasa kasa taki komawa gidan Hjy Kaltume, bata aika an dauko Abdul din ba ma, ko da tanada tabbacin Umma ta ziyarci Hajiyar amma bata ce mata komi, ita da Baffa sun sa mata ido sai wani lallabata suke, ta share kowa a gidan hatta Maryam data taho ta rasa gane kanta.

  Babu Wanda bai san asibitin nan mai suna *HASEEB MEDICAL CENTRE* ba, ba don komi asibitin tayi fice ba sai domin kwarewan babban likitan(CMD). Dr Haseeb Junaid Galadanci dogo ne mai dan jiki, launin fatar jikinsa chocolate ne hakan yasa tsakar mallacin da aka yi masa suka fito sosai a gefen kumatunsa a 'yar doguwar fuskarsa wadanda suka kara fito da kyaunsa na zahiri.

Yana da zafin nama sosai, hanzarin nasa ya dace da irin aikinsa watau kwararren likitan da ya shahara yai suna bangaren daya shafi rashin lafiyar kwakwalwa, kashin baya da halittun da suka danganci wadannan ababe masu matukar muhimmanci a jikin Dan Adam 

Dr H.J.G yadda ake kiransa yasan hallitar kwakwalwar bil adama tamkar yadda yasan tafin hannunsa, kazaliza don ya bude kan mutum ko baya ya mayar ya dinke ba wani abu ne mai wuya a wajensa ba, da taimakon Allah duk wata matsala da aka kawo masa akayi sa’a ya duba yai aiki ko bada magani a kanyi nasara.

Dalili kenan da sunansa ya bunkasa tun daga gida Nigeria har kasashen waje, manyan asibitocin ketare ma dashi suke takama don ba inda kafafunsa basu taka ba. Sabida yawace-yawacen da yake yi ne yasa shi jin harsuna daban-daban, yana jin harshen larabci, faransanci, jamusanci, dangane da yaren harsunan kasarmu kuwa tun Yana jami’a ya iya yaren yarbanci, fulatanci dana igbo, abin ban sha’awa duk yaren daya juya harshe Yana yi sai mutum ta rantse daman shine mother tongue dinsa.

Ganin yadda ayyuka suka yi masa yawa, zirga-zirga na neman tauyesa wajen sauke hakkin iyalinsa dana iyaye yasa ya yanke shawarar gina makekiyar asibiti Wanda ya nemi wasu kwararuj likitocin suka hadu suna gudanar da harkar asibitin gadan-gadan.

Babban abin shaawa da yawanci maganar da mutane suke fadi shine ma’aikatan asibitin nada karamci tun daga leburori zuwa nurses da doctor’s dinsu balle shi kanshi uban tafiyar, ta ta shahara wajen tsabta sosai, babu wulakanci tsakaninsu da patients, sun dauki Mai kudi da talaka gudane, patient sunansa patient Kuma Abu guda suka zo nema (lafiya) don haka babu banbanci.
Ba nan ya tsaya ba da kyautatawa patients dinsa ba, da duk ya lakanci basu da halin biyansa hakkinsa ya kan taimaka yayi aikin kyauta tareda kulawa ta musamman.

Daga bayan nan yawanci manyan asibitocin gwamnati ke turo masa da patients yai musu abinda ya dace gwamnatin ta biyasa hakkinsa.
Can kasashen waje ko yaushe irin aikinsa ya taso sukan bugo masa waya ya tafi don ceton rayuwar Al’umma, a dalilin hazakarsa ne suka yiwa sunansa laqani da Mr Brain.
Ga Wanda bai taba ganinsa ba kuna yin ido biyu fuskarsa zata nuna maka alamar mutum ne mai ji da kansa domin miskili ne na karshe. Wani irin mutum ne da samun irin halayensa sai an tona, fuskarsa a daure take ko yaushe, baya dariya gaban kowa amma kuma mutum ne mai saukin kai idan aka fahimci halinsa.
Dr Haseeb mutum ne da bai dauki abin duniya da ita kanta duniyar wata tsiya ba face wajen gwaji da neman tsiran gobe kiyama har ya kance mutane na shirme wajen maida duniyar wajen zama tamkar ba za a mutu a barta ba, mutum ne shi mai sadaukar da kai da maida dukkan al’amurranss ga Allah. Bai da saurin karaya don haka ya fita zakka cikin abokai da sa’oinsa musamman ma da wuya suke gane inda yasa gaba.
Mutum ne Mai son rayuwa don ance ka nemi duniyar tamkar ba zaka mutu ba, ya rike addininsa matukar gaske saboda ance ka gyara lahirarka tamkar yanzun zaka tafi. Ya kanyi wuya a tabashi ya hakura in dai har ya tabbatar da gaskiyarsa, mutum ne Wanda baya karya yakan Kuma kure duk Wanda ya nemi yai masa hassada har sai yaga abinda ya turewa buzu nadi.
Bai da fargaba, bai da tsoro, bai da hayaniya, mutum ne natsatstse kamilalle, bai son raini don bai rana na gaba dashi ba, yana son ayi masa biyayya, bai daukar jita-jita, baya son girman Kai ko nuna Kai wani ne, bai taba daukan kansa wani abu ba, Yana son hira da Wanda ya amincewa, idan har an zauna dashi mutum ne da ake karuwa dashi ta hanyoyi da dama, Allah yai masa laqanin iya zama da mutane.

Haka nan yakan kaunaci duk Wanda ya nuna masa kauna ya Kan guji makiyinsa cikin kowanne hali.

Dr Haseeb mutum ne Mai tsananin kusantar Ubangijinsa, wajen ibada da adduoi neman taimakon Mahaliccinsa a dukkan al’amurran da suka jibanci rayuwarsa, bai Kuma taba tunanin Ubangiji bai amsa bam

Ranar da Mahaifiyarsa tayi masa batun auren matar kaninsa Rabiu ya razana sosai, batun ya dameshi ya tsaya masa a rai matuka, amma damuwar data fi masa ciwo itace yi mata musu sabida in har yana kaunar mutuwarsa to zai so abinda zai bata mata rai, baya kaunar abinda zai sosa Mata rai ko kadan.
A kullum yana danganta samun nasarar da yake a rayuwa da dimbin adduointa ne garesa bayan albarkar da take sa masa kullum.

To yanzun data gangamo aure, auren ma na wace ko a mafarki bai taba tunanin faruwarsa ba ya zaiyi da bukatar ta? Ba wani abinyi illa amincewa da bin umurninta da fatar Allah yasa ya zame musu alkhairi duka.

 Amma ya yankewa kansa the most difficult decision in his life duk da bai yanke shawarar ba sai da yayi adduoi kamar yadda ya saba ya roki Ubangiji fa'ida kan al'amarin, da alamu akwai haske sai kara neman taimakon Allah.

Tunaninsa ya koma Kan yarinyar ko yace matar da ake son ya auran, zuciyarsa ta amince Rahima yarinya ce mai natsuwa da hankali, tanada biyayya tunda bai taba jin ance wani sabani ta shiga tsakaninta da marigayi ba, yasha jin irin yabawar da Hajiya ke Mata, yasan yadda ita din take girmama Mahaifiyarsu wanda mutuntata da take yi me ya Kara haddasa son hada wannan auren. Idan ya tuna yaronsu Kuma, Abdul ya shaku dashi, shima jaksn fiye da ‘ya’yan cikinsa ma wanda bai rasa nasaba da matsalar uwar yaran da tafi son ‘ya’yanta su yini su kwana a can gidansu fiye data kawosu wajen Hajiyarsu. Da ya nuna rashin amincewarsa ta kawo masa uzurin sunfi sakeea a can saboda akwai yara sa’oinsu Kuma tunda shi ba mazauni bane meye na complain.

Yan kwanakin nan da Hajiyar ta diba masa ayyuka sunyi masa sauki don hakane ya Sami daman yin nazari da adduoinsa a natse, ysi reaching decision don haka bai bata lokaci wajen dumfararta da shawarar da ya yanke ba.
07/09/2020, 23:52 – Anty saliha: …ˆRAHIMA…doc by Jami

18

  Ganinsa tunda sassafe a Rana ta takwas da yin maganarsu baisa ta saki fuska, ya durkusa ya gaisheta ta amsa a dakale. Daga can cikin uwar daki Abdul yaji muryar babansa ya tashi daga barci ya fito yana mutsuke idanu, Haseeb ya riko sa ya zaunar dashi cinyarsa ya rungume ya kalli Hajiya yace "Ashe har yanzun bai koma ba?"

Tace “Mamansa bata zo ba Ni kuma ban aika ba.”..
Ya kalli yaron da kullum idan ya hansa sai ya Tina da danuwansa, ya kada Kai tare da kara rungumarsa, nan da nan ya koma barci, Hjy Kaltume tace “Wannan shakuwa taku tayi yawa, muryarka fa yaji yasa ya taso barcin bai ishe shi ba.”
Ya kada Kai hakane, ba a kaishi makaranta ne naga har kusan tara yana barci?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button