NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Yaji tayi shiru, ya aje remote ya fusknceta ” kin gama?”
“Eh ta amsa.
Yace “Tunda Allah yasa yau da kanki kie son ayi batun sai ince alhamdulillah do n many times nayi yunkurin mu zauna mu tattauna issues dunmu kika ki yarda kika nuna abinda ke faruwa duk laifinane, Amma tunda kin yarda akwai problems a zamantakewar mu sai ki fadi muji a Ina na kuskureki?

Zuwaira tace “Baka ji abubuwan dana lissafo bane?”
Yace “Oh sune kike ganin problems dinmu kadai? To bari ni in bayyana miki ko ince in baki amsa ki hujjojina na sanya miki ido da nayi.
Na farko duk matar arziki tana nunawa matukar kulawa da harkokin maigidanta na yau da kullum, har idan akwai shawarwarin da zasu amfaneshi ta bashi , idan gari ya waye ta kula da dawainiyar breakfast dinsa Dana yaranta in akwaisu, idan zai fita aiki tayi masa adduar fatar alkhairi, su rabu cikin farin ciki su yini begen juna, idan ya dawo ya sameta cikin suturar mutunci, ta tarbesa da da abinci masu gamsarwa, idan lokacin barcinsu yayi suyi hirarsu Mai sanyayar da zukatansu har in suna cikin mood su kusanci juna ta hanyar da Allah yai mana umurni Kuma Manzon Allah yai mana koyi a addinance sabida hakan zai haifar musu da nishadi da Kara musu shakuwa ba a kwana ana jin haushin juna ba.
To ke kuwa duk safiya na Kan tashi ne in barki kina barci baki sa niyyar tashi ba ma saboda kinada rauni a addinin naki, batun hidimata dana Yara kuwa kin halastawa mai aikinki tayi Mana, lokacin da na dawo gida ba lale in sameki ba, kin dau mota kina garari a gari, ba Kya gidan wannan buki ba Kya gidan wancan abokiyar kasuwanci.

Idan anci saa kin zauna a gidan, Zan shigo in taras dake da kawayenki ne yan duniya, wadanda suka fi karfin mazajensu iskar duniya na dibansu.

Abincin da kikan girls so da yawa nakan gwammace zuwa ci a hotel da inci naki sabida baki zauna kin kula yadda mutum zaici hankali kwance ba, ke kanki ba Kya cin abinda kika dafa a tukunyarki kin gwammace kullum ki aika a sayo miki nama ki ci.

Batun rashin kusantar yara da kike kin basu damar zama cikin gidansu ne? Ko kuwa kin kaisu wajen mahaifiyata tace na zata iya ba? Nasan gidanku kike kaisu but mun san zama gidan ubansu yafu musu fa’ida.

A nan ta hayyayako “Ai da tuntuni ka nuna rashin amincewarka dana rinka barin maka yaranka muga tsiyar da zaka basu a gidan..
Yayi wanumi dan murmushi “Duk takamarki kudi ko? Gidanku ba matalauta bane, to Ni dinma ba matsiyaci bane.
Yanayin aikina yasa na amince miki Kan ki rinka kaisu gidanku din sabida da kina zama a gida da yaran basu rinka watangaririya ba.
09/09/2020, 14:13 – Anty saliha: …RAHIMA…doc by jami
21

Dr Haseeb yaci gaba da fadin "Shin kin taba tunanin kai yaran nan wajen Mahaifiyata su rinka debe mata kewa? Ah ah ke sam babu ruwanki da harkar dangina sai wadanda suka zama miki dole, yau satinki nasa rabonki da gidan Hajiyar? 'yanuwana sunyi korafin kin kama 'ya'ya kin rike basu san kowa ba sai danginku, sun gaji da complain sun hakura.

Kina korafin bamu shaku da juna ba ko? Ta yaya hakan zai kasance bayan kin nunawa duniya mutanen da kike hulda dasu a waje sun fini mutunci da matsayi a zuciyarki, ya za kiyi tsammanin ni Haseeb in zama second best a rayuwarki?
To bari ayita ta kare yau Zuwaira, shin kinsan nasan fa duk shigi da ficin da irin mu’amalar da kuke yi da wasu mazan da sunan kasuwanci in and outside Nigeria? That’s why naja baya dake, na sakawa sarautar Allah ido, duk ranar da Allah ya kawo karshen aurenmu shikenan don na gaji da zama da wace zuciyata ke mata zargin fasikanci.”

Tana jin yai shiru ta tuma gefe ya dafe kirji tareda zaro idanu “Kazafi Kuma za kayi min Haseeb?”

Ya girgiza Kai “Kinji Kuma daya daga cikin halayenki dana tsana karya duk maganar da zaki Fadi aka yi nazari aka tace sai an gano karyarki tafi gaskiyarki yawa a cikinta, kinga bani ba har Allah daya haliccemu ya la’anci mai yinta, yai hani da yinta, kince Kuma kazafi wane irin kazafi ga dahir nan kowa na gani?
Ba ma sai an kaita da nisa ba, fara tuhumar kanki tun daga Kan irin shigar da kike yi, yadda kike gudanar da tsarin rayuwarki, na mijinki da zuriyyarmu, yaya tarbiyyarki ke tafiya, shin kina kokarin tsare abubuwan da Allah ya umurceki kiyi, kina gujewa abubuwan da suke munkar a gareki?
Look at you now, just look at irin shigar da kika yi a matsayinki ta musulma, fara da gashin kanki, gaki nan roba ce ko yizgar doki ko wace tsiya ce kika Kara a kanki oho wai ke gayu, gayu ko yin biris da hanin addininki, ke kin isa kiba kanki abinda mahaliccinki bai azurtaki dashi ba?
Dubi tun daga yatsun kafarki zuwa hannu, yanke kumba bai cikin tsarinki abinda Manzon tsira yai mana koyi da yanketa duk ranar jumma’a don inganta tsabtar jikinmu da samun lada saboda ita din najasa ce, wani lokaci har fenti kike musu wai duk cikin gayu tunda ibadar bata tsaya miki bane, bki ma san hukuncin barin lam’a wajen al”wala ba, kalli suturar dake jikinki, gata nan har Kara amma bata kare a hango yanayin surar jikinki ba….

“Karfa kaga laifina a nan, wallahi kai nikewa kwalliya saboda idan banyi ba ka isheni da korafi.’

Ya kalleta wani iri “In don nine kike sabon Allah irin haka na yafe. Duk matar data san mutuncin kanta ba zata rinka irin shigar da kike yi ba, idan Kuma domina kike, ai ko Ina kasar ko ba nan hakan kike shigarki, haka kike fita duk inda kuka ga dama keda kawayen naki, mutuncinki a zube, na iyayenki a watse, Ni Kuma duk irin matsayina a garin nan wasu na min kallon namijin hotiho wace matarsa tafu karfinsa, to ba fun karfina kika yi ba, Allah ne shaidata tunda naga kin fara canza salon rayuwarki na fara yi miki nasiha, baki ddauka ba, na gaji na hadaki da iyayenki duk a wofi,maimakon ki canza sai kika Kara fekewa, Kika ce wai Ina neman hadaki dasu ne, to sai na gaji na sanya miki ido kije duniya taci gaba da rudinki, shaidan yaita busa miki sarewa kina taka rawa, abinda na sani gida biyune, da inda zamu tafi komin dadewarmu a duniyar, yau Ina Rabiu, kina ganin lokaci kalilan Allah ya rabamu farad daya, kafin shi mutane miliyan nawa suka rigamu gidan gaskiya, mu din ma ba zama za muyi ba, tun muna jin na wasu wata rana za aji namu, ke don Allah ko tunanin mutuwa ba kya yi?
A kance wanda duk yai nisa bai jin Kira, Zuwaira ta fara nisa, tafiyar ta tafi sai nema mata shiriyar Ubangiji saboda rabi -da rabi take saurarensa, hankalinta ya dauku da tunanin irin cakewar da zata yi wajen bukin wata kawarsu da za ayi a Hotoro, Kuma a kullum ta kanso tayi shiga ta burgewa da tsadaddun kaya don ta nunawa duniya ita ‘yar business ne, matar shahararren likitan da ake damawa dashi a kasarmu Dr Haseeb Junaid.

Ya lura hankalinta bai tare dashi, ya kakkabe rigarsa ya tashi ya dauko key din motarsa yai bar mata gidan

Bai zame ko’ina ba sai gidansu Zuwaira ya wuce Kai tsaye cikin gidan y gaida matan gidan su uku, sarakuwarsa ce Uwargida sai masu bi Mata. Dr Haseeb ya koma falon surikin nasa ya zauna Yana jiran fitowarsa, nan ya tsudumma tunani, kwakwalwar sa ta tariyo masa tarihin rayuwarsa tun yana karami da dalilin haduwarsu da Alh. Muhammad..

Shi dai an haifesa a unguwar Galadanci, mahaifinsa Mal Junaid rikakken dan boko ne daya kware a fannin kimiyya, malamine a jami’ar Bayero. Ya mallaki mata daya Kaltume da albarka da guda daya tilo, sun day dogon lokaci basu Kara samun haihuwa ba a dalilin haka Mal ya nemi auren wata bazawara Kuma daliibansa ya aure. Tun tarewan amaryar ta nuna ita babu ruwanta da Uwargidanta balle wani danta daya tsone Mata ido. Yaron ya zama wajen uwarsa kadai yake samun sararawa wace ganin halin ko in kula da uban ke nunawa danta bayan ya Kara auren yasa ta ajiye kunya ta rungumi abinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button