NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Baiyi sanya a gwiwa ba nan da Nan ya nemi Baffansu Rabi’u da kanin Hajiyarsul watau kawunsu yai musu bayanin halinda ake ciki. Suma basu bata lokaci ba suka amince, suka hadu su hudu suka nufi gidan Mamman Mai yadi a matsayin mabidan auren wa dansu diyarsa.

Ba wai ta fannin saye da sayar da yadiddika kadau yasa sunan Alh. Mamman yayi fice ba, ah ah duk wani Mai hulda dashi ta cinikayya ko harkokin yau da kullum ya shaidi mutym ne Mai son jama’a da mutunta su, ya iya hulda da mutane kwarai da gaske.

Ta fannin iyalinsa kuwa matarsa uwar 'ya'yansa  Habiba ita kadai ya mallaka, tunda ya aureta suke zaune lafiya, zaman so da kauna da mutunta juna sai bai taba sha'awa ko tunanin karo wata matar ba, gashu sun hayayyafa, Allah ya azurtasu da diya takwas, biyar maza uku mata. A zahiri diyanta bakwai ne amma tunda matarsa ta amshi marainiya Rahima ta shayar da ita yarinyar ta shiga zuciyarsa, yaji yana tsananin sonta, irin son da da mahaifi har bai son yaji wasu su furta bashi ya haifeta ba, itama kanta Rahimar Saida tayi wayo ta fara sanin ciwon kanta  ne ta fahimci cewan ba sune mahaifanta ba, ta Kara tabbatar da hakan yanzun da aka ce mahaifinta na wajen Uba ne yai ruwa sa tsaki wajen hanata ci gaba da karatunta.

Hausawa kance wani ma yai rawa ballantana dan makadi, su Alh. Mamman kan shiga su fita suyi wakilcin aurarraki da dama har sau sunga an kulla sunnar Manzon Allah SAW suke numfasawa to Ina ga Kuma ana batun auren diyarsu aka zi yi, ‘yar lelensa wace yake ji da ita?

‘Yanuwan Rabiu da sukayi tattaki zuwa wajen neman auren sunsha mamakin irin karamcin da akayi musu bayan an karbesu hannu bibbiyu. Sun rabu kan cewan an basu yarinya saura batun sa ranar daurin aure sai abinda ‘Yanuwa suka tattauna zasu nemi dangin angon.

Mutunta su day aka yi ya karawa Hasseb kwarin gwiwar aiwatar da abubuwan da suka kamata dangane da auren. Kudi ya ware masu yawan gaske ya baiwa matarsa ta hado kayan lefe setin akwatuna uku dankare da tufafi, kayan shafa, jakunna, takalma da sauran tarkacen da ake hadawa budurwar data hadu Kuma ta dace da Mai yin. Shi kansa Rabi’u akwati guda ya cika masa da tsadaddun shaddodi na shigar angonci kana ya samar masa Dan madaidaicin gidan da zasu zauna amma mahaifiyarsu taki amincewa da hakan, tace tafi son ta zauna tare dasu tunda daga amaryar har angon yarane suna bukatar zama kusa da manya domin tsawartawa lokaci-lokaci.

 Dalilin haka yasa Haseeb ya gyarawa kanin nasa dakuna biyu dake saman bene, kicin da toilet a gidan Hajiyar tareda Kara yiwa nata bangaren kwaskwarima duk da ko can ko ina a gyaren yake.

Lokacin da Alh Mamman Mai yadi ya tafi gidan aininhin mahaifin Rahima batun auren bayan ya sanar dashi ko su waye maneman, Mal Ali Mai goro ya nuna masa halacci, din kekasa kasa yayi yaki amincewa ayi maganar dashu ya kare da fadin “Wannan yarinya diyarka ce Alh. halak makak, kana da damar aurar da ita ga duk Wanda ka so, mene nawa a cikin wannan zancen? Babu ruwana, Kuma don Allah duk abinda ya taso karka sake tuntubata, kaida uwarta kun isa ku zartas da hukunci.”
Tunda Rahima ta dawo hannunsa sanin kansa ne mahaifinta bai taba nuna masa ba shine ubanta ba, yana yi masa kawaici fiye da yadda ake zato, Yana jin dadin haka, sai dai halaccin da ya nuna masa yau ya tabbatar da Alh. Ali ya cika dattijon da yasan yakamata yasan ciwon kansa. Dadi ya rufesa, zuciyarsa ta Kara zurfafa da kaunar diyar tasa bai san lokacin da ya fara zuba godiya ba…

Alh Ali yace “Ni ke da godiya Alhaji, a yau da zamani ya canza harka sami Mai rike maka d’a tsakani da Allah, ba cuta ba cutarwa, ba wata tsangwama balle banbanci ai sai mutum ya godewa Allah, ya rinka wansa yai masa namijin kokarin nan addua, wallahi ni nakan rasa irun godiyar da zanyi maka ma, Allah dai ya saka da khairan yasa diyan suji kanmu.”
Alh. Mamman yace “Ameen Nima nagode, zamu je mu Kara tattauna batun sa ranar buki da uwarta tunda naga dangin yaron tuni sun shirya.”
Mal Aliyu yace “Ba laifi Allah ya sanya alkhairi yasa za ayi damu, insha Allahu Nima goben ko jibi Zan tafi Gumel in shaidawa tsohonmu halinda ake ciki, kasan tun fil azal shi ta tayar da rikicin Nan.”

Alh Mamman yace “To ya za ayi, duk inda tsoho yake sai lallabawa da lallashi har Allah yasa a rabu lafiya, Ni da nawa tsoffin suka dade da rasuwa har shaawar irinku Nike, yawanci wadanda suka manyanta da iyayensu sai kaga suna musu yadda suka ga dama ko su rinka cewa rigimarsu ta ishesu.”
Mal Ali ya nisa “Wani abin da muke ganin rigima ce sai kaga sunada dalilin aikatawa, yanzun shi wannan wa yasan dalilin kafewarsa Kan lalle sai a fiddata makaranta ayi Mata aure? Mu dai har kullum albarkarsu muke nema dole mu bi son zuciyarsu don mu gama lafiya.”

Alh. Mamman tace “Hakkun, maganarka dutse, Nima Zan shirya in bika mu tafi in Kai masa goro da hannuna in shaida masa diyata ta samu miji yaro danye sharaf ba irinsa ba.”
‘Yan dattijan suka bushe da dariya kana suka yi sallama cike da murna.
03/09/2020, 10:52 – Anty saliha: Afwaan jama’a ga number da zaku turo shaidar payment ayi adding dinku.

080 34243456

 ....ˆRAHIMA...doc by Jami

5
Habiba ta shiga goda tana rafka sallama tun daga sori amma babu wadda taji har saida ta iso daf da kofar daki. Dukkansu ‘yanmatan biyu suka amsa salkamar tare da fadin “Lah Umma yaushe kika shigo?”
Rahima tayi saurin amsar jakar dake hannunta tace “Duk laifin Maryam ce, ta kuntuke da surutu ba wakafi ba aya, balle alamun motsin rai.”

Maryam ta zaburo “Amma da alamar motsin tambayar da baki bani amsa ba ko?”
Habiba ta cire hijab tana fadin “Anyi babbar kwabo, ke kenan ki tasa kanwarki gaba kiyi ta tsatstsagarta?”
Cikin shagwaba Rahima tace “Tunda kika fita gidan ta bude faifaina dana Rabiu har kaina na ciwo.”
Habiba ta jayo kujera ta zauna kafin tace “Bata ko jin kunya, wannan yaushe zaice dake wata Yaya?”
Rahima tayi mata gwalo ba tareda uwar ta gani ba tace “Nima haka Nike fada mata tuni.”
Maryam ta Kai Mata bugu cikin wasa “Ni na rasa irin girman da ake son dora min ba gaira ba dalili alhalin watanni uku kacal fa na bata.”

Habiba tace “Sai girman jikin ba, kowa ya hanku zaiyi zaton shekaru uku kika bata ko Ina Zaki Kai wannan jikin oho.”

Rahima ta sake fakar idon Ummar tasu tayi mata gwalo kana tace "Aure Umma za ayi mata, yanzun nan take fada min wai Abbas ya matsa mata da zancen aure."

Maryam ta kara zaburowa “Allah Rahima ki kiyayeni, Umma karya take min.”

Habiba tasha mur ta kallesu “Eh ba shakka, tabbas Kun cika yan zamani, kiri-kiri Kun zauna batun aurenku kuke ba kunya ba wani shakka, Allah ya shirya Mana,wannan zamanin sai shiru. To ni ince ko Kun dora min sanwa ko kuna can kuna hirar samari?”
“Tun dazun muka Dora Umma.” Suka bata amsa tare sannan suka nufi kicin din domin duba girkin, ta bisu da kallo, cikin zuciyarta ta ce inda da gaske shi Abbas din ya shirya ai da an hada bukin ayi rana daya mu huta.

Maigidan ya dawo ya shigo dauke da ledojin kayan lashe-lashe da yakan sayowa yara, su Rahima suka fito da hanzari suka durkusa “Sannu da dawowa Baffa.”
Ya amsa Yana Mai farin cikin ganinsu yace “Ina kannin naku ne banji motsin kowa ba.”
Maryam ta amsa “Wallahi Baffa suna can sama suna kallo ba suji muryarka bane da tuni sun sauko.”
“Bari na kirasu.” Cewar Rahima. Ta hau a guje ta shiga ta kashe Tv din tace Sarakunan kallo to Bafda ya dawo yana nemanku idan kunga damar sauka.”.

Har da zasu tsaya korafin an hanasu kallo sai suka jiyo muryarsa, sanin lalle da abin lasawan da yake tahowa gida dasu yasa suka rugo kasa suba fadin “Baffa oyo yyo me ka sayo Mana “

Maryam ce ta bude ledan ta shuga rarraba musu youghurt da biscuits, Rahima Kuma ta bude ledan nama ra busde ta rabawa kowa nasa, kafin ta mikawa Maryam tasa hannu cikin na Samunu ta diba yanka biyu ta saka a Baki, yaro ya saka kuka, Rahima ta kalleta “Kash Maryam meye haka?”
Umma ta harareta “Zalunci mana, ba Kya tsaya a baki naki ba gandoki?”
Ta saki dariya “Wallahi miyauna ne ya tsunke Umma.”.
Rahima ta ce “Ai nasan maganinta, ta kasa rabin Maryam din biyu ta mikawa kaninsu, Maryam ta taso tace ba zata sabu ba bindiga a ruwa ta juyo zata amshe na Rahimar, ta gudu daki, ta bita Yana dariya.
Iyayen suka bisu da kallo cike da sha’awa da tausayin su.
Alh Mamman yai ajiyar zuciya ya numfasa bayan yasha ruwan da Umma ta kawo masa tare da abinci, Ya kalleta cike da kauna yace “Kinsan abinda ke damuna?”
Ta kada Kai “Sai ka Fadi Alhaji.”
Ya gyara murya “Ina jimamin yadda yaran nan zasu rabu da juna ne, sauran kwanaki tara kacal fa bukin Rahima, ya ‘yaruwata zata ji?”
Tace “Hhmmm kace ya za ayi da kewar juna dai, Ni kuwa nafi tausayin Rahima na rasa dalili.”
Yace “Ai kinsan maraya da shiga zucci dole ki rinka tuno ‘yaruwarki yanzun musamman da auren nan ya kawo jiki saukinmu idan Allah ya turowa Maryak nata mijin tayi auren sai hankalunmu yafi kwanciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button