
Mal. Sunusi yace “Insha Allah na komi, Ubangiji fa ba yadda bai iya tsara al’amarinsa ba, idan cikin hikima da basirarsa ya kaddaro Alh. Muhammadu ya taimaki yaron nan ba makawa, ai shine kaddarar, zaki ga wani mutumin ba ko a mafarki tunani bai taba kaika cewan zaku hadu ba sai kwatsam Allah ya hadaku a shiga cin gajiyar juna. Kai dai har kullum gargadina gareku shine Wanda duk Allah ya hadaku dasu ku zauna dasu tsakani da Allah da zuciya daya, banda hassada ko kyashi, Banda biyewa zuciya ko mutanen duniya ‘yan Kai kawo su shiga tsakaninku, banda daukar jita-jita.
Ka sani daukaka Allah ke yiwa mutum ba kowa ba, idan ya so ka daukaka iya hassadar makiya basu isa su hana ba, kazalika in baiyi nufu ba ba Wanda ya isa ya kaika inda Allah bai Kai ka ba.
Banda wulakanta mutum da kowacce irin halitta, banda kwadayi don yana janyowa mutum wulakanci da kaskanci, kayi imanin komi ya same ka cikin rayuwarka rubutacce ne daga Allah, wani ko wata, mutum da aljan basu isa suyi maka abinda ba Allah ya rubuto zai faru dakai cikin Lauhul Mahfuz ba.
Ka riki gaskiya duk inda ka tsinci kanka cikin kowanne yanayi, Ina gargadinka daka rike addininka hannu biyu, ko da Allah zai daukaka nan gaba ta azurtaka karka butulce masa son duniya ya shagaltar dakai bauta masa gwargwadon iyawarka…
Ka rike mutumin daya taimakeka da hannu biyu, ko da ace baiyi maka komi ba kaunar daya nuna maka ta isa domin duk Wanda ya kaunaceka irin haka, ba don wani Abu naka ba sai domin Allah ya gama maka komi, karka sake samun duniya ma’ana dukiya ta hadaka dashi, Kar ka zame masa mutum mugun icce.
Da wadannan nasihohi masu mugun shiga jiki Abdul-Haseeb da mahaifiyarsa suka yi na’am da Alh. Muhd.
Shi kuma can ya kosa yaron ya dawo yaji ta bakinsa domin har ya nemi alfarmar gwamna cewan yana da d’a idan mai girma gwamna zai tura hazikan dalibai karatu kasashen waje a saka sunansa.
Gwamna ya amsa da alkawarin idan lokaci yayi nan da watanni uku zai sanar dashi.
Lokacin da Abdul Haseeb ya koma gidan Alh Haseeb kansa ya daure, an nuna masa ya riga ya zama dan gida, kowa sai ji dashi yake kamar daman a gidan yake tafiya yayi ya dawo, hidimomi salamu Alaikum.
Kaltume da maigidanta musamman Abdul Haseeb ya kaisu yi masa godiya shi da iyalinsa.
Kafin watanni ukun Alh Muhd yaja Haseeb a jikinsa sosai ya Kuma bashi labarinsa tas, shima yace ya taso cikin wahala sakamakon iyayensa sun rasu tun Yana karami amma daga dangin uwa har na uba aka rasa Mai daukar nauyin karatunsa, nan ya shiga neman abinda zai hucewa kansa takaici, ya fara da yiwa wani attajiri kiwon doki, ya kanje ya yanko ciyawa ya share turkensa ya kula da dawakin ana biyansa, daga nan ya koma sayar da sigari, da goro, minti ashana da sauran tarkacce a tire a tashar mota, daga nan Allsh ta tarfawa garinsa nono,ya kafa dan tebur daga nan sai shagon kayan masarufi, daga nan Allah ya daga shi sannu-sannu ya fara kwangila tareda taimakon Allah, Ubangiji ya daga har ya Kai matsayin da yake ciki yanzun.
Ya auri mata uku bai Sami haihuwa da wuri ba, da ya samun sai Allah ya azurta shi da diya Mata.
Alkawarin da yayi suna gama sakandire zai aurad dasu, Amma duk ranar da Allah ya bashi d’a namiji sai inda karfinsa ya kare.. Zuwaira ce diyarsa ta biyu, Mai bala’in kama dashi saboda hakane yake sonta kwarai da gaske, irin son da ya janyo mata sangarcewar.
A lokacin da ya hadu da Haseeb duk suna makaranta, Zuwaira na aji uku kacal.
Duk wani takalihunsa ya koma hannun Alh Muhd, duk da haka bai saki jiki ya daina buga-bugan sa ba. A hankali ya fara koyon hanyoyin kasuwanci ya rinka aiwatar da abinda ya saukaka a garesa.
Yayin da gwamnatin jihar Kanota dauki nauyin fitarsu zuwa kasar Neatherlands domin zama kwararren likita.
Abdul Haseeb ya zama Neurologist ya zamewa uwa da uba dashi kansa Alh Muhd din d’a daya tamkar goma, ya cika dan halas domin matukar girmamawar da yake masa yasa koda yai masa tayin auren diyarsa Zuwaira bai musa ba duk da Yana ji da ganin irin gurbatacciyar tarbiyyarta.
Wajen hidimar auren Alhajin yaso daukar nauyin hidimar komi, Abdul Haseeb yaki yarda yace hakkinsa ne ya dau nauyin iyalinsa.
Tunda Allah ya azurta shi yake dawainiyya da iyaye, ‘yanuwa dana matarsa. Da Allah ya tashi ikonsa ya aikowa Mal Junaid hadarin motar da yai sanadin dakushewan kwakwalwa, bai iya tuna kowa da komi, hatta mata da ‘ya’yan cikinsa.
Asibitin Murtala aka kwantar dashi lokacin bai bude nasa ba.
Duk da haka shi ya dau nauyin hidimar komi Wanda yasa matar uban kuka da hawayenta sharaf -sharaf tana roko gafarar Kaltume da danta, Wai Ashe tun kafin ta auri Mal Junaid tayi asirin farraqa shi da mahaifin gudun Wai kar tazo ta haihu ya nunawa Haseeb fifiko (Kunji wani rashin tunanin) to ta cimma burinta amma ta dawo tana dana sani wace a baya takan tsaya inji hausawa.
Shin mu mata bama tunanin cewan duk yaron da aka tsana cikin gidansu Allah na iya daukaka shi ba? Shin bamu tunanin tunda bamu muka halicci mutum ba bama iya tsarawa wance ko wane abinda zasu zama a rayuwa? Allah ya kiyashemu aikata aikin dana sani, domin da mutane sun san hassada takin arziki ga Wanda ake yiwa da ba ka yi ba.
Ta roki Kaltume da danta gafara sun yafe mata to shu mijinta data ha’inta yake kwance bai san inda yake ba fa, wanda ya rasu kwanaki uku da yin hatsarin, wata shari’ar sai gobe kiyama.
Bayan rasuwar mahaifinsa ya dauki nauyin kulawa da dukkan hidimomin kanninsa da uwarsu. Bayan an raba musu gado ya budewa kowannansu shago a kasuwa saboda sun nuna sunfi son kasuwanci ba karatu ba balle aikin gwamnati, ko da aurensu yazo ma shi ke kan gaba wajen basu gudumuwarsa, uwarsu sai godiya take tunda ta dawo hanya ta tuba Allah ya sahale mata bakin cikinta kullum cikin istigfari, tsakaninta da Haseeb sai san barka.
Mahaifinsu ya rasu da shekara guda tal Allsh yaiwa mijin mahaifiyarsa rasuwa, Haseeb yayi babban rashi yai kukan rashinsa, a dalili da duk fadin duniya su hudu kawai ke zaunar dashi su fada masa gaskiya, daga mahaifiyarsa sai shi sai Alh. Muhd sai kuwa abokin mahaifinsa daya saba dashi tun Yana zuwa daukar karatun allo, to ko da ya girma bai yada malaminsa ba
Bayan ta gama takaba ne ya saya mata gida a Yakasai da yake daman gidan Mal. Sunusi na tarayya ne, shekara na zagayowa ya kaita ta sauke faralli, ta dawo ta bata jali tunda ta nace sai tayi sana’a.
Dr Haseeb Junaid ya saki wata doguwar ajiyar zuciya, ko me yasa brain dinsa tariyo masa abinda ya wuce oho don wasu tuni ya fara mantawa sai fa yau. Tunaninsa ya koma Kan yadda ya rike kaninsa da suke ciki daya, ko girmamawar da suke masa ya isa yai hidimta musu cikin kowanne hali in ya ture batun shakuwar da yayi dasu kenan, su Hayatu na kaunarsa fiye da zatonsa musamman marigayi Rabi’u, ya tuna yanayin aurensa da ya taso a gurguje haka ma haihuwar ashe ba dadewa zaiyi a duniya ba
A kullum ya tuna wasiyyarsa garesa inda ya bashi amanar Rahima da Abdul ransa kan dugunzuma ya bacu ya rasa me ke masa dadi a sararin duniya, to sai gashi wai shine da Shirin auren matarsa, babu irin tunanin da bai yi ba kan issue din but tabbas akwai Shirin da Allah cikin al’amarin, yes da akwau hukuncin Malikal Mulk don haka gara ya cire komi a zuciyarsa ya rungumi kaddara.
Shigowarsa biyu kenan yana ganinsa cikin zurfin tunani don bai ko san ya shigon ba sai a na uku ya sallama ya fada falon, ya amsa yaga kamar Daktan na share hawaye tunda ya cire glass dinsa, yai kamar bai gani ba ya mika masa hannu suka gaisa.”Ka dade kana jira ko afwaan.” Cewar surukinsa.