NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

   Rahima ta nemi kujera ta zauna tace "Bari in tayaki aikin mu ci gaba da hirar sai mu karu da juna..

Uwale tace "Ai ke Hajiya Allah ta tarfawa garinki nono, da mata na dacen irin mijinki da ba za suyi kukan komi ba, ko su Mairo da suke 'yan aiki sun shaida balle ku, kin kuwa ji ance kyakkyawar safiya tun daga maraice ake fara ganewa, jumma'ar da zata yi kyau tun laraba ake ganeta, wallahi haka nake son namiji yasan mutuncin 'ya mace.

Rahima tayi dariya “Ai ko mazan namu ana samun wadanda basu San darajar macen ba, da na dauka jahilci ne yasa wasu mazan ke maida matansu tamkar jakuna ashe ba hakan bane, ko a birnin haka wasu mazan suke, kiga namiji bai san mutunci da darajar matansa ba, mace bata isa yai shawara da ita ba, don a ganinsa shirme ne, ke wani fa ya dau mace tamkar Mai karamar kwanya ce don haka baki Kai matsayin da zai fada miki wasu sirrinsa ba, sai kiji wani na kiran matarsa Wai dabba ko jaka don rashin sanin kimarta da rainin hankali, amma bai hana ya nemi biyan bukatarsa, bayan haka sukan manta mace dai ta haifesu suke mata isgillancinka bayan Allah ya daukaka darajar martabarta, saboda duk inda namiji ya Kai da mukaminsa, sarauta, jin Kai dole macen yake dawowa.

Uwale tace ai baki ma san wani abu ba, mijina madokine, kina masa laifi komin kankantarsa sai ya jibgeki, shi bai kyautata yadda Allah yace ba, bai baki isashshen abinci ba, ba suturarsa fa sai an bamu kwance nida yara, ya rinka hura hanci yana tafe yana busar iska da shan kamshi sai kace Wanda aka kadawa tambari, dare nayi yaje gashi nan bisa kanki, kina gardamawa ya kile ki yayi abinda yake so, ya barki da tsamin jiki ga yunwa dake kwakularki tunda ba ki ci abinci ya isheki da daren ba, gari na wayewa ki shiga fafutukar nemawa yara kalaci.

Rahima ta kyalkyace da dariya tace “Uwale Kar kisa cikina ciwo don Allah don Allah ki daina maganar mamaci haka, ki yafe masa tunda ma ai kusan lefinki ne, wa yace ki rinka gardama bayan ance idan baki amince ba kuka kwana yana fushi dake mala’ikun rahama tsine miki za suyi, Allah yai fushi dake.”

“Hhmmm Hajiya na sani amma sai aka ce suma kar su kyautata mana su sauke hakkokinmu a kansu, kullum ko wa’azi aka tashi sai dai kiji ana fadin mu mata mu sauke hakkokin mazajenmu, su Kuma su rinka tinkaho suna gadarar aljannar mu na karkashin duga-duginsu, suna takamar tunda ance matarka gonarka ce ka zo mata duk lokacin daka so, ko a saman rakumi ne.”

Rahima ta Kara kyalkyacewa da dariya “Shin Uwale zaki bari mu karya mu kimtsa ko sai kinsa cikina ya cika da dariya tukunna?”
Uwale ta kece da dariya itama “Da takaici ne Hajiya.”.

Tace "Kuma na yarda da batunki, ya dace maza su rinka bamu darajarmu da Allah ya bamu su daina raina hankali da tunaninmu, mu ma muna da kaifin hankali da zurfin tunaninmu, mu ba dabbobi bane mun san ciwon kanmu mun san ya kamata, mun san hakkinmu, mun san nasu, ya dace ace yadda muke kokarin kyautata musu suma su kyautata mana don mu kara ingantuwar zamantakewar aurenmu.

Uwale tace "Hakane wallahi,idan muna kokartawa zamu rinka ganin canji, Allah ya taimakemu.

 Bayan sun kammala kalacin safe, Rahima tayi wanka ta tsala kana ta rinka zagaye sabon gidan nata.

12/09/2020, 22:49 – Anty saliha: ˆRAHIMA ..doc by jami
????????RAHIMA????????
27

Zuwaira ta gyara zama a tsakiyar kawayenta taci gaba da masifa "Ku barni dashi zai dawo ya sameni, tun kafin aje ko'ina ya fara nuna injustice."

Karaf a kunnin Innarta yar mahafiyarta ta kirata gefe ta fara fada “Ni fa ko da ake gaya min kina hulda da kadangarun bariki ban yarda ba sai yau dana gani da idanuna, ashe wayonki ya zan na banza tunda za kiyi sake wadancan shaidanun su rika hure miki kunni bayan duk fushin da iyayenki suka yi dake ko a jikin ki ko?”

Ta turo baki kamar na jaba “To ke Inna baki ga rainin hankalin da yai min bane sai nawa za a gani don na nemi hakkina?”

“Yi min shuru sakaryar banza, har wani hakki Kika ajiye? Ana tarboki kina fandarewa, to wallahi duk Kika bari iyaye suka juya miki baya sai dai ki nemi na bariki da suke zugaki.”

Haka al’amarin ya kasance gareta har aka watse.

A can gidan amarya mutane sai sha daya suka watse sai Maryam data tsaya suyi sallama sai kuwa matar da Hjy Kaltume ta nemo mata ta rinka tayata aikin gida wace yar uwar Mairo ce.

Rahima ta yaba da tsarin gidanta sosai everything looking nice and cute, ta kama hannun ‘yaruwata dake tsaye tana niyyar tafiya tace “Nagode sosai Yaruwa Allah ya bar zumunci….
“Haba kanwata tsakanimu ya zarce haka, Kuma da kike ta wani godiyar gida ba fa ni kadai na tsara ba harda angonki don haka shi ta dace ki yiwa godiya.”

Ta zaro idanu “You don’t really mean that..

Maryam tace “What’s so hard to believe? Mijinki mutum ne mai saukin Kai, ga wanda ya fahimcesa,Nima dane nike masa muguwar shawar but mu’amalar da muka yi na dan lokacin nan na fahimce sa sosai kema zaki fadi more nan gaba.”

Tace “Hhmmm ni ba abinda ke damuna illa yadda zan kallesa a matsayin mijina idan ya dawo, gaskiya ban san abinyi ba.”
Ta kyalkyace da dariya har tana kwalla “Kenan Ni zan fada miki abinda za kiyi? To tunda abin ya zama haka bari ya dawo shi zai sani.”

Tana gama magana tayi gaba ta barta nan, dole ta rufe kofar falonta tunda maigadi ya rufe gate Maryam na tafiya.

Ta leka dakin da Uwale take taga har tayi barci…
Ta shiga bedroom dinta ta shige toilet inda ta sake yin wanka ta dauro alwala, ta fito tayi haramar sallar nafila., tayi adduointa ta kare kana ta haye gado da niyyar samun isashshen barci don wartsake gajiya, amma barci ya gagara, har zuwa karfe ukun dare tana juyi dalilin kekashewar da idanunta suka yi, ba alamun barci ko kadan
Tunanine ya addabeta, to yanzun ita Rahima ta tabbata matar Yaya Haseeb kenan ko, shin akwai wadanda Allah jarabta irinta kuwa? Anya rayuwarta zata taba komawa normal? Yes ta sani kowacce rayuwa da irin kaddarorin da aka rubuta mata, yau kaga fari gobe baki, yanzun yau kaga abinda kake so gobe ka samu kishiyar hakan, yau murna gobe ko jibi akasin hakan ba don komi ba sai don Mahakiccinmu ya gwada karfin imaninmu da kasancewar bawa bai taba dauwama cikin abu guda. To ita a matsayinta na musulma wace ta yarda da kaddara mai kyau ko maras ya zama wajibi a gareta tasa hannu biyu ta rungume ta duk da kasancewarta mace mai rauni.

Tunanin marigayi suka kutso Kai daidai lokacin Wanda ya haddasa gudanar hawayenta suka fara jika pillow, Allahu Akbar! Ta fadi a fili, rahamar Ubangiji ya ni’imta makwancinsa, sunyi rayuwar aure ingantacce duk da sunce zo mu zauna zo mu saba, zamantakewar su abin koyi ne ga ma’aurata, Bata taba tunanin aurensu zai zo karshe da wuri ba, Amma kash! Mai katse dukkan wani hanzarin mutum ta kusanto ta rushe dukkan ginin da suka fara dorawa… To shin yanzun zata iya dora wani tubalin don gina sabon rayuwar aure da Yaya Haseeb? Idan tasan zuciyarta tasa fa? Ya zata iya tarayyan miji da Aunty Zuwaira gashi tun ba a kai ko ina ba ta fara jin sabanun da ya shiga tsakaninsu?
Ta juya gefe guda tace Oh Ya Allah gani gareka, kai ka kaddaro min auren nan , Kai kasan dalili, Ina rokon ka tallafa min tafiyar da al’amarin auren nan nan cikin sauki tareda jagorancin ka.

Bata samu barci ba sai bayan data idar da sallar asubah, ta sureta kenan aka Kira wayarra dake kusa da itaa
Ta dauka ta sallama ido a rufe.

Amsarsa tasa ta bude tangaran..”Ba dai na tashe ki daga barci ba ko?” Ya tambaya bayan amsa mata sallamarta.
Shock ya shigeta faras daya, zuciyarta ta fara ras-ras…
“Are you alright? Ya sake tambayar ta amsa da Kai, nan take ta tuna bai ganinta tace “Komi lafiya.”

“Ban amince ba, your voice is very low what’s wrong.”
“Wallahi ba komi.”
Ya amsa “Hakan dai kika ce, anyi sha’ani lafiya ba wani problem ko”
Rahima tace “Aljamdulillah.”
Is the house ok?”
Ta sake amsawa a natse.

Daga daya bangaren Dr Haseeb ne ke tuhumar  me yasa take bashi short answers,wata zuciya tace baka disconnecting wayar ka huta tunda ba hirar ya kirata suyi ba, a nasa tunanin ma gaisawa kawai za suyi but ya kasa aje wayar ya rasa kalmar fadi Kuma sai kame,-kame.

Ya nisa ya sake tambaya “Ina Abdul? Yana lafiya ko?”
“Yana wajen Unma.”
Yai shiru yana murzan goshinsa da yatsu biyu, ya rasa dalilin kasa aje wayar, dalili ya wuce matsayinta na matarshi da son cika amanar da ya dauka?

Can yaji muryarta tana tambayar “Ya patient?”
Ya amsa “Alhamdulillah, he’s progressing well, nagode.

“Masha Allah
Ubangiji ya bashi lafiya.”
“Ameen bari in barki ku huta zan kiraki gobe Amma idan da abinda kike so ki yiwa Hajiya magana.”.
Tace “Ba wata damuwa insha Allah may be dai inje in dubosu zuwa jibi.”

“A ina kika taba ganin amarya na yawo? Ki bari saina dawo mu tafi tare.”
“Ta amsa shikenan.”
“A shafa min kansa, nagode.
????????RAHIMA????????
28
Ta sauki mintoci heart beat bai koma normal ba, watau a takaice so da kaunar Ya Haseeb na neman mamaye mata ruhinta, ta girgiza Kai wannan ma ai shine abin kunyar, hhmmm da zai fahimci haka ya zai dauketa, maras tunani ko maras matunci? In kuwa hakane gara ta yiwa kanta rigafi ta danne zuciyarta zai fi mata alkhairi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button