NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Hjy. Kaltume ta tattara kayan gabanta ta ture gefe tace “Bari dai in tsaya muyi maganar nan sosai don na fahimci hira kake ji yau, shin me yasa kake son maida hannun agogo baya ne? Na fada maka Kai kadai, na gaya maka tare da ‘yanuwanka, yau ma zan Kara fada maka ni ban raina hidimar da kake min ba, iyaka nafi amincewa da in nemi nawa na kaina, ba sai na jiraka ba balle ‘yanuwanka da basu da hali. Ranar da Allah ya hore maka kayi inyi murna da farin ciki, ranar da baka dashi sai inyi amfani da nawan da kuke rainawa, kaga na rufawa kaina asiri na rufa muku, banda wannan yau da gobe bata bar komi ba, koda nike mahaifiyarku ba lale Allah ya tara min duk masu jin kaina ba, idan Kuma har na samu hakan nasan irin matan da zaku auro? Wata matar ita ke hana da ya kula da iyayensa yadda ya kamata duk da ni alhamdulillah matanku na kwatanta min da’a. To idan duk muka ture wannan batun, ka duba kaga kaine babba, Allah bai ba ‘yanuwanka rufin asiri irin naka ba, kai kake dawainiya dani, kayi dasu da dangina, ka taimaki dangin mahaifinka, Ina tausaya maka kwarai da gaske don ka zama hannu guda ba wani mai tallafa maka, ga iyali ka fara tarawa dole in rinka taimakonka, misali ko haihuwa matarka tayi na baka gudumuwar zanin goyo ban taimaka maka ba?”
Dole yayi murmushin da har kyawawan hakoransa suka bayyana yace “Wallahi Hjy kin ban dariya, amma insha Allah ba zan sake shishishigi cikin hidimominki ba, Allah Kuma ya kara taimakawa.”

“Yauwa yanzun naji batu, to tunda naga ka saki ranka yanzun sai muyi maganar dalilin nemanka.”
Ya amsa “Ina saurarenki, Allah yasa lafiya.”
” Lafiya kalau, batun kaninka Rabi’u ne, kasan na fara yi maka bayanin neman auren da ta fara kwanaki ko? To shine jiya ya taho min da maganar cewan wai iyayen yarinyar sunce inda gaske yake ya fito.”

Haseeb yai kasake na wani lokaci kafin ya furta “Har yanzun yana nan yana shirmen nasa kenan?”
Tace “Wane irin shirme Kuma, yaro na neman raya sunnar manzo?”
“Hmmmm hjy Rabi’un guda nawa yake ne? Ni fa karatu na turasa makaranta yayi ba soyayya ba, don Allah Ina zai kai mata yanzun?”

"Ban gane ina zai kai mata ba, bai isa auren bane ko yaya?" Ko kuwa don ka turashi karatu sai yaki aure, maza da mata nawa ke yin auren su ci gaba da karatun nasu?"

Ya kada Kai “Kwarai ana yi amma ga Wanda ya shirya, yana da muhallin da zai aje matar yanada kamu sayar domin ciyar da ita da daukar sauran lalurorin yau da kullum na shi kansa da ita matar da ya aje. Rabi’u karatu yake Hajiya, duka -duka 200 level yake a jami’a, me zai hana ya hakura ya kare sauran shekara dayan, ya samu abinyi kafin muyi wani batun aure?”

Ta fara harzuka “Da yawan yajin aikin da ake yi a jami’oi ne zai gama karatun nan da shekara gudan? To naji, yanzun ya kake son ayi da iyayen yarinyar, me zamu ce dasu?”

Ya amsa “Ace musu bai shirya ba sai ya gama karatunsa tukunna.”
Tace “To ita Kuma yarinyar da aka ce za a aurar da ita yanzun ne fa?”
Ya bata amsa da “Ta nemi wani ta aura tunda iyayenta sun matsu su aurar da ita, shi Kuma Allah ya bashi wata nan gaba idan lokacin auren nasa yayi.”

Ta fusata “Na fahimci ka shiryawa kowacce tambaya zanyi maka, kawai ka fito fili kace ba zaka taimakawa danuwanka hidimar aurensa ba fakat.”

Ya Kara ladabtar da kansa “Ko kusa ba haka bane Ni a ko yaushe shirye nike in yiwa ‘yanuwana kowanne irin taimako suka bukata daga gareni. Ba wai baba son Rabi’u yai aure bane, tunanina mene na gaugawa,hanzari ba nasa bane, ya bi a hankali mana har Allah ya bashi daidai shi.”

Hjy Kaltu ta juya masa baya “Kai kake da lokacin surutu, da kake gaya min wannan zancen wofin kaninka da kuke uba daya nawa suka yi aure? Gaba dayansu babu Wanda ya haura shekaru ashirin a cikinsu, me yasa baka hanasu ba, wane irin gudumuwa ce baka basu ba, sai yanzun yaro ya Kai shekaru da biyar a duniya ya isa aure kace zaka tauye masa hakkinsa?”

Yace Yi hakuri ban tari numfashinki ba, wadanda kike magana na amince musu ne saboda kowannansu nada shago a kasuwa, sunada abinyi,tunda sun nuna su kasuwancin suke so fiye da karatun, na tabbatar Kuma zasu iya daukar takalihun matansu, amma Kya hada da wannan ahi ba karatun ba, shi ba aiki ko wata katamammiyar sana’a ba? Idan Kuma kina ganin banyi magana Kan auren su Hamisu ba na Hayatu shima na hana shi ai amma shima don rashin sanin ciwon Kai matar shekararta biyu ya sake auro wata, gasu nan banda tashin hankali me suke yi?”

Ta juyo a fusace “Ka rufa min bakinka kaji, ai fa tunda ba Kai ya shafa ba yanzun zaka rinka kawo min kabli da ba’di, to shima da ya auri mata biyun ai ance matar mutum kabarinsa da yaje yana neman na banza a waje ai gara ya tara cikin gidansa. Kai wai ya za ayi daman ra’ayin rikau dinka ya zama irin na kowa? Naji ta bakinka, tashi jeka, kaga kyaun sana’ar da kake mita, ni zan tsaya, Allah kuma zai taimakemu ayi wannan auren da yardar Allah autana ba zai kunyata ba, idan ba zaka jagoranci harkar auren ba ai ba Kai kadai bane, kaninka na Nan, Allah dai na gani na baka hakkinka na kasancewa babba.”

Da ya tabbatar da al’amarin yai nisa gashi bai son bacin ranta ko kadan har dai in ya tuna can inda aka fito da can dole ya fara lallashi yana bata hakuri yace “Tunda abin ya zama haka ba komi Hajiya, daman ni naso ace ya kara sanin ciwon kansa ne yasan wahalar ya nemi na sa yadda idan yai auren zai fi rike matar da daraja da mutunci amma tunda an matsa insha Allahu ba damuwa za ayi yadda kika ce cikin yardar Allah. Zan nemi Hayatu mu tafi gidan iyayen yarinyar cikin satin nan in yaso duk yadda muka yi dasu Kya ji, anjima ki turo min Rabi’un yai min bayanin unguwar, Allah yasa mana hannu.”

  Dadi ya rufeta cikin murna tace "Insha Allah yau dinnan zaka ganshi yana dawowa gida zan turo maka shi, Allah yai maka albarka."

“Ameen nagode, idan babu wani abu Ina son komawa asibiti amma shi Rabi’un ya sameni a gida.”
Ya ciro kudi cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta bisa tabarma, ya mike kana yai mata sallama ya fita tana sanya masa albarka.
03/09/2020, 10:52 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
4
Rabi’u yace “Yaya Haseeb, Rahima da iyayenta ‘yan usulin jihar nan ne, gidansu na unguwar rijiyar lemu, muna iya kiranta marainiya don ta rasa mahaifiyata tun lokacin haihuwarta.
Bayan Allah ya amshi ran mahaifiyarta ne kanwar uwar dake shayar da nata jaririyar ‘yar kimanin watanni uku ta dauketa taci gaba da shayar dasu gaba daya.
Kasancewa mahaifinta daman matansa biyu sai abin yazo masa da sauki domin ta samu saukin maraicin diyarsa da aka mutu aka barin masa, ko sa yake ita ce diya kwara daya tilo da mahaifiyarta ta bari su bakwai ne cif wajen mahaifinsu, sunan mahaifiyar nata aka mayar mata don tunawa da marigayiyar.
Sunan mahaifinta Aliyu ana kiransa Ali mai goro, data girma ta isa shiga makaranta saita shiga da suna Rahima Mamman Mai yadi, sunanta marikinta kenan, kowa dai ya san Mamman Mai yadi na Yakasai, tsakanin gidansa dana Hajiya bai wuce loko biyar zuwa shidda ba, bayan wannan Rahima yarinya ce mai hankali da zurfin tunani Ya Haseeb.
Hayatu ya kallesa “To ai ka bari har mu bincika muji wa kunuwanmu tukunna kana mu zartas da hukunci, Kai daman ya za ayi ka Fadi wasu aibunta tunda kana sonta.”
Rabi’u yace “Balle ma bata dasu, yarinya ce mai da’a wace ta samu dimbin kyawawan tarbiyya nagari Kuma nagartacce.”
A nan dole Haseeb yai murmushin da bai shirya ba yace “A nan kan Ina bayan Hayatu Rabi’u, idan har mun bincika mun tabbatar da yarinyar da halayen daka fadi babu shakka kayi sa’ar Mata, idan kuma munji sabanin haka sai dai kayi hakuri. Yanzun sai ku koma gida, idan Allah ya kaimu gobe zanyi abinda ya dace sai kaje kaci gaba da adduar Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Duk yadda muka yi goben za kuji insha Allah.”
Sunyi sallama cikin farin cika da murna.
Kamar yadda ya dauki alkawari, ya binciko dukkan abubuwan da suka dace ya sani ya Kuma ji ta gamsu saboda aure tsakanin Rabi’u da Rahima tabbas ba makawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button