
Ta girgiza Kai “Ba damuwa, mu shiga daga soro ko?”
Ya fito ta rufe motar yana biye da ita, suna shiga tace “Zan amso key din dakin baki.
Ta wuce cikin gida ta shaidawa Umman tana tareda bakone, Umman cikin farin ciki take wanda bai misaltuwa don ta gane waye ta Rahima ta kira bako. Har zata fita tace “Haka ake tarbon bakon ko ruwa ba zaki Kai masa ba balle lemu? Ban sanki da rowa ba Rahima.”
Ba tareda da tanka ba ta bude fridge ta dauko gorar ruwa da lemo da cup ta dora bisa faranti ta koma soron, Yana ganinta ya mika hannu ya amshi kayan ta bude kofar tace “Bismillah.”
Bayan sun shiga ciki ya ajiye farantin ya zauna kan kujera, Saida ta durkusa ta zuba lemun a cup ta ajiye sannan ta zauna gefen tabarma.
Ya dan kurbi lemun kadan ya mayar ya ajiye yana kallonta ta cikin dark glasses dinsa yace “Ina Abdul dina ne ko har yayi barci?”.
Ta daga Kai “Ya riga yayi barci.”
Yace “Yaron dana san yana kai wajen sha daya bai kwanta ba sai anyi ta fama dashi?”
Tace “Ban da yanzun kuwa ko don bai jin dadi ne oho.”
Ya bude baki cikin mamaki “Ya akayi ban sani ba, baki aiko min ba ko Hajiya?”
Can kasa tace “Don naga ba it’s not that serious.”..
“Ya akayi kika San hakan?” Yai tambayar a fusace.
Ta sunkuyar da Kai “An kai shi asibiti sunce malaria ne sun bada treatment shi yasa naga ba sai na aiko ba.”
Ya gyara zama “Daga yau karki sake min haka, duk abinda ya shafesa wajibi a sanar dani komin kankantarsa do you get me?”
Ta daga kai alamar amsa.
Ya kalleta sai Kuma ta bashi tausayi, ya sassauta murya yace “Look why not a daura auren nan this week mu ragewa kanmu jidali tunda Allah ya kaddaro mana haka, daman shawarar dana zo mu hadu mu yanke kenan. Mu ba yara bane, mun San ciwon kanmu naga zaifi dacewa ayi abinda iyaye keso zai fi mana sauki…
Rahima tayi shiru yaci gaba “Ko Hajiya abinda ke damunta kenan saboda ta sanya abin a ranta.”
Ta dai kyalesa ya shirya mai yuwwa tana saurarensa yayi ya gama, ya mike zai tafi ya mika mata rafar kudi tareda tsadaddar handset.
Cikin kwanaki uku kacal aka gama tsarawa da shirya komi. Daktan ya aika kayan aurensa akwatuna biyar, ya shaida mata ba zai ajiyesu gida daya da Zuwaira ba ya nemi amincewar yazo su tafi taga gidan da ya saya inda zai ajiyeta a dorayi, tace ba sai taje ba.
Bata da niyyar yin kowanne irin shiri kan auren, Maryam tayi surutunta ta gaji ta kyale, ba tareda saninta ba sun shirya abinda ya dace game da gyaran gidan amarya sun Kuma nemi angon yasa an kaisu suka tsara shi yadda ya kamata amaryar data hadu a ga gidanta.
Ranar da za’a daura aurensu tunda asubah aka nemi Daktan ya taimaka ya nufi Riyadh dubo maras lafiyan Nan, wannan karon ba gardama, aikinsa ceto rayuwar dake neman agajinsa da taimakon Allah in yai nufin patient din ya tashi, in Kuma lokacinsa yayi ba makawa.
Yana gab da tashi ya kira Rahima ya bata hakurin rashin samun daman halatar daurin aurensu, tace ba komi Allah ya kai shi lafiya ya dawo dashi cikin amincinsa, tayi masa adduar Ubangiji ya bashi sa’a yayi nasaran shawo Kan ciwon da yai tafiyar dominsa.
Karfe bakwai daidai na agogon Nigeria jirginsu ya daga suka nufi kasar Saudiyya kan hanyarsu ta isa babban birnin kasar Saudiyya, Riyadh.
10/09/2020, 22:44 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
26
Abin sha'awa iyaye, 'yanuwa, da abokan arziki ne suka tsaya aka daura auren Abdul-Haseeb da Rahima.
Kafin ayi haka labari ya baza gari, jama’a suka shiga fadin albarkaci bakinsu wasu suka ce yaci amanar Rabiu, wasu suce daman can da kulalliya tsakaninsu, surutai dai gasu nan barkatai masu matukar daga hankali musamman ga wadanda abin ta shafa, da yake shi angon yai nisar kiwo sai damuwar ta tattara kan amaryar kadai daman cu
cikinta take. Ta yini babu karsashi ba walwala ba wani kwalliya, bata gayyaci kowa ba hatta collegues dinta basu sani ba, to abu ya taras da miskillancin tsiya, ita Sam bata damu tayi kawa ba a tunaninta Maryam ce kawarta, aminiyarta Kuma ‘yaruwa rabin jikinta.
Umman da Maryam sunce ba za suyi taron buki tamkar ana zaman makoki ba don haka suka gayyaci dimbin jamaa bayan ‘yanuwa wajen yinin bukin da suka shirya.
Taro yayi kyau, an ci an sha an koshi, bayan azahar masu wa’azi suka dasa tasu nasihohin suka rinka fassara ayar Allah suna fassarawa. Suka fara da fadakarwa kan masu ganin auren wa ta auri matan kani jahilci ne suka yi kaca-kaca da masu kafa tsirku kan fadin Allah, suka dawo suka yiwa amarya nasiha kan hakkokin mijinta da suka rataya a kanta, suka hangaro na tarbiyyar diyanmu kana daga karshe suka rufe da matsalar data fi addaban Mata yanzun ‘kishi’
Wa’azine masu ratsa zuciya da shiga jiki ga wadanda keda sauran imani sun kudurta gyaran kurakurensu, ga wadanda suka yi nisa Kuma sai ido .
Karfe biyar na la’asra Jamila da Haulatu suka jagoranci tawagar sauran matan kannin Daktan suka taho, a nan drama ta tashi Rahima na kiransu Aunty a matsayinki na matan wan mijinta, yau kuwa reshe ya juye da mujiya, ita ta koma Auntyn tasu a sabon matsayin da Allah ya bata matar babban Yaya.
A can ainihin gidan Daktan uwargidan amarya ta gayyato kawayenta marasu mutunci sun cika gida makil, hatta ‘yanuwanta komawa gefe suka yi suna kallonsu ..
Kawayen sun gama zugata da bata shawarwarin da ba zasu amfaneta ba, harda shirya mata abinda zata yiwa amaryar don tasan ba wurin zamanta bane.
Shashashar ma ashe bata san ma cewan ba gida daya zasu zauna ba, Saida ta aika gidan Hajiya a dubo ko tana can ne aka fada mata dorayi aka kaita.
Ta dakawa Dan sakon tsawa “Dorayi wane gida? Jeka dubo min ka dawo yanzun.”
Suna ta yi mata famfo tana hauka cewan ai kamarta raunin hankaline ma ace mijinta yai mata kishiya ko wane dabiun kwarai take dasu da zai hana ayi mata oho.
12/09/2020, 13:05 – Anty saliha: 🦈🦈RAHIMA🦈🦈
28
Ta sauki mintoci heart beat bai koma normal ba, watau a takaice so da kaunar Ya Haseeb na neman mamaye mata ruhinta, ta girgiza Kai wannan ma ai shine abin kunyar, hhmmm da zai fahimci haka ya zai dauketa, maras tunani ko maras matunci? In kuwa hakane gara ta yiwa kanta rigafi ta danne zuciyarta zai fi mata alkhairi.
Ba sauran barci a idanunta don haka ta fito daga dakinta ta nufi kicin inda ta taras da Uwale harta kama aikin hada breakfast, tana ganin Rahima ta durkusa ta gaisheta “Hajiya barka da fitowa.”
Ta amsa “Ina kwana Uwale ashe kin tashi tun dazun.”
Tayi dariya “Ai mun saba, a can kauye ina muka ga lokacin barcin safe, muna alla-allah bayan munyi sallah mun karya kummalo da dumammen turo mu zuba hatsi a turmi mu shiga neman na abincin rana mu da yara..
Rahima tace “Gaskiya kuna kokari,kuna wahala, shiyasa akace mutum ta rinka kallon na kasa da Kai, nan zaka gane ni’imar da Allah yai masa sai Kuma ka gode masa don wasu sun fi kane Kai Kuma kafi wasu, amma gaskiya idan kika duba rayuwar matan karkara sunada matukar tausayi, sai muce mu aljanna muke.”
Uwale ta nisa “Ina ma ki kasan haka Hajiya, sai Kinga macen kauye a ce miki sa’arki ce ki yita rantsuwar ba haka bane don ta kusa haihuwarki a fuska, ta tsofe ta komade saboda wahala, hakora sun zube, ba isashshen ingantaccen abinci, ba hutu, na kyakkyawar muhali balle wani sutura mai kyau ga rashin samun kulawa daga mazajenmu, yawanci mazanmu fa basu San darajar mace, iyakar ki dashi ki dafa abinci, wata har noman abincin ma da ita za ayi, kiyi surfe da daka, idan ya bukaceki ya sarrafaki kamar yadda yakewa jakarsa da yake kiwo,idan kin dauki ciki ki babu wani kulawa, wajen haihuwar ma wani a rabu kacar sabida yaushe ya barki Kika je wani asibiti don inganta lafiyarki balle na dan cikin ko jariririn da aka haifa, wasu kuwa don su doki mace ba wani aibu bane a garesu, to mazan nawa ne suka san hakkokin matan da ya rataya a kansu?” Dalili kenan koda mijina ya mutu zawarawa suka yo min caa!! Nace bada Uwale ba, anyi daya ba za a kara na biyu ba, da in zauna cikin jahilci da rashin sanin me auren ya kunsa da rashin sanin hakkokin juna gara in taho birni in nemi sana’a.”