NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Wani yaro Dan makwabtansu ne ya shigo Yana sallama suka amsa “Wai ance ana Kiran maman Abdul a waje.”…
Rahima ta kakki Maryam kinji Kuma Bala da gulma shi daya saba shigowa har cikin gida a gaisa “.
Maryam tace “May be sauri yake, fita kiji in zai koma da Abdul dinne tunda ban gansa da kayansa ba.”

Maimakon ta tsaya saka hijab, katon gyalen Maryam ta dauka ta yafa ta fita cikin sauri.
08/09/2020, 13:42 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by jami

19
Tun daga kan soron farko kamshin turaren ‘fame’ ya fara dukan hancinta, zuciyarta ta fara bugawa cikin sauri, ba dai zarginta zai zan gaskiya ba?
Ta karisa cikin tsakiyar soron gidansu inda tayi arba da HASEEB in person, rawar da jikinta ya fara, bai hanata saurin durkusawa cikin ladabi tace “Barka da yini, ya su Aunty Zuwaira?”
Ko kallon arziki bata samu daga gareshi ba
Ya amsa a takaice “Lafiya.” Ya shiru
Ta dan jima tsugunne tana jiran taji da wacce ya taho tunda bai taba zuwa gidansu ba.
Da ya tuna bai da wata mafita dole ya fadi dalilin zuwansa kamar yadda yaiwa Mahaifiyarsa alkawari,ya cije, cikin isa da miskillancisa ya tambayeta “Magana ta kawo ni ko zan sami damar Fadi?”

Kamar ta amsa cewan bata da lokacin saurarensa, saita tuna kaninsa,da irin girmansa da yake gani kamar uba ba wa ba, ta tuna dawainiyar da yake dasu, hakan yasa ta hadiye zuciyarta tace “Ba damuwa Ina saurarenka.”

Ya gyara tsayiwarsa sosai ya jingine da bango tareda goya hannayensa a kirji yace “Hajiya tace tayi miki bayanin komi don haka ba zan tsaya wani dogon bayani ba tunda kin amince da shirinta nima hakan akan dole yanzun ya rage naki kiyi shawarar yaushe kike ganin ya dace a daura auren?”

Gabanta ya buga rugugu, aure? Haka ake zancen auren cikin isa da kasaitar mulki, aiki jawur, tun kafin tafiya tai nisa bata iya cewa ta fasa, daman ta amsa ne saboda bata san shine ba, wata zuciyar kuma tace zaki zan mai karya alkawari kenan wanda a addinance hakan ya zama munafuci, can ta nisa, tace “Bani da yancin kaina koda nike bazawara, iyayena keda hakkin wannan sai abinda kika ce.”

Shi kansa yasan nai kyauta, bai dace ya furta mata wadannan kalaman ba, ba ita ta Kar zomon ba, yaja numfashi yace “Okay zan jira su zartas da shawarwarinsu, nawa iyayen zasu taho in Sha Allah.”

Da yaji ba zata kara cewa komi ba,sai ya Kara gyara murya yace “Abdul kuwa bai ji dadi ba amma naga ya warware, dazun jikin yafi masa zafi.”

Tana dai tsugunne kanta sunkuye har zuwa lokacin, maganar da yake yi bai sa ta dago ba balle tayi responding.

Ya kada Kai "Ni zan koma, na wani problem ko?'

Ta girgiza Kai.
“Ina Abdul, in koma dashi ko a bar shi?”
sai a nan ta amsa “A tafi dashi, sai an jima a gaida Hajiya Aunty da Zuwaira.”

Tana gama magana ta yunkura ta mike ta shige cikin gida ta barshi nan a tsaye.
Tana shiga ta cewa Maryam “Don Allah dauki Abdul ki mika sa waje zasu koma gidane.”
Ta kalleta taga fuskar nan tata a daure bata tsaya tambaya ba ta rike hannun yaron suka nufi kofar gidan. Ko da wasa ba tayi zaton shi zata gani ba amma ta danne mamakinta ta gaisheshi, Abdul ya ruga wajensa ya kama hannunsa suka shiga mota suka wuce.

Har tana tuntube wajen saurin komawa cikin gida inda ta isko Rahima ta cika tayi dam, ta kalleta ta tuntsure da dariya tace “Yau Allah ya hadani da famous Dr Abdul-Haseeb Junaid din da ake magana, he’s very handsome, ashe ganinsa a zahiri yafi ganinsa a tv.”
Rahima ta cafe “May be ganun baiwar kyaun da Allah yai masa da kirar jiki msi kyau ne yasa yake wani ji da kansa.”
Maryam tace “Ke fa na lura ba zaki kwantar da hankali ki fahimcesa ba, to komin ji da kansa dai gashi ya taho har gida, ya kuka yi?”

Ta tabe baki "Maganar ma da kyar yake har Yana m fada min shi dole ne ya amince da batun auren Wai Kuma yaushe nike son a daura? Ke kinji wani galari, wallahi ba domin ina ganin mutuncinsu ba da yaji magana daga bakina, darajar Rabiu kawai yaci, ko an fada masa nima da son raina za ayi oho."

Maryam ta tausayawa ‘yaruwarta tace ‘Gaskiya al’amarin da rikitarwa Rahima amma kiyi hakuri ki rungumi kaddara,Allah da ya shirya faruwan haka daku yasan dalilinsa, mu ‘yan tayaku addua ne, ki daure karki dorawa Dakta laifi, shima na tabbatar abin na damunsa dole yaji a jikinsa.”
Ta share hawayen da suka gangaro tace “Ya zanyi hakuri ya zama dole but babban bakin cikina reaction din daya nuna min, koni na nemi auren nan iyakar cin fuskar da zai min kenan.”

Maryam tace “Ni kuwa ban dauka wulakanci bane, kisa kanki a position dinsa ki kwatanta ya za kiji…

“Maganar ta wuce Maryam, I’ve already made up my mind and there is no going back, so zsn daure ko me zasu taso, hhmmm Allah dai yaji Kan Rabiu.”

Maryam ta mike tsaye “Zaki fara ba, to ba dani ba, naga alamun su Umma sai dare zasu iso ko in dan saurara zuwa karfe tara ma tafi gida?”

“Yes idsn ba wani damuwa nasan suna gab da shigiwa insha Allah kinsan Baffa bai son tafiyar dare.”

Takwas saura kwata na dare suka dawo, Baffa yace su tsahirta yayi sallah sannan su gaisa, Umma Kuma ta zauna suna hirar ‘yanuwa da abokan arziki na garin Gumel.

Alh. Mamman ya shigo bayan ta fito daga masallaci ya fadawa Rahima tanada bako a waje, taso taki fita Umma ta fara fada.
Direban Daktan ne jingine da mota yana jiran fitowarta, tana isa ya durkusa ya gaisheta kana ya bude motar ya fiddo wasu manyan ledoji guda biyu ya mika Mata Wai sakon ubangidansa..
Ta karba a sanyaye tace ya jirata kadan, ta koma ciki ta dauko masa tukwici ta kawo masa ya karba da kyar yana godiya.
Ta sake komawa tana shifa dakin ta kwashi ledojin ta diresu gaban Umma “Gashi wai inji baban Abdul “
Kafin Umma tace komi Maryam ta zaburo “Masha Allah, iye ‘yar gidan Daktan ba, bari mu gani Musa albarka.”

Umma ta harareta “Wannan zarbabin na menene?”

Ta kalli Rahima "Kinji Umma tafi son ki bude kyautar da hannunki ko kin ban izni in bude?"

Rahima ta amsa “Idan kin ganin ki wuce dasu na baki banso.”

Tayi wani shewa ta shiga zazzage kayan, ledan farko tarkacen cosmetics ne, na biyun atamfar super ce biyu, Holland biyu hade da lallausar hadaddiyar shadda.
Ta kyalkyace da dariya “Ashe ni ras, bari inga wace zan fara dinkawa, ta bude turmi guda wani envelop ya fado mai dauke da rafar kudi Wanda aka rubuta kudin dinki a bayan envelop din..
Sakonsa ya daure mata Kai, shi da ya taho Yana shan kamshi yana fadin an tursasa masa ne meye na wahalar da Kai, ko kayan ma matsa masan aka yi ya aiko?

Baffa ya shigo dakin a lokacin suka gaidashi da tambayar mutanen Gumel, yace kowa lafiya duk zasu taho daurin auren Rahima da bukin tarewa.”
Ta zumburo baki ta kalli uwar “Yanzun Umma har Kun karas da abinda babu tabbas?”
“Kunji munafuka inji Maryam, mu kam mun tabbatar tunda dazun nan Dakta Haseeb ya taho wajenta Baffa sannan ya aiko da sakon nan ace babu tabbas?”
Umma ta harareta “Wane irin zuga kike mata ne, kina son Baffan yai fada ne ko yaya?”.
Rahima ta saki ajiyar zuciya “Ni nama kosa ta tafi gida hakan nan tunda tazo ta isheni da surutu har ciwon kai ya kamani.”
Iyayen suka kalleta cikin tausayi suka ce “Rabu da wannan babbar gwazar kinji sannu, nemi magani kisha ki kwanta ki huta.”

Maryam tace “Hhmmm bari dai in zo in gudu tunda sauran girmana tunda taron dangine abin.”

Rahima tayi murmushin cin nasara watau ta danawa Maryam bom.
Cikin wasa da dariya suka ci gaba da hira har Alh Abbas yazo dauka matarsa, ya shigo ya gaida surukansa kana ya dauki Walida da tayi barci ya sallamesu ya fita. Rahima ta zubawa ‘yaruwarta kayan shafan hade da turmin super ta mika mata, Umma ta diba Mata tsarabar Gumel sannan suka fita Rahimar na rike da kayan har wajen motarsu ta bude ta aje mata su a baya.
Alh Abbas ya leko da kansa ya fara tsokanarta “Ni fa naji kamshin amarci.”.
Tace “Amarya za kayi ba labari?”.
Yace “Amaryar dai tadan kanta.”
Maryam tace “Rabu da ita Alhaji Wai Kai zata yiwa siyasa, bari mu isa gida kaga kayan da angon ya fara kawo toshi ka gani.”
Yace “Ki bari don Allah?”.
Ta amsa “Zancen kake so kenan.” Ta juya wajen Rahima ‘yaruwa kije ki kwanta karki wani wahalar da kanki shan kwayoyi kinsan dalilin ciwon kanki ba ruwana da akai min kazafi.”
Alh Abbas yace “In don ciwon kaine meye na raki kinada likita a hannu, hala bai San amaryar bata jin dadi bane?”
Da taga sharrin nasu zaiyi yawa ta juya fuu tace “Mu kwana lafiya, sarakan sharri.”
Yaja motar Yana dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button