
A dakinsu sun dade itada Umma suna hira, tun tana kaucewa har ta gaji ta kalli Rahimar maganar na cin ranta tace “Ashe yau likita ya zo.”
. Ta amsa a ciki “Eh ya taho Umma ko da yace dolene a garesa, wallahi Raina ya baci kwarai da furucinsa tunda nima ba son nike yi ba, Zan fi farin ciki idan Allah zai hadani da wani daidai Ni.” Ta share hawaye
Umma ta matsa kusa da ita ta kama hannayenta ta rike “Haba Rahima bai dace kin rika gaba kina dawowa baya ba, mun riga mun gama magana kince min kin amince yanzun ya kike son sakawa zuciyarki damuwa da bacin rai a banza? Ko wane hali ya nuna ai ya zan shiririta tunda gashi ya biyoki har gida ya baki mutuncinki na diya mace Kuma ki tuna ba fa mu iyayenki muka nema masa ke ba, daga can wajensu batun ya taso don haka bai isa ya wulakanta mana ke ba, kina da damar bugun gaba diyar Umma don haka share hawayenki kinji, muna nan muna adduar idan babu alkhairi a cikin al’amarin nan Ubangiji ya musanya miki da mafiyinsa.”
A nan ta danji dadi tace “Allahumma Amin Ummana, nagode.”
08/09/2020, 23:11 – Anty saliha…..ˆRAHIMA…doc by jami
20
Dr Haseeb ya dade tsaye cikin office dinsa yana jangen motocin dake kara kaina ta windon amma kallon kawai yake tunanisa ya kasu. Na farko yana tunanin rabonsa da gidansu Rahima kwanaki uku kenan kacal amma zuciyarsa na kwadaita masa sake komawa ya ganta don wanke laifin kalaman da ya fada mata wadanda basu dace ba.
A hakikanin gaskiya ya yaba da hankalinta, amma addinin data rike hannu biyu ya fara burgesa. Tunaninsa na biyu ya danganci matarsa Zuwaira, wajibi ya bata hakkinta ya fada mata halinda ake ciki na Shirin auren matar kaninsa, kana ya zama dole yaje ya nemi shawarwarin da suka dace wajen abokin mahaifinsa shahararren malami don Kara tabbatar da alkhairin auren, sai ziyartar surukinsa mahaifin Zuwaira saboda kar yaji daga sama ya dauka zaiyi auren ne don yaci amanar diyarsa.”
Bai san abinda yasa duk cikin wadannan tunanin zuciyarsa tafi karkata da son zuwa gidansu Rahimar gashi bai San dalilin da yasa da duk ya tuna yai mata alkhairi ya kanji wani irin farin ciki ya lullubesa ba.
Itama Hajiyarsu taji dadi, tunda hakane kenan kafin ya sake komawa shiga boutique ya gansa….
Ya nutsa har baiji bude kofa da shigowar abokin aikinsa Dr Kabir office dinsa ba saida ya iso daf da teburinsa waya Kuma tayi ringing, kana ya dawo hayyacinsa yasa hannu ya daga wayar dake bisa tebur ya fara magana da harshen turanci kafin ya juya harshe zuwa larabci, sin dau lokaci suna magana da Wanda ke wancan bangaren kafin suyi sallama
Ransa a bace ya kalli Dr Kabir yace “Dr Taariq ne daga Riyadh Wai suna neman taimakonmu by nextwk sabida suna da patient da patient da yake cikin coma suna tunanin zai sami amnesia idan ya farfado .
Dr Kabir ya dan sosa keys “To ai wannan aikin kane Dakta.”
Dr Haseeb ya zauna ya jawo wani file yayi rubutu ya mayar ya rufe ya ajiye gefe sannan yace “Gaskiya I have commitments next week, so I think they’ve to do without me this time.”.
Dr Kabir ya zauna shima yace ” Kana ganin in an kyalesu an kyauta kenan? They relied on your services ka sani.”.
Ya dago Kai ya kalli Dr Kabir yace “Nasan haka Dakta amma inada wani uzurine next week din, Ina sa ran a daura min aure by then kaga kuwa da wuya in sami yin abinda suke so.”
Dr Kabir ya bude baki cike da mamakin da al’ajibi don ko kusa bai taba tunanin Daraktan nasu zai Kara auren ba…
Yayi murmushi ya daga masa hannu “Don’t be surprise, kasan shi aure nufin Allah ne, sai kaga Wanda ya shafa ma bai taba mafarkin faruwansa but idan Allah ya rubuto mutum baida wani dabara “
Ya gyada Kai “Kwarai da gaske, may I then offer my congrts Sir?” Cewan Dr Kabir.
Ya sake daga masa hannu “Thanks a lot, by the way mahaifiyar yaron nan Abdul da ka sani amaryar.”
Yaga ya fadada murmushinsa sabanin yadda ya zata, ya Kuma Kara da fadin “Wallahi kayi abinda ya kamata, Allah ya sanya alkhairi “
Dr Haseeb yai ajiyar zuciya “Nagode sosai Dakta, I really appreciate your support and prayers.”
Yace “Haba ba komi, Ni zan shiga office, batun tafiyar a bari a ga abinda haki zai yi ko?”
Ya amsa “Gaskiya sai yadda na gani still a shigar da tafiyar cikin schedule dinmu mu gani.”.
Yace “Ba damuwa Dakta.”
Ya fita ya bishi da kallo, yasan yanzun batun auren nasa zai karade cikin asibitin.
Yau kwanakinta takwas kenan da dawowarta Umrah amma basu yi zaman ko rabin awa ba tareda mijinta, ita wannan hali na Dakta na daure mata kai kuma ta fara gajiya don haka ta kashe ta tsare dole yau ta saurateta su tattauna problems dinsu, idan Kuma yaga bai auren ya gaji ne y sauwake mata taje ta nemi wansa zai san darajarta ya rinka kulata, amma Ina amfanin zaman aure irin nasu? Duk da tasan yawanci laifinta ne, zuciyarta taki amincewa, to yaushe zata yarda ta dorawa kanta laifi haka siddan.
Ko da ya dawo gidansa bai taba tunanin zai sameta a gida ba tunda Allah yayi ta mai yawon tsiyace.
Doguwar riga ce a jikinta Wanda duk da ta rufe tun daga hannayenta zuwa kafafu shara-sharar yadi ne marar kauri dake nuna duk ilahirin surar jikinta, kallo daya yai Mata ya kauda Kai, ta amshi briefcase dake hannunsa tare da rungumarsa “Sannu, ka dawo da wuri lafiya?”
“Lafiya.” Ya amsa mata yana tafiya zuwa bedroom dinsu domin yai wanka.”
Zuwaira ta hada kayan abinsa a bisa carpet saboda bai cin abinci bisa dining table, ya fito sanye da kananan kaya a jikinsa Yana zuba kamshi, ya zauna kafin ya fara cin abinci ya tambayeta “Ina su Khalifa?”
Ta amsa “Suna can gida.”
Ba Kara ce komi ba, ya karbi plate din data shakare da shinkafa da miyar data dafa, yayi bismillah ya saka cokali daya a baki ya tauna ya hadiye da kyar, yaja tsaki ya aje plate din yace “Sabida Allah Zuwaira a matsayinki ta mace baki iya sarrafa wani nau’in abinci bane sai shinkafa da miya kullum, ta yau ma bata nuna ba, miya ga tsami sai kace ba mace ba?”
Ta harzuka nan take “Yauwa daman maradinka bai kunya ai, kai kenan babu ranar da zan dafa abinci kaci lakadan ba tareda complain irin na sauran maza ba, ni kenan komi ban iya ba a idanunka.”
“Ni bance ba ki iya komi ba, ina fada miki ki rinka kwantar da hankalinki kina abinda ya kamata cikin gidanki, ai ga abincin nan dauki kici kiji Mana idan zuwa anjima indigestion bai kamaki da heart burn basu dameki ba…
Tayi shewa “To idan kwarnafin ya taso ba sai ka bani magani ba? Kaga idan ba zaka ci ba kace da inda kake zuwa kana ci ka koshi, to da hakan kuwa gara ka aurota zaifi min nono fari.”
Ya shareta bai ce komi ba, ya dau remote ta canza channel zuwa CNN yaci gaba da sauraren news.
Ta mike ta kwashe tarkaccenta ta mayar kicin ta dawi ta zauna, zuwa can tace “Ina son magana da Kai.”
Yace “Hhmmm Ina saurarenki bismillah.”.
Ta kura masa ifo na wasu dakikoki tukunna, ta gyara zama tace “Tambayarka zanyi, saboda Allah irin zaman da muke yi ya dace da tsarin rayuwarmu, kana ganin shine daidai?”.
Bai dagi ba ya kalleta ba ya amsa “Wane irin zama kike nufi?”
Taji haushin amsar da ya bata tace “Ai baka ma sani ba ko? To in fada maka, Zama ne muke yi tamkar ba ma’aurata ba, kowannanmu na harkarsa, ba shakuwa, baka San halinda nike ciki ba, nima ban san halinda kake ciki ba, in har ya zama dole muyi magana bata kaiwa ko Ina m gayyar take watsewa, ko yaranmu baka ja su a jiki ba, Ina iya cewa ma yadda ka shaku da wannan yaron Abdul baka shaku da ‘ya’yan cikinka ba, basu Sami wannan gatan ba.”