
Ya manna dark glasses din a fuskarsa tukunna kafin yayi dan murmushi “Ai ban wani dade ba Alhaji”. Ya mayar masa.
Sanin miskilancinsa da rashin son yawan magana yasa Alhajin baiyi masa shishshigi bai tambayarsa sai abinda yaso fada masa da bakinsa, ganin halinda yake ciki na damuwa ma baisa ya nemi jin ko menene ba har suka yu ‘yar hirarsu, zuwa can Alhajin yace “Wai Ina Zuwaira ne tazo ta zubar da yara daga zanje un dawo yau kwana biyu kenan bata ba labarinta?”
Ya amsa “Tana can suna hidimar bukin wata kawarta ce, nasan ko zata waiwayesu sai an kare komi.”
Uban yaja tsaki “Watau ita dai ba zata daina halinta ba ko? Amma ban zargin kowa sai kaina Dana shagwabata, na manta cewan diya mace ce komin dadewa aure zata yi, nasan da wani take aure da tuni ta sako min it’s, an taba mace na sanin ya kamata ba kamun Kai?”
Haseeb yace “Allah ya kyauta a ci gaba da yi Mata adduar shiriya don tayi nisa Alhaji.”
Ya nisa “Wallahi tuni na fahimta wace bata damu da yayan cikinta ba ma? Wallahi ko jiya Saida muka yi maganar nan da uwarta, duk dai kuskuren ne, gata ko cuta? Shawarar dana yanke idan ka gaji da halinta ka sakota ko Allah zaisa tayi hankali karta gurbata maka tarbiyyar yaranka.”
Haseeb ya sunkuyar da Kai “Allah ya tsare, tsakanina da ita babu saki unless haka Allah ya rubuto Mana Ina Nan Ina Mata addua.”
Alhaji ya girgiza Kai “Duba Nan Dakta wallahi kasan rantsuwar musulmi kenan ko? Idan kaga ba zaka iya zama sa ita ba ka sauwake mata ka huta, nuna haifeta nasan halinta sarai don haka na baka izni, kar kaji nauyin komi Kar Kuma kayi tunanin yadda muke da Kai, tsakaninmu da ban hulda da matarka daban, ni ba zanso ace ka zauna da ita tana cutar ka kana hakuri sabida ni ba, nima na fara gajiya da halinta, uwarta ma tayi fushi da ita muddin Kuma ba zata zauna gidan aurenta tabi dokokin Ubangiji ba bani bata.”
Ya fara rarrashun tsohon yace “Allah ya huci zuciyarta insha Allah muna fatar ta natsu, may be idan taji zanyi aure.”
Alhajin yace “Alhamdulillah kamar ka shiga zuciyata, shawarar da nayi niyyar baka kenan ince ka Kara aure ka huta da wahala wannan yar banzan.”
“Don Allah Alhaji ka daina zaginta kayi hakuri, daman abinda na zo shaida maka kenan batun auren amma har ga Allah bani na nema ba, iyayene suka ga ya dace in auri matar marigayi Rabiu, gaskiya da ban amince ba amma daga baya sai Ina ganin watakila auren ya zama sanadiyyar shiriyyar Zuwaira domin yarinyar tasan addinita na yaba da hankalinta kwarai.”
“To Masha Allahu haka ake so, Allah yasa ayi damu, yaushe ne daurin auren?”
Ya gyara zama “To ai kune masu neman auren Alhaji shine nazo sanar maka gobe idan Allah ya nuna mana sai ku tafi, nan dai Yakasai inda aka daura auren marigayin, daga nan zan nufi wajen Malam Nuhu ne in sanar dashi shima.”
Alhaji yace “Karka damu amma Ina fatar ba za a dau dogon lokaci ba.”
Haseeb yace “Nima hakan nike so.”
Daga nan ya nufi Sharifai gidan Malamin nasa ya shaida masa halinda ake ciki. Malam yai murna ya shiga yi masa nasihohi musamman kan kwatanta adalci tsakanin matan daman tsoronsa kenan tunda yaga yadda mahaifinsa yaiwa Mahaifiyarsa.
Malam ya Kara masa da shawarwari da adduoin fatar alkhairi da neman jagorancin Ubangiji.
Yana Kan hanyarsa ta komawa gida yana mamakin irin na’am da farin cikin da kowa keyi Kan wannan auren, zuciyarsa ta Kara karfi, nan bisa hanya ta fara tsara yadda yake son a tafiyar da sha’anin amma har sai ya isa gida yaji ta bakin Zuwaira da ita kanta yarinyar da akeyi dominta.
10/09/2020, 06:02 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by Jami
23
Karfe goma sha daya na dare ya isa gida amma har zuwa lokacin Zuwaira bata koma ba, ya tube ya shiga wanka ya fito ya hada ruwan shayi tukunna kafin ya zauna kallon tv
Sai sha biyu saura na dare yaji maigadi na bude mata gate din gida ta shigo da motarta.
Ko da ta shigo falon bata lura yana kwance bisa settee ba, tana tafe tana ‘yan wake-wakenta, sai wani irin kamshin turare Mai shegen haea Kai take, har zata wuce bedroom ta gansa taja ta tsaya masa kerere bisa Kai “Oh ashe ka dawo ban lura da motarka ba.”
Ance tankawa yabawa biyan bashin matsiyaci, bai ce Mata uffan ba, ta fasa shiga ciki ta dawi ta zauna kusa dashi ta fara kame-kame, kusan minti biyar tana ta surutu ba tareda ya tanka ba ta gaji tayi shuru.
Ya kalli matar da suka shafe shekaru fiye da takwas da aure Amma m har zuwa lokacin Nan bai San dadin auren ba, bai San me zai karas ba, ya kanji dai abokansa na hirar hidimar da matayensu keyi musu.
Ya sake kallonta ya rasa me zaice Mata, to bata jin wa’azi, in anyi mata fada ta tashi tana masifa tace an tsaneta, idan aka rarrasheta ta zake har tafi da don haka ya zabi yin biris da ita kawai yafi masa alkhairi ya ci gaba da yi mata addua
Da taga yaki ce mata komi ta mike zata shige ciki harda sakin dogon tsaki…
Takaici ya kamashi kawai ya sakin mata bom “Zuwaira Ina sanar dake Zan Kara aure.”
Tayi wani irin juyi gaba daya, hankalinta ya dawo garesa sosai taga Yana kwance lakadan kamar bashi ya furta Mata wadannan kalaman masu dacin gaske ba, ta buga kirji “Aure! Aure fa kace??
Ya amsa “Kwarai ba kince gara inyi ba zai fi Miki nono fari?”
Ta sake buga kirji “Ni din wace sakaryar macece zata ce da mijinta ya kawo Mata kishiya?”.
” Sai ke Kuma shawarar taki na dauka.”
Amsarsa ya sake tunzurata “Oh ashe zargina ya Zan gaskiya da wace ka aje a waje that’s why kake wulakanta ni kana nuna min halin ko in kula.”
Yace “Ni ban wulakanta ki ba, ban Kuma ajiye kowacce mace a waje ba don Ni ba fasiki bane.”
Tayi tafi ” Abokiyar yin naka dai zaka auro a tahi a cakuda min ‘ya’ya da shegu.”
Ya tashi daga kwance da yaji zata wuce gona da iri yace “Kinga karki batawa yarinyar mutane suna, ba wata daban da baki sani ba Zan aura, ai kinsan Rahima maman Abdul ko,Allah yai nufin ita Zan aura “
Taji dum amma hakan bai hanata yin shewa ba “Ahayye girma ya Fadi, su Yaya babba anji kunya, to daman kace ka gani ka kyasa tuni ba damar yi masa snatching ne da ransa, yo Ashe duk shan mur da kau da Kai na munafunci ne ana so ana kaiwa kasuwa, to me yasa tun farko bka aureta ka barshi ta aureta. Gaske naga danta ya zama dan lelenka sabida son uwa ke sa na d”a. Amma wallahi ka ban mamaki ka bani kunya, ka rasa matar da zaka aura sai matar kaninka Haseeb, wannan abun kunya dame ye kama?”
Maimakon yaji haushin magsnganunta dariya suka bashi yace “Zuwaira wane irin kunya Kan abinda addininmu ya halasta bayan kinsan ance babu kunya a addini? Abinda ya halasta ne mu mutane muke haramtawa kanmu sabida jahilci, to in ba tsintsar jahilci ba Ubangiji ya halasta abu Kai bawa ka kawo al’ada da wasu shirme ka gindaya? So ki fahimci akwai aure tsakanin wa da matar kaninsa idan ya rasu za Kuma ayi shine na sanar dake don shi Alhajinku ma rokona yayi ayi da wuri Kar a dauki lokaci, to na bi shawararsa sai kije kiyi tunanin me kike bukata inyi miki ma fadar kishiya?
Ta tabe baki “Idan duk jikina kunnuwane ba Zan taba yarda cewan Alhajinmu da kanshi zai goyi bayan ka yiwa diyarsa kishiya ba.
“Me zai hana tunda diyar bata neman albarka bata faranta ran iyayenta?”
Ta balla masa harara “Don zaka auro wannan yarinyar ce kake fada min magana?”
Yace “Ke Kika ja yai nisa, and ki bar tunani cewan yarinya karama zan auro shekaru nawa kika bata?”