NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ba sauran barci a idanunta don haka ta fito daga dakinta ta nufi kicin inda ta taras da Uwale harta kama aikin hada breakfast, tana ganin Rahima ta durkusa ta gaisheta “Hajiya barka da fitowa.”

Ta amsa “Ina kwana Uwale ashe kin tashi tun dazun.”
Tayi dariya “Ai mun saba, a can kauye ina muka ga lokacin barcin safe, muna alla-allah bayan munyi sallah mun karya kummalo da dumammen turo mu zuba hatsi a turmi mu shiga neman na abincin rana mu da yara..

Rahima tace “Gaskiya kuna kokari,kuna wahala, shiyasa akace mutum ta rinka kallon na kasa da Kai, nan zaka gane ni’imar da Allah yai masa sai Kuma ka gode masa don wasu sun fi kane Kai Kuma kafi wasu, amma gaskiya idan kika duba rayuwar matan karkara sunada matukar tausayi, sai muce mu aljanna muke.”

Uwale ta nisa “Ina ma ki kasan haka Hajiya, sai Kinga macen kauye a ce miki sa’arki ce ki yita rantsuwar ba haka bane don ta kusa haihuwarki a fuska, ta tsofe ta komade saboda wahala, hakora sun zube, ba isashshen ingantaccen abinci, ba hutu, na kyakkyawar muhali balle wani sutura mai kyau ga rashin samun kulawa daga mazajenmu, yawanci mazanmu fa basu San darajar mace, iyakar ki dashi ki dafa abinci, wata har noman abincin ma da ita za ayi, kiyi surfe da daka, idan ya bukaceki ya sarrafaki kamar yadda yakewa jakarsa da yake kiwo,idan kin dauki ciki ki babu wani kulawa, wajen haihuwar ma wani a rabu kacar sabida yaushe ya barki Kika je wani asibiti don inganta lafiyarki balle na dan cikin ko jariririn da aka haifa, wasu kuwa don su doki mace ba wani aibu bane a garesu, to mazan nawa ne suka san hakkokin matan da ya rataya a kansu?” Dalili kenan koda mijina ya mutu zawarawa suka yo min caa!! Nace bada Uwale ba, anyi daya ba za a kara na biyu ba, da in zauna cikin jahilci da rashin sanin me auren ya kunsa da rashin sanin hakkokin juna gara in taho birni in nemi sana’a.”

   Rahima ta nemi kujera ta zauna tace "Bari in tayaki aikin mu ci gaba da hirar sai mu karu da juna..

Uwale tace "Ai ke Hajiya Allah ta tarfawa garinki nono, da mata na dacen irin mijinki da ba za suyi kukan komi ba, ko su Mairo da suke 'yan aiki sun shaida balle ku, kin kuwa ji ance kyakkyawar safiya tun daga maraice ake fara ganewa, jumma'ar da zata yi kyau tun laraba ake ganeta, wallahi haka nake son namiji yasan mutuncin 'ya mace.

Rahima tayi dariya “Ai ko mazan namu ana samun wadanda basu San darajar macen ba, da na dauka jahilci ne yasa wasu mazan ke maida matansu tamkar jakuna ashe ba hakan bane, ko a birnin haka wasu mazan suke, kiga namiji bai san mutunci da darajar matansa ba, mace bata isa yai shawara da ita ba, don a ganinsa shirme ne, ke wani fa ya dau mace tamkar Mai karamar kwanya ce don haka baki Kai matsayin da zai fada miki wasu sirrinsa ba, sai kiji wani na kiran matarsa Wai dabba ko jaka don rashin sanin kimarta da rainin hankali, amma bai hana ya nemi biyan bukatarsa, bayan haka sukan manta mace dai ta haifesu suke mata isgillancinka bayan Allah ya daukaka darajar martabarta, saboda duk inda namiji ya Kai da mukaminsa, sarauta, jin Kai dole macen yake dawowa.

Uwale tace ai baki ma san wani abu ba, mijina madokine, kina masa laifi komin kankantarsa sai ya jibgeki, shi bai kyautata yadda Allah yace ba, bai baki isashshen abinci ba, ba suturarsa fa sai an bamu kwance nida yara, ya rinka hura hanci yana tafe yana busar iska da shan kamshi sai kace Wanda aka kadawa tambari, dare nayi yaje gashi nan bisa kanki, kina gardamawa ya kile ki yayi abinda yake so, ya barki da tsamin jiki ga yunwa dake kwakularki tunda ba ki ci abinci ya isheki da daren ba, gari na wayewa ki shiga fafutukar nemawa yara kalaci.

Rahima ta kyalkyace da dariya tace “Uwale Kar kisa cikina ciwo don Allah don Allah ki daina maganar mamaci haka, ki yafe masa tunda ma ai kusan lefinki ne, wa yace ki rinka gardama bayan ance idan baki amince ba kuka kwana yana fushi dake mala’ikun rahama tsine miki za suyi, Allah yai fushi dake.”

“Hhmmm Hajiya na sani amma sai aka ce suma kar su kyautata mana su sauke hakkokinmu a kansu, kullum ko wa’azi aka tashi sai dai kiji ana fadin mu mata mu sauke hakkokin mazajenmu, su Kuma su rinka tinkaho suna gadarar aljannar mu na karkashin duga-duginsu, suna takamar tunda ance matarka gonarka ce ka zo mata duk lokacin daka so, ko a saman rakumi ne.”

Rahima ta Kara kyalkyacewa da dariya “Shin Uwale zaki bari mu karya mu kimtsa ko sai kinsa cikina ya cika da dariya tukunna?”
Uwale ta kece da dariya itama “Da takaici ne Hajiya.”.

Tace "Kuma na yarda da batunki, ya dace maza su rinka bamu darajarmu da Allah ya bamu su daina raina hankali da tunaninmu, mu ma muna da kaifin hankali da zurfin tunaninmu, mu ba dabbobi bane mun san ciwon kanmu mun san ya kamata, mun san hakkinmu, mun san nasu, ya dace ace yadda muke kokarin kyautata musu suma su kyautata mana don mu kara ingantuwar zamantakewar aurenmu.

Uwale tace "Hakane wallahi,idan muna kokartawa zamu rinka ganin canji, Allah ya taimakemu.

 Bayan sun kammala kalacin safe, Rahima tayi wanka ta tsala kana ta rinka zagaye sabon gidan nata.

29

Gidan Rahima sashe-sashi biyu ne sai fili daga can gaba, ginin kansa ya tsaru sosai, ga furanni masu fitar da kamshi daban-daban, tun kafin ta tare saida aka yi mata saukar qur’ani da adduoin neman tsari da albarkar zaman baki daya..
Sun gaisa da maigadin Mai suna Mal. Hassan yayinda dansa Haladu ne zai rinka yi musu wanki da guga da share-sharen waje da gyaran shukoki.

Sha daya amaryar ta fara baki, zuwa azahar sai ga uwargida Zuwaira da tawagarta sun danno mata baya, suna mata kirari "Sai ke uwargidan likitan likitoci..

Tayi musu maraba cikin ladabi, ta gaishesu suka share, tasa Uwale ta kawo musu kayan motsa baki dasu lemu shima ko kallo balle su dandana sai sakin magana suke.

Ba inda Rahima ta burge kowa sai da taki kulasu tayi tamkar bada ita suke maganar ba don ta lura so suke ta tanka su ci mutuncinta, da taga haka maimakon suyi tafiyarsu sai ta mike tace su biyota wai suga cikin gidan, kawayen Zuwaira su bakwai suka bita duu tana gaba suna biye, Saida suka gama zagaye ko’ina kana suka dawo falo ta tsaya a gaban Rahima tace “Miko min key din dakin Dakta sabida Nan ne kadai ban shiga ba.”
Cikin natsuwa Rahima tace “Kin dai shiga inda suka dace ki gani, inda kike batu yanzun kuwa sai ki jira amincewar mai dakin tukunna in ya dawo.”

Kawar Zuwaira Hussaina ta girgiza Kai “Lalle yarinyar nan taga gadon barcinki ta rainaki wallahi.”
Wata cikinsu kuma tace “Ya dace ji nuna mata da gidan da maigidan dyk mallakin kine.”
Tana wani jijjiga jiki kamar Mai shirin hawa bori tace “Ki kiyayeni wallahi, zaki bani ko sai rayuka sun baci tukunna?”

Rahima ta yunkura ta mike tsaye ta bisu da ido tace “Kin ban mamaki Aunty Zuwaira da zaki tsaya kadangarun bariki na hura miki m wuta a gidanki. Da akwai girma da arziki watakila in daure in baki keys that’s in ke kadai ce ma, amma yanzun ba Zan iya ba, kiyi iko da naki gidan inyi da nawa, abu na karshe Ina rokon don Allah ki kwashe tarkacenki gayyar na ayya kuyi gaba. Daga yau idan ba girma da arziki zai kawo ki ba please Kar ki sake zuwa min gida, nagode da ziyara, Kuma a rinka taka tsantsan da duniyar nan tamu mai halin Dan mangwaro, sai kana shansa dadi ya fara tsumaka ya subuce maka, hakan nan ita din rawar ‘yan mata ce, na gaba Kan koma baya…

“Tafdijan! Lalle wuyar yarinyar nan ya isa yanka, to ke Kyaleta za kiyi Zuwaira ta rainaki a gabanmu?”

“Zuwaira ta cika tayi fam tace “Wai ita ‘yar gani lasheni..

Daya kawar tace “Ba ki sharara mata mari ta gane banbancin aya da tsakuwa?”

Kamar go ahead kawai take jira ta daga hannu zata kaiwa Rahima mati, tayi wuf ta rike hannun cikin sa’a tana girgiza kai “No Aunty Zuwaira Kar ki fara, duk haukar da za kiyi zan kyale but Kar kiyi mistake din hannunki ya Kai ga jikina, don ni din Dan hakin daka raina ne, Ina iya tsone idanunki.”

Zuwaira tayi kokarin kwace hannunta ta kasa, kawayen nata na ganin haka suka tasowa Rahima haikan, ta kallesu a wulakance tace “Duk wace ta matso kusa dani sai buzunta.”

    Suna cikin haka tawagar iyalan gidansu Haseeb dana bangaren su Haj. Kaltume suka shigo, kanwar Hjy Kaltume mai suna Hjy Iya ta rafka salati sauran jama'aa suka dauka suma "Me zan gani Rahima?

Ta saki hannun Zuwaira tace "Tambayi Aunty Zuwaira...

Ta juya wajen Zuwairan tace “Ya kike son zubar da girmanki, anyi bukin nan an watse lafiya, meye na tayar da husuma, tunda Allah ya hadaku zaman tare ba sai kuyi hakuri da juna ba, mijinku na can na nema muku abin rufin asiri, ku kuna nan gaban jama’a kuna zubda mutuncinku, ina amfaninsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button