NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tace “Sakin bai dameni ba, hakan nike so Amma wallahi ba zan bar gidansa kafin aurensa ba wannan yarinyar ta dauka ta isa ta koreni, sai tazo ta zauna na nuna mata ruwa ba sa’an kwando bane, wutsiyar rakumi tayi nisa da kasa.”

Husaina tace “A ina ya samu matar ne?”

Ta amsa “Matar kaninsa daya rasu dinnan nan, shine iyayenta suka cusa mata ita don sun ga da maiko.”

   "Tashin hankali inji Husaina ta Fadi cikin karaji "Yarinyar dake teaching makarantar kurame?"

“Yes ita, wani abu ne?”

Ta kada Kai “Yadda nike ji yarinyar nada kamun Kai da rike addininta, Kinga ko nan an samu difference.

   "Wannan lalurar tace Husaina ta Fadi tana daga kafada irin bai dameta ba dinnan, fada min meye shawara yanzun?

Tayi shiru tukunna kafin tace ” yanzun Kam kwantar bauna za muyi mu jira ta tare sai ki bullo da kissa da munafunci hade da karfar baka Wanda yafi asiri aiki mu gama da ita. Da dai baki da niyyar barin gidan ne da mun hadata da malam Mai gobe da nisa.”

Zuwaira tayi hamma tace “Shikenan sai mun sake haduwa, bari in koma gida don yau harda su Khalifa su Mama sunce in kwashesu, na baro an kaisu makaranta ne.”

Tayi tagumi “Oh in banda abin Dakta meye na hadaki da iyaye Kuma, ya barki kiji da jinyar kololon bakin cikin daya mulmula ya saka miki a kahon zucci don kishi cuta ce.”

Ta mike tsaye” Ki barsa kawai zan bashi mamaki, ni kam na tafi.”

“Zan iskoki har gida ba sai kinyi wahalar dawowa ba, yi jinyar tsamin jikinki.”

Yau kwana biyu kenan da taji labarin Hjy Kaltume na fama da zazzabi,tayi niyyar ta share ko ta aika kawai a dubota, Umma da Maryam sunce bai dace ba, ciwo ya kore komi Kuma tafi gaban sharewa a wajenta, ita tasan hakan illa dalilan da suka taso suka haddasa nisantar junansu.

Ba domin batun aurensu da ya taso ba ai Hjy Kaltume uwarta ce mai bata nono tasha ta koshi.Tuni ta daina jin haushinta sai kunya data karu fiye da dauri, ta bi maganar iyaye ta shirya zuwa dubo Hajiyar

Karfe takwas daidai ta fito daga gidansu sanye da wata doguwar riga ta yadin Kampala shadda maroon colour, wace ta dora Mata after dress a samanta cream colour.

Tafiyar cikin rashin karsashi a natse take yi alamar dole ne yasa ta fito.

Iskar dake bugawa a hankali ta rinka kada abayar da lullubinta, tafe take tana jan adduoin neman kariyar Ubangiji daga sharrin mazan dake ta son yi mata magana
Yau saita ga gidan Hajiyar yai mata nisa, iya kauda kanta Saida wani Mai motar ya kyala ido ya ganta, ya Kuma bi bayanta har zuwa daidai lungun da zata shiga kwanar gidan Hajiyar, yai parking ya fito ya tsaya jiran fitowarta….

Ta shiga tareda sallama, Mairo ta amsa cikin murna “Marhabin maman Abdul sai yau, idonki kenan?”
Tayi dan dariya “Kinada bakin magana ke sau nawa kika taho wajena?”.
“Ai kuwa sai dai ki zargeni na kanje in duba Umma mana” Mairo ta kare kanta…

“To ai shikenan ya jikin Hajiya?”
“Da sauki kin San halinta ai bata son a ga gazawarta.”
Rahima tace “In shiga in ganta, Allah ya sauwake.

Hjy Kaltume na kwance bisa katuwar katifar da aka fito mata da ita falo, ta dago kai, tunda taga bakuwarta ta tashi ta zauna “Ni fa naji kamar muryarki sai naki amince ke dince tunda kin gujeni Rahima, Ina dan gidan Baba?”

Rahima ta zauna kusa da ita daf da katifar ta gaisheta tukunna kana ta ajiye ledar data riko mata lemu da ayaba tace “Allah ban gujeki ba Hajiya hidimomin ne sukayi yawa, Abdul na baro sa gida naga darene yasa bance ya rakoni ba, Su Baffa da Umma na gaidaki da jikin.”

Tace “Nagode Allah yai albarka Ina amsawa, ita Umma takan lekoni, nima nakan aiki Mairo ta dubota.”.

Rahima tayi shiru, zuwa can ta tambayeta “Hajiya ko irin rashin lafiyar nan ce da kika taba yi bayan an kawoni ba dadewa?”

Ta amsa “Ina tsammanin shine, domin yanayin jikin nawa kasala ce ke rufeni inji ko hannuna ban iya dagawa balle inyi motsi mai karfi, ga rashin samun isashshen barci, dare ya tsala kiga kowa na barci Ni kuwa lokacin nawa idanun zasu bushe in kasa barcin in rasa kuzarin tashi in gabatar da kiyamul lail yadda na saba, shi yafi damuna.”

“To kin sanar da Yaya kuwa?”
Ta kada Kai “Hhmmm wannan Yayan naku hidimomi sunyi masa yawa, baida kwanciyar hankali wallahi har tausayinsa nike ji shiyasa nayi biris da tawa lalurar.”

"Hajiya ba'a yiwa ciwo haka fa, idan ya fahimci halinda kike ciki ba zaiji dadi ba, to Yaya Hayatu fa?"

“Shima bai sanin ba Yana can yana zirga-zirgan Shirin tafiyarsu Hajj.”
Rahima tayi dan murmushi “Ai kuwa da sauran lokaci ko azumi ba muyi ba.”
“To Rahima Mai kwarmin ido ba da wuri yake fara kuka ba? Duk da ba karamin kuzuri aka biya musu gara dai su nema su Kara saboda mutum bai San yanayin da zai kasance a kasar da ba tasa ba.”
“Hakane gaskiya, zuwa Hajj Kam a wannan lokacin said mutum ya shirya, Allah yasa a dace.”.

Hajiya tace “To ameen, tabarbarewan al’amurran kasarmu sai addua.”

Rahima ta tuna dare ne ba rana ba, ta yunkura ta mike tace “Hajiya dare nayi bari in isa gida Zan dawo in an kwana biyu.’

Ta bita da kallo kawai na ciki na ciki, tana son yi mata maganar Daktan ta kasa, Rahima na jin nauyinta kar ta matsa Mata, taja baki ta tsuke… Kafin suyi sallama amon muryar da kesa gabanta faduwa ce ta tsinkayo yana magana da Mairo… Nan take kirjinta yai mata nauyi sanadiyyar bugawar da zuciyar keyi ba control, tun kafin ya iso kamshin turarensa ya Kara tabbatar mata da shigowarsa.

Ta mutu a tsaye, gaga tsara gaga, wannan shine gaba damisa baya siyaki, Ina zata shiga, uwardakin Hajiya ko saurin ficewa?
Ta juya kwakwalwarta tayi dim ta tsaya cak! taki aiki balle taba sauran sassan jikinta umurnin next step da zata dauka.

Ya kunno kai cikin dakin bayan Hajiya ta amsa sallamarsa, Yana shiga ya doshi gefen katifar uwar ya zauna, ya dago ya kalli Rahima dake tsaye a sandare yace “Ba dai har zaki tafi ba, daga can gida nike Umma tace kina nan.”

Da za abata zabi da basu ko gaisa ba ta sulale ta gudu that’s in tafiyar zata yuwwu mata kenan da gwiwoyin da suka yi sanyi har kafafunta na rawa, nan ta durkushe ta gaisheshi.

Amsar da ya bata cikin sakin fuska ya bata mamaki, eh to a gaban Hajiya ai ba zai rinka wannan cin maganin ba a nata tunanin.
Cike da farin ciki da jin dadi ta kallesu “Ko zaka rage mata hanya ne tunda tayi shirin tafiya?”.

Rahima ta girgiza Kai “Hajiya tafiyar guda nawa ce, ba komi nagode yanzun zan Kai gida, mu kwana lafiya, Allah ya Kara sauki.”

Dr Haseeb yayi dan murmushinsa ba tare da yace komi ba.
Hajiya tace “To shikenan Allah ya bamu alkhairi, nagode Allah sa albarka.”

Da hanzarinta ta fito waje ta saki wata ajiyar zuciya amma me zata gani? Mutumin dake jiranta ya fito daga mota ya karaso wajenta "Salamu Alaikum don Allah Hajiya ina son magana dake."

Ta kalleshi a tsorace ta amsa “Nima don Allah kayi hakuri bani da lokacin magana da Kai.”

Babban mutum ne da ganinsa bata son cin mutuncinsa amma bai fahimci hakan ba ya sake matsawa kusa “Yi hakuri ki bani minti biyar kacal, sunanki da uguwarku nike son sani tunda kina sauri yanzun ki bani time in taho gida ga compliment card dina.”

"Hajiyar ta gode rike card dinka don bata bukatar sanin sunanka an riga anyi mata miji.". Bata yi aune taji muryar Haseeb na maida jawabi.

Mutumin ya kalli Rahima yaji bata musa ba, ya kalli Haseeb duk da yana sanye da bakin glass dinsa fuskar nan ba alamun rahama nan da Nan yace “Don Allah kuyi hakuri sai anjima. Suna kallonsa ya shiga mota ya tafi.

Sun dade ba tareda cewa juna kanzil ba, ta tuna gida zata tafi, ta juya tace ‘Nagode, ta fara tafiya…
Ya bita da kallo “Na yiwa Hajiya alkawarin kai ki so ki shiga mota mu tafi or are you ready for that kind of attention irin Wanda ya faru yanzun?”

 Cikin siriryar murya tace "Ni bani na kirashi ba..

“Ba zarginki nayi ba, mu tafi ko?”

Tare suka shiga motar yaja suka isa cikin minti goma kacal. Motar na tsayawa ta bude kofar ta fito tace “Nagode a gaida su Aunty”

Ya waigo “Magana nike dauke da ita ko kina jin barci gobe na dawo?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button