NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ta gatsina hanci “Yo Ashe ma tsohuwa ce kake wannan rawar jikin da dimirgishi Wai dafa kauri ba da.”

“Nima ai tsohon ne tinda na na Kai 41 yes Kinga za mu yiwa juna daidai kenan.”
Ta kallesa ta watsar “Kaji dashi Wai ciwon ajali a Dan yatsa.”

Ya dagi ya kalleta “Please shiga ciki ki kwanta kin dameni da surutu sai da safe.”

Tayi kwata “Surutu yanzun na bude chapter sai dai Kuma idan dinke bakina za kayi tunda baka da tausayi a zucci ka yanka ka dinke, Kuma gobe gidanmu za ni.”

Ya amsa “Allah ya Kai mana rai suma nemanki suke kije kije ki kwaso yaran da kika zube a can tamkar basu da gata.”

Yana fadin haka ya gyara kwanciyar sa nan alamun ba zai ma shiga bedroom din ba balle taci gaba da bala’in.

Ta gaji da zama taja jiki ta nufi ciki tana Kun kunai kamar wata yarinya karama.
10/09/2020, 12:29 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami

24
Gari na wayewa ko wanka bata yi ba tana idar da sallah ta nufi gidansu, Kai tsaye ta wuce dakin mahaifiyarta, Hajiyar na zaune tana lazumi don al’adarta kenan.

Ta dago taga Zuwaira ce taci gaba da karatunta ba tare da sake kallon inda take ba, ita kuwa ta haye bisa gadon uwar ta kwanta.

Ba a jima ba taji muryar mahaifinta ya shigo yadda yake yi duk safe ya zagaya dakin kowacce mata yaga yadda ta kwana tareda iyalinta yaji ko tana da wata matsala su tattauna hanyar da zasu bullowa al’amarin.
Ya zauna falon uwargidansa Hjy Lami yana jiran ta kare adduointa, Zuwaira taji muryarsa ta taso ta fito ta durkusa ta gaishe shi. Ya kalleta cike da mamaki “Ba dau Zuwaira nike gani yanzun ba, tun yaushe kika shigo gidan Nan?”

Ta sunkuyar da kai tace “Ban dade da shigiwa ba, ina kwana?”

Ya kalli agogon hannunsa yaga ko karfe takwas bata cika ba cikin tsawa yace “Wace irin sakayyar yarinya ce, ki baro gidan mijinki tun sassafe ki zo me zaki dauka?”
Ta marairaice “Karansa na kawo Baba, wallahi duk ya canza, yanzun ma wai aure zai yi, da karya ma har yana cewa ka bashi goyon baya?”

Uwar ta shafa adduarta ta fito ta durkusa gaban mijinta ta gaisheshi ya amsa kana cikin bacin rai yace “Ya akayi kika Kyaleta a zauna har tana kwanciya miki a dak?”

 Hjy Lami ta kada Kai "Yadda ka ganta hakan na ganta ko gaisawa ba muyi ba."

Yace “Mutumiyar banza kina nufin kin kwaso kafafunki ne kinzo muyi miki mene, mu hana sa aure? Wallahi Mamana (haka yake kiranta saboda sunan mahaifiyarsa yasa mata) kin ban kunya, ban taba tunanin ba zaki zauna gidan aureki cikin mutunci ba,yarinya kin zama sai kace goyon arna?”

Hjy Lami tace “Ya za ayi mijinki ya kalleki da mutunci bayan kin zama tamkar maras mafadi?”

Ta saka kuka “Wallahi Mama Haseeb kazafi yake mini.”

Alh Muhd ya sake daka mata tsawa "Rufa min baki ko in tashi in tattakaki, wallahi muddin baki canza dabi''unki ba daga yau mun sa kafar wando daya ni dake, bar ganin na sake miki ina ksunarki, zata koma kiyayya tsakaninmu Kuma kin sanni sarai kamar yunwar cikinki, wallahi ko ke kadai na haifa ina iya yafeki har abada don banga amfaninki ba."

Hjy Lami ta kalleta cikin bacin rai tace “Dubeki yarinyarki dake kin bata rayuwarki da kanki ga kinan duk kin jeme kin lalace, Kuma da kike cewa kazafi likitan ke miki su mutanen duniya da kike mu’amala da kawayen banzan da kike hulda dasu duk kazafin ne? Duk inda kika shiga ana ga ‘yar wance da wane.”

Alh Muhd yace “Dalili kenan da muka bashi goyon bayan ya auro mai mutunci tunda ke kin zubar da naki, idan kinga ba Zaki iya zama dashi ba ga hanya nan bude to banga amfanin zama da igigiyar aurensa a kanki ba, sai kije kiji da zunubi daya.”

Uwar ta fashe sa kuka “Alhaji kalli yarinyar nan ka gani ba abinda ta sawa gaba sai burin duniya da kyale-kyale, dan rayuwar da take takaitatta. Wai don Allah wane irin gata ne ba a nuna miki ba? Me kika nema kika rasa a gidanku ko na mijinki? Allah ya hore dukiyar da ake taimakawa wasu ma, to me kike nema ne?”

Maimakon ta nuna alamun nadama sai ta dauko wani zancen da bai danganci fadar da ake Mata “Mama ni gaskiya ba Zan zauna da kishiya ba, kishiyar ma yarinyar data san sirrina, bayan duk wata takama da Haseeb ke yi da wani ji da kai, mahaifina ne silar duk abinda ya samu, duk abinda yake takama dashi Kai dinnan Baba kaine sanadin, ko yana nufin anci moriyar ganga ne za a yarda kaurenta, to gaskiya Baba da sake…

Bata ga mikewarsa ba, ji tayi kawai an dauketa da tafi ta kifa kasa, ya bita ya taka yana zagi, uwar ma ta rufeta da duka, Nan ta fara kwarma ihu sauran matan gidan suka taru don cetonta..
Da kyar da rarrashi aka kwaceta, ko kafin ayi haka fuska ta kumbura jiki ya murzu da duka.

Alh Muhd ya fara haki, jiri ya kwashe shi, matan suka tareshi, akayi hanzarin dauko masa maganin hawan jininsa aka bashi yasha kana suka kamashi ya koma daki ya kwanta.

Hjy Lami ta dawo dakinta ta cimma ‘yar nata kuka tace “Ya jikin Baban?”
Ta kalleta ta watsar “Tashi ki bace min da gani, ina ruwanki da jikinsa? Ai kinsan yanada hawan jinin don kece sanadi, to ki dage ki zama kece ajalinsa.”
Ta Kara fashewa da kuka “Don Allah Mama ku yafe min, Allah zan daina komi, bacin raine yasa Ni fadin wannan maganar.”
“Da gangar kika yi tunda an Sha gargadinki kan furucin da kike yi, yau kika yiwa mijinki gorin? Maras tunani, da kike fadin ubanki ne silar arzikinsa yanzun hidimar da yake mana ya zama ke Kika sa shi? Yarone dan halas da yasan darajar iyayensa da naki.”

Ta daga kai “To Ni Mama so kuke in zura masa ido Kan batun aurensa?”

“Ah ah kike kiyi abinda zaki iya kinji zabin da muka baki ai. Ni tashi ki fita min a daki, ki Kuma dauki yaranki ki maida gidan ubansu tunda baki San ciwon kanki ba, albasa bata yi halin ruwa ba.”
10/09/2020, 18:03 – Anty saliha: ….RAHIMA…doc by jami

25
Zuwaira ta tabbatar wa kanta ba zata sami yadda take so wajen iyayenta ba, saita canza shawara ta tuntubi Husaina daya daga cikin kawayenta a tunaninta ita din ce kadai zata iya taimaka mata warware matsalarta.
Tafiya mikakkiya ta isa gidan Husaina dake gadon albasa, Sha daya saura na safe ta matsa kararrawa, saurayin dake mata wanki da guga ne ya bude mata kofar ta shiga yana gaisheta ta tambayesa “Ina Hajiyar?’

“Tana ciki.” Ya amsa.
Kai tsaye ta wuce bedroom din Husaina ta taras da ita a kwance “Lalle kina jin dadinki, ni ina ga time din barcin safe?”

Tayi Mika tace “Zuwaira Wai Ina kika shigane tun safe nike neman wayarki?”
Zuwaira ta zauna bakin gado “Kinga ni yunwa nike ji bari in ci abinci tukunna kisha newa.”

Husaina ta dago ta kalli yanayin fuskarta ta saka salati ,”Ke ya aka yi haka?”

Tace “Labarine mai tsawo bari in koshi jikina har rawa yake, rabona da abinci tun jiya wajen bukin nan.”

Cikin hanzari ta kira yaron gidanta ta umurcesa yaje ya hado musu breakfast, ya fita da sauri."

Zuwaira ta kalleta sama da kasa “Haba Husaina dubi shigarki fa sannan kika yaron gidanki har cikin bedroom dinki?”
“Look Zuwaira nu dake duk kanwar ja ce fa, jirgi daya ya kwaso mu, ya saba shigowa sai me?”
Ta gyada Kai “No duk rashin da’ata ba zan bar wani kato ya shigo min cikin dakin barcinmu ba don na dauke shi matsayin sacred secret place

“Hhhmmm ba dai kin koshi ba? Mu bar zancen mu koma na dalilin nemanki, shin ina Alhajin da yaso like miki wajen bukin nan, ya dameni in bashi lambar wayarki, ya isheni da naci that’s why na kiraki tunda safe, me ye ra’ayinki?”

Tayi saurin girgiza Kai “Raba da wuya kinji, in don kayan da muka ce muna so ne zamu sara ya taimaka mana ya bar abinsa, irinsu sun cika mita kawai ya hana min sikit.. Ni dai yanzun Kinga fuskata ko? Wallahi aikin Baba da Mama ne suka taru sukai min sukuwar Sallah don nace ban amince Haseeb yai aure ba.”

Ta furzar da ruwan da sanyin data kurba ta bugi kirji cikin tsoro “Dr Haseeb zai yi aure? Wonderful…
“Kin ganni nan fa cikin tashi hankali nike, that’s na garzayo bidan shawarki don iyayena sun bashi go ahead.”

“Yo inya sakeki ba kin huta ba, ga masu sonki ido rufe?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button