NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Yana kara shekaru yana fahimtar yadda mahaifinsa ke yin nesa dashi Wanda da ya dauka kunya ce irin wanda iyaye kanji na dan fari but daga baya ya gane wata irin kiyayyace da bai San mafarinsa ba

Abinda ban mamaki ace farad daya uban daya haifeka ya dawo bai kaunarka, duk da haka daga Kaltume har Dan basu danganta hakan da komi ba.

Amaryar malam ta fara haihuwar diya mace ta rasu, tun daga lokacin Abdul Haseeb ya fara karaya da lamarin mahaifinsa domin rashin jaririyar nan da akayi tamkar zautu yayi, bayan nan Allah ya bata haihuwar diya biyar, mata biyu, maza uku, Allah ya sake amsar matan ya bar Mata mazan.

Duk da ya kasance shine babba, a kullum mafarkin mahaifinsu ya ta’allaka Kan kanninsa ne kawai na su din su gajeshi fannin karatu. Ba zai taba mantawa wata rana suna zaune gewaye da uban suna hira,kowa na fadin abinda yake son ya zama idan ya girma, Abdul Haseeb yace shi likita yake shaawar zama maimakon uban yaji dadi ta bashi kwarin gwiwa sai ya hantare sa ya daka masa tsawa yace “tafi can da wace dakusassar kwakwalwar? An fada make batcu ake a tashi a zama likita? Ko da wannan tsamin bakin da in inar taka ce zaka zama likita?
A lokaci bai wuce shekaru goma sha biyu amma yaji zafin gorin da mahaifinsa yai masa, kalamansa sun sa hawaye masu zafi gangaro masa wadanda uban ya lura yace ya tashi ya bashi waje ..
Kaltume ta gansa yana kuka ta tambayi dalili yaki fada Mata don ta fara wayon gudun bacin ranta, sai dai tun daga ranar ta Kara zage damtse ya daukarwa kansa alkawarin zama wani abu a rayuwarsa duk wuya iya wahala, ij karatu nasa mutum yai suna to sai yayi suna gabas da yamma kudu da arewa sai an San da zamansa.
Ya dage da karatu ita Kuma uwa ta dage da neman maganin gyaran tsamin baki da in Ina da ya tashi dasu, duk inda taji magani zata nema ko Saida wani Abu nata ne ta amso ta bashi bayan adduoi da yake karya kummalo dasu,idan zai kwanta barci su din zasu masa bargo. Kullum cikin sanya masa albarka da Kara masa kwarin gwiwar cin ma nasarar abinda yasa a gaba take.
Tsakaninsu da mahaifinsa ba wani canji haka yasa yaja baya dashi da ‘yanuwansa da tun farko ba a nuna musu muhimmancin zumunci da junansu ba balle su kusance sa.”

Yayi kokarin gano dalilin rashin samun kyakkyawar kulawa daga mahaifinsu abu yaci tura a yayinda uwar ke kokarin hanashi kullatar mahaifinsa da komi cikin zuciyarsa tunda itama ta kasa gano komi zaman hakuri take duk da tana zaune dashi fisabilillah

Kwatsam aka wayi gari malam ya saki Kaltume har saki uku, wannan Abu ya tsayawa Haseeb a rai, a nasa wautar yaso uwar ta zauna gidansu komi wahala amma zama ya kare.

Tana gama idda ta sake aure inda Allah ya azurta ta da Yara biyu maza, Hayatu da Rabiu.

Ba a taba tabbatar da hazakarsa ba saida ya shiga jami’a ya samu gurbin karatu kan koyon aikin likitanci.
A nan Abdul Haseeb ke matukar neman taimako da dukkan kwarin gwiwar da ya dace iyaye da duk masu kaunarsa su bashi sai dai ina kana uban yayi alfahari da godewa Allah da ya bashi hazikin yaro amma Ina ! Bai samu ba, gashi uwa duk ta gama sayar da dan abinda ta mallaka a Kan neman ilmin da kwara daya tilo, hatta da yar gonar da tacu gado ta sayar anyi amfani da kudin basu isa ba.
Shi Kuma bai son matsa mata saboda bai da kwanon abinci gidan ubansa, duk wata lalurar ci da sha da sauran abubuwan bukatunsa sun ta’allaqa ne kadai Kan mahaifiyarsa, tausayinta yake har dai da yaga mahainsa ya dara mahaifin su Hayatu karfi sosai, Kuma mahaifinsa na daukar nauyin hidimar sauran ‘yanuuwansa shi kadai yake yiwa wannan yankan kaunar.

Wata rana kudun sayen handout yai masa teahe ya rasa yadda zaiyi dole ya nufi wajen uban neman taimako amma me zai faru, fada ya rufeshi dashi yana fadin “Wa yace kaje ka zabi course Mai sa kashe kudin tsiya kassn ba Kai kadai na haifa ba don haka ba zan talike a kanka ba, ya wurgeshi da rabin kudin yace karya sake zuwa ya dameshi don da yai nasa karatun babu Wanda ya taimaka masa kwadago yayi shima yaje yayi ya nemi nasa.

Ance gayawa Mai zuciya buki ba Mai dukiya ba, wadannan kalamai sun Kara zaburar dashi sunsa masa rai kwarai sun Kuma tunzura shi, ya zuciya, irin zuciyar da ake son yaro yayi ya ajiye girman Kai da tunanin shi wani ne ya tashi ya nemi na kansa. Ya fara yawon neman abinyi idan ya gama lectures ya shiga gari neman aikin, duk inda yaga ana gini ko aikin bulo ya nema ya tube yayi a biyashi, bashi wajen kafintoci bashi tashar mota wajen yun dako. Idan ya samu kudin aikin yinin ranar ya Kan raba uku, Kashi daya ya mikawa uwa, Kashi na bukatun yau da kullum Kashi gudan a jefa a asusu na hidimar karatunsa ne.

Wata rana inda yake aikin bulo suka samu kwangilar ginawa wani dan kwangila sabin gida, a cikin maaikatar da aka dauka har dashi ga jarabawarsu ta matso ga bukatar kudin a tare dashi don haka ya kwashi takardunsa ya rinka tafiya dasu site din inda da ya samu lokacin tsaya sai ya duba tukunna kana yaci gaba da aikinsa.
Lokaci lokaci Alh Muhammad Kan ziyarci site din don ganewa idanunsa yanayin aikin da ake masa, a nan ya hango wannan saurayi inda ta dade yana nazarinsa Yana karatu a natse, sau uku kenan yana ganinsa, haka kawai yaji yana son jin labarin yaron. Yasa aka Kira masa shi, ya kwaso littafansa ya zuba a jaka ya iso inda ake nemansa. Yana zuwa ya durkusa gaida Alhajin amma ya mika masa hannu su gaisa, ya dan tsaya saboda jin nauyi, Alh. Muhammad ya riko hannunsa Yana dariya, ya tambayi sunansa ya fada masa, ya sake tambayar dalilinsa na yawo da littafai Yana aiki ya bashi amsa da “Ina neman na kaina ne.”
Ya sake tambayarsa wanene mahaifinsa ya fada, nan da Nan ya gane don shi din sanannan mutum ne, Alh Muhd yai mamakin jin sunan mahaifinsa da yadda ya bar dansa na kwadigo bayan Allah yai masa rufun asirin da zai taimaki wani ma ba dansa kadai ba.

Yana son jun ainihin tarihin yaron nan don haka ya mika masa katinsa yace ta samesa a gidansa a ranar, ya karba yana mamakinsa dalilin da yasa yake son ganinsa tareda alkawarin zuwa da dare.
Karfe takwas na dareya isa gidan Alh Muhammad, da alamun an bada labarin zuwansa domin yadda maigadi ya tarbesa yai masa jagora har falon maigidan.

 Alh. Ya mike ya sake Mika masa hannu suka gaisa kana ya bashi umurnin ya zauna ya zabi abinda zai ci cikin nau'ikan abincin da aka baza a tsakiyar falon.

Yasha lemu kawai yace ya koshi, Alh ya jima yana kallon yaron da ya shiga zuciyarsa farad daya ki domin baida da namijine ohom.

Yaso yaji dukkan labarinsa but Abdul Haseeb ba haka yake ba, bayan miskillanci yanada rike sirrinsa domin ba ayi ciki don tuwo kadai ba, to ma haka kawai ne daga haduwa da mutum bai San kowanne irine bane zai zayyane masa sirrinsa, no bai san abinda zaije ya komo ba, bai san me mutumin ke nufi dashi ba.

Alh Muhd ya tabbatar da ba zai Kara jin komi daga bakin bakonsa ba ya hakura ba don ya gamsu ba sabida har zuwa lokacin Yana mamakin uban da zai samu hazikin yaro kamilalle irin Haseeb yai biris da al’amarin neman ilminsa, da daure kai sosai amma tunda yaron ya dage kan cewan Yana kwadagon don ya taimaki kansa ne ya kyalesa a haka yai masa taimakon da zai iya yi masa.
09/09/2020, 23:56 – Anty saliha: ..ˆRAHIMA …doc by jami

22

A ranar yaiwa Haseeb albishir din cewan saboda ya yaba dashi matuka gaya zai taimaka masa Kan harkar neman ilminsa tun daga kasarmu zuwa kasashen ketare har ya cimma burinsa. Yace Yana son ya dau masa alkawarin zai amince ya zama dansa saboda shi bai taba haihuwar da namiji ba, ‘ya’yansa takwas duk matane. Bai yi saurin amincewan ba ya nemi ya bashi kwanaki uku yaje yai shawara tukunna, Alh.Muhd ya amince ya kawo kudi ya bashi yace yai kudin mota.
Ya amsa yai godiya ya tafi. A ranar ya sallama gidan mijin mahaifiyarsa Yana kiransa Baffa, ya shaida musu duk abinda ya faru, Kaltume ta tsaya shiru ta rasa ta cewa, maigidanta yace mishi “Kaje ka amshi taimakon nan da hannu biyu ka rikesa da zuciya guda bisa amana tareda adduar Allah ya taimakeka bukatarka ta biya.”
Kaltume ta nisa “Anya? Ina jinjina batun mutumin nan Malam, kana ganin za’a kwashe lafiya, ka fa san halin mutanen zamanin nan na mu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button