NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ta amsa “Yana zuwa mana ka sani, bai jin dadi ne tun jiya da dare ya kwana zazzabi har yana firgita yana Kiran uwarsa Yana kuka.”

Ya dafa kansa “Ashsha subhanallah, ya taba jikinsa, gaskiya har yanzun da alamun zazzabin ko asibiti za a kaishi?”
Tace “Nima tunanina kenan.”

Ya Kara duba shi Kuma yace “Ba sai yaga likita ba idan yasha magani ma zazzabin zai sauka bari inyi masa addua yanzun.”

Dr Haseeb ya dafa jikinsa ya karanto *BISMILLAHI A’UZU BILLAHIL AZEEM MIN SHARRI KULLI URQIN NAARIN WA MIN SHARRI HARRIN NAAR…
Ya kara dora hannunsa na dama saman goshinsa ya karanto *AS’ALUL LAHAL AZEEM RABEEL ARSHIL AZEEM AN YASHFEEYAKA… Bayan ya gama yace insha Allah zai samu waraka.” Ya mike ya maida shi cikin dakin ya kwantar dashi kana ta dawo ya zauna..
Ta daina abinda yake yi ta fusksnce shi sosai tace “Tun shigowarka nike alla-allah inji ta bakinka ka barni inata ci da kuda, wace shawara ka yanke?”
Ya sunkuyar da Kai tare da yin kakkarfar ajiyar zuciya, to in ba domin uwa, uwa ce ba wa ya isa ya tursasa masa yin abinda baiyi niyya ba? Ya dago Kai a hankali yace “Tunda kin ganin auren alkhairi Kuma kin amince shikenan.”
Ta saki murmushin jin dadi tukunna kafin tace “Fito fili kayi min bayani, shikenan kamar yaya?”

Ya sake jan dogon numfashi “Ina nufin na yarda Zan aureta, sai dai kin tuna ina tsoron ajiye mata biyu domin shakkar rashin yin adalici tsakaninsu bayan haka kina ganin zamu zauna cikin kwanciyar hankali bayan Ni da ita ba son juna muke ba?”

Dariya ce ta kubuce mata tace “Itama Zuwairar da bata zake a kanka ba da tasha wuya, miskillancinka ba boyw yake ba, wannan Kuma batun soyayya bata ko taso ba ya ma rage naku, ko kuso juna ko ki da zaran Allah ya hadaku addua kawai za muci gaba da yi muku.’
Hhmmmm ya Fadi a zucci Hajiya mahaifiyarsa ce yana alfahari da hakan, har bugun gaba yake yana ganin yafi kowa sanin jakinta but akwai so many times da ya kanyi doubting hakan musamman idan ta murde ta rikice ya kan rasa inda zai bullo mata kamar yanzun. To in ma banda abinta ya za ayi mace da namiji suyi zaman aure da ya dace bayan babu so da kauna tsakaninsu? Har gara ace mutum guda na so, in tafiya tayi nisa sai dayan yaja ra’ayin gudan amma wannan halin kaka Ni kayi dane yai kama?, Da shi da ita duk basa so, sai yaya kenan?..

Tayi kamar baya dakin ta jawo tarkaccenta zata fara kulle-kullen ta, yasan hali muddin bai sake magana ba ta kare nata zancen kenan don haka yai saurin tambayarta”Yanzun me zanyi abin nufi wane mataki za a dauka nan gaba?”.
Taci gaba da hidimarta
“To ni Kuma zaka tambaya kana namiji kace baka san yadda ake neman aure ba, Kai don Allah baka ji kunya ba, lokacin da kaje samartakat auren farin nina koya maka yadda zaka yi?”

Ya dafe Kai!Oh oh ya shiga uku, ya lura so take ta tursasa shi, ya daure yace “Hajiya wancan da wannan ba daya bane, kin manta inada matsayi a gidansu Zuwaira tun fil azal bayan kaunar dake tsakaninmu?”

To nan dinma sai ka gwada gidansu Rahimar ka gani su ma wanne matsayin zasu baka idan itama kana neman samun gurbi a zuciyarta kasan hanyoyin da suka dace ka bi, Allah yass a dace.’

Yadda ta hakikice tana maida mishi martani yasa shi dariya da sha’awa yace “,Idan naje anjima da laasar na ganta banyi laifi ba ko?”

“Wane Kuma irin laifi ai sai fatan Allah ya kulla alkhairi, kaje ka gabatar da kanka matsayin mijin dana ce nayi Mata Kuma tayi alkawarin ta amince, idan zaka tafi ka biyo ka tafi da takwaranka yaga uwarsa don da biyu taki zuwa gidannan, Nima naki aikawa dashine saboda jiran wannan ranar, sai kaje Ina saurarenki, Ina gaishets da kyau.”..
Ya fita Yana murmushi itama haka.

Ranar a gida Maryam ta yini, Rahima na dawowa makaranta kenan direba na ajiyesu, Walida tasa kuka bata ga Abdul abokin kirinyyarta ba, Saida aka tula mata kayan wasansa tayi shiru.

Su kuma iyayen nata hidimar dora sanwar abincin rana saboda Umman tasu ta tafi Gumel dubo mahaifinsu da bai ji dadi ba, amma tana gab da dawowa, hatta yaran gidan kanninsu basa gida.

Bayan sunci sun koshi sunyi sallar laasar Rahima ta shiga wanka ta fito ta sake dauro wata alwalar kana ta shigo daki ta shirya tsaf Kai kace shirin zuwa buki take.
Maryam ta kalleta “Sarkun kwalliya kina burgeni wallahi karki so kiji yadda Nike sha’awar kirar jikinki ‘yar caraf dake, wa zai ce wannan dafaffen cikin ya dauki da kin haihu.””

Rahima ta kanne mata ido guda “Aunty Maryam sarkin mita, ke din ai kike jawowa kanki katon ciki, inda halitta da rashin kulawa, irin naman da kike dankara lafiya ne, ki ci kowanne irin nama, kisha kayan Zaki, kefa duk inda kayan dake Kara kitse suke kina Nan ya ba zaki ajiye teba ba, gaki Nan haihuwa daya kin zama wata guzuma, idan kin Kara sai Alh Abbas ya auro daidai misali don har Hjy Suwaiba barakallsh Masha Allah.”

Ta wurgeta da maficin dake hannunta “Shima din ba kiga yadda ya koma ba har tozon wuya ya fara fa.”
Rahima tace “Hhmmmm da Rabiu na nan da ya kusan kibar Alhajinku, dubi yadda ya koma kafin rasuwarsa.”
Maryam ta shareta, ta sake maimaitawa, a nan ta kalleta tace “Saboda Allah Rahima ba zaki bar wannan bawan Allah ya kwanta makwancinsa lafiya ba, ke kenan da duk aka tada magana sai kin sako zancensa, Ina amfanin haka, adduarmu kadai yake bukata.”..
Ta nisa tareda dafe kanta “Nima bana sanin time din da nike ambatonsa Maryam, Ina kokarin dainawa.”
. “Ah to gara ki yiwa tufka hanci don ba namijin da zai dauki Yana aurenki kina zancen wani wanda ya rigamu gidan gaskiya.”

“Nace miki zan bari, da kike fadin hakan ai mijin fari wuyan mantuwa gareshi, balle ma kowa na aura dole yai hakuri dani.”

Ta kalleta a shagube “Sai dai kuwa idan bai sonku, muddin Yana kaunarki zaku rinka Kai ruwa rana ne, Wai ma ba haka ba ya batun Dakta?”

Rahima ta canza nan take “Ki bar batun nan don Allah, ai don in nunawa Hajiyar ba Mai yuwwa bane in har hakan take nufi naki komawa gidanta, har Abdul na bar musu in dominsa suke son aikata abin kunya, ko hausawa sunce ana barin halas….

Maryam ta harareta ” Jiya dominki nayi tambaya a islamiyya kan shirmen da kike yi Kuma in fada miki don kin auri Dakta ba abinda ya kaucewa shariar musulumci bane, Malam yace addininmu nai hana wa ya auri matan kani na idan Allah yai masa rasuwa hakan shuma kani na iya auren matsn Wan sa in haka ta kasance.. Har da misalin cewan ko suna da rai ce dayansu ya kamu da rashun lafiyar da ya hana yin sunna da matarsa an nemi magani an rasa na tsawon shekarun da aka gindaya masa zai sahale mata gashi ya yaba hankalinta bai son tabar gidan don kyakkyawar dabi’,unta Yana iya yiwa danuwansa maganar cewan iin ya saki shu ya aureta idan sun daidaita tsakaninsu, Kuma auren ya halasta, ke dinma banga abun tada jijiyoyin wuya bayan da bakinki kika fada min kina son Daktan .

Ta kauda Kai “Na dai so mutumin da aka bani labarinsa, da lamarin ya juye Kuma na sanu canjun ra’ayi.

Ta wani kalleta ‘Karki kawi mun burgar banza, karyarki wallahi, was yace Miki ana yiwa soyayya yankan kauna, yadda mashin son wancan ya soki kirjinki haka na Daktan zai huda zuciyark tunda batun mutum guda ake in dai dama ba karya kike ba Wanda a sanina ba a karyar so da kauna.”

Da taji alamun ta kamo hanya zata kureta saita canza hirar cikin dabara….

Suna cikin hirar suka ji yar karamar muryar Abdul ya shigo a guje Yana fadin 'Mami Kinga jirgina baba ya saya min."

Murnan ganinsa ya rufeta, ta daukeshi tana sumbatarsa “Oyo-oyo Abdul Ina Hajiya?.
Hankalin yaron ma wajen Walida, ganin hakan ta sauke shi, Walidan ta fara kukan sai ya bata jirginsa. Rahima tace Baba ya hada rigima kenan dole gobe inje in sayo miki naki jirgin”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button