
Zuwaira ta figi gyalenta ba tareda Kara cewa komi tace wa mutanenta “Mu tafi, ai zamu sake dawowa.”
Suna fita mutane suka shiga tseguminsu, Rahima ta katse su "Ni dai ku daina cin namansu din Allah, kuyi musu adduar shiriya idan zaku iya, idan ba zaku iya ba kuyi shiru."
Da dare ne Maryam ta kwaso su Umma, da goggo Lauratu matar mahaifin Rahima din dasu Abdul suka taho gidan amarya.
Bayan sun gama gaisawa iyayenta suka ci gaba da yi mata nasihohi domin ko da yake ita din ba yarinya bace, ba aurenta na farko bane iya yar Adam ce ajiza, wani da gangar yakan kauce hanya ya bi son zuciyarsa, dalili kenan da yasa ake son manya su rinka nasihohi da fadakarwa tareda jan hankali domin gyara.
Maryam ce ta dauko batun su Zuwaira, Umma tace ke dai bari duk magana ta karade a Yakasai Wai tayi hayar yan daba su taho su baki Kashi.”
Rahima tayi murmushi “Gaskiya surutun mutane ne ‘yan sa ido da tsegumi, ko ba ayi abu a gabansu ba zasu ce sunji sun gani.”
Maryam taja tsaki "To ai ita Zuwairan tasan haka, yau mitum ake kiwo ba dabba ba, me yasa ta kwaso 'yan bariki ta kawo gidanki har suci miki mutunci, hhmmm Allah ya tsare da nice wallahi da anyi kare jini biri jini, gobe ko anzo ance ta taho sai tayi fargabar dumfarata."
Umma ta harareta ta kalli goggo "Kinji fa, maimakon taba 'yaruwarta hakuri sai Kara tunzura take, ni ban San ranar da za kiyi hankali ba, haihuwa uku."
Goggo ta bushe da dariya "Ai ba rashin hankali bane, koni da tsufana ba zan kyalesu irin yadda Rahimar tayi ba, ai ko bata mareni ba sauna sharara mata tafi don kunyar jin maras kunya asara ce."
Maryam tace "Musamman ga wadanda basu san mutuncin kansu ba balle na wani."
Umma ta kada Kai ” Yadda tayi yayi daidai Kuma nagode, baku see ba a biyewa mahaukaci ba, ka Kan koma gefe ne kayita kallonsa yana shirmensa idan ka biye masa kuwa sai ku haukace gaba daya… Rahima tace “Nima shiyasa naki biye mata muyi fadan Kuma ta gane ba zan dauki rainin wayo ba kowacce tasan matsayinta.”
“Nagode hakan Nike so ki ci gaba da hakuri komi mai wucewa ne ” Cewar Ummansu .
Maryam taja Rahima daki tace “Yaya ya kira waya?
“Tunda safe.” Ta amsa a takaice..
Maryam tace “Da kyau Daman shi na kosa inji.”
Rahima ta tabe baki “Da baki ji ba fa sai Yaya?”
“Sai yaya kuwa illa nasan kanwar tawa zata damu ance an daura aure ango na can wata usa duniya, amarya ta kwana ta yini cikin gidansa ace ba kiji muryarsa ba, fita hayyacinki za kiyi sabida mutumin nan ne fa….
Ta harareta “Bari don Allah ban son kuna tuna min wancan zancen ya wuce.”
“Ni kuwa nace yanzun aka fara Amma na bar maganar.”
Sai tafiyarsu wajen goma na dare suka sami hutu ita da Uwale wace ta fara gyangyadi, Rahima tace taje ta kwanta, ita Kuma ta shiga toilet ta watsa ruwa, ta gabatar da nafilolin data saba kana ta haye gado, tana kwanciya aka Kira m waya, ta dauka cikin dariya “Haba Maryam nace miki zancen nan ya wuce ko ..
“Wane zance kenan?
Muryar Daktan ke tambayarta.Duk da cewa ba ganin fuskarsa take ba kunyarsa ta rufeta ta kasa magana for some seconds.
Jin tayi shiru yace “Ko kin kife wayar ce?”
Ta girgiza kai “Ah ah, da kace sai gobe zaka Kira…
Yayi dan murmushinsa “Just want to say goodnight, ko nayi laifi?”
Tayi saurin fadin “Ah ah ba haka bane.”
Wayar tasu kamar ta safe, babu wani kwakwkwaran magans, itama sai inda-inda sai kace saurayi da budurwar da suka kamu da son juna bayyana yai musu wuya.
Suka aje wayat kowa da tunanin danuwa.
13/09/2020, 13:28 – Anty saliha:¦ˆRAHIMA..doc by jami
30
Kwanan Dakta biyar a kasar Riyadh ya kira waya cewan yana kan hanyar dawowa. Cikin kwanakin Rahima zata kira sarakuwarta su gaisa kana wajibi ne taci duk kalar abincin da ta girka don sanin muhimmancin ta.
An kawo Abdul ya kwana biyu yaki zama aka maida shi inda ya saba, baki na ci gaba da zuwa ganin amarya, wasu collegues dinta, wasu ‘yanuwanta dana angon, Hayatu ma zuwansa uku, yace wai yana debe mata kewar Yayansa ne, ya maisheta aunty Rahima yanzun duk da ta nuna bata so yace ina ai mukaminta yanzun yafi gaban a kira sunanta gaba gadi.
Wani lokacin idan Hayatu ya zauna yana abubuwansa yakan rinka tuno mata da marigayi, saboda suna kama sosai, barkwanci yanayin son jama'arsu daya ba irin Yaya Haseeb ba. Taf! Shi wa yaga fuskar ma balle hakoransa da sunan dariya, gaskiya ko da take miskila, nashi ginshirar ya shafe nata.
A ranar ta shidda da likitan zai dawo tunda suka idar da sallar asubah suka fara shirin tarbon ango. Sun shirya abinci da drinks (natural) kala-kala.
Suna cikin aiki Uwale ta tsaya tace “Wai shin Hajiya in tambayeki mana, Kuma ba shishshigi nike son yi miki ba, kin kuwa shirya tarbon maigidan?
Ta kalleta “Ban da wannan hidimar da muke yi, akwai nau’in abincin karkara da zaki nuna min a dafa masa ne?”
Tace "Hajiya nifa ba abinci nike nufi ba, ina batun gyarane?"
Rahima ta sake fadin “Kinada Mai ko turare mai kamshi ne ki bani?”
Uwale ta dafe kai “Wai ni Allah Hajiya duk basu nike nufi ba, Sai dai Ina jin kunyarki amma tunda ya zama dole bari inyi miki bayani.. Shin kina ci ko shan ‘yan abubuwan nan masu gyara mace? Misali mu mutanen kauye muna cin furen zogale, shan kindirmo, madara, kankana, aya rake da gwanda, to Kuma naga matan birnin ma suna irin nasu”
Rahima tace “Me yasa kika yi min tambayar nan?”
“Kaji Hajiya! Maigida irin Alhaji? Ni dai ga gudumuwata can na aika an kawo miki, sauran bayanin gaskiya da ‘yar kunya tsakaninmu.”
“Hhmmm inda da kunyar da baki yi min zancen nan ba Uwale, amma nagode da kokari, mu ci gaba da aiki duk da bai Fadi lokacin isowarsa ba.”
Sai da suka gama gyara dakinta da cikin gidan tsaf sannan ta shiga dakin da aka shiryawa Daktan ta share ko'ina ta kara gogewa duk da daman ba datti a dakin tunda komi sabo ne. Air freshners kala-uku ta fesa a dakin bayan turaren wuta, dakin ya dau kamshi, ta koma falonsa nan ma hakan tayi, gidan gaba daya ya dau kamshi mai sa natsuwa da kwanciyar hankali.
Zuwa la'asar tana zaune a falonta ta barbaje littafan da Maryam ta kawo Mata, iya kwakwan son karatunta ta kasa karanta ko da shafi dayane cikin kowanne littafi dalili da ta kasa natsuwa, sai wani fargaba da tsoro da taji motsi, har karar waya ta rinka imagining tana ji a kunnenta. Hhmmm! Kar dai Ya Haseeb ya sata zautuwa...
Shiru bai iso ba bai Kira waya ba har bayan la’asar don haka ta sakankance ya fasa dawowa a ranar.
Ta tashi ta canza doguwar rigar data sanya a jikinta ta saka wani simple sky blue, dinkin buba, ta saka silver earrings da chain dinsu hadi da bracelet da wrist watch water proof hade da zobenda data sanya a yatsunta na dama, yatsun hannu hagunta ta saka gold rings guda biyu madaidaita.
Banda kamshin man enchanteur (stick deodarant) data shafa a armpits dinta, ta kara anti- perspirant deodarant, ta kara fesa perfume (Adorable) sai kamshi duk inda ta gilma.
Dr Haseeb Junaid ya kalli rolex din dake daure a hannunsa da lallausar suma suka bi suka kwanta ya gama shirunsa tsaf ya juya ya kalli Zuwaira dake zaune gefen gado yace "Ni zan tafi ba wani abu?"
Ta kallesa ta watsar bata tanka ba.
Yai ajiyar zuciya ya mike tsam ya nufi kofa kafin ya isa ta rigashi ta taresa “Kana nufin can Dorayi zaka tafi yanzun ka kwana can?”
Ya kura mata ido ta cikin glass dinsa yace “Me kike so inyi miki ne Zuwaira,tunda na shigo gidan nan kike neman ffitina, me kike so?”
Ta Kara tare kofa “Me nake so? Ya za kayi min wannan shegiyar tambayar bayan wani gida kayi niyyar tafiya ka kwana, bani da right da zan tuhumeka?”
Ya girgiza Kai “Ki tuhumeni for what reason? Look Zuwaira ki gane addini yaba magidanci damar sauka duk inda yaso in ya dawo daga tafiya in har ya mallaki mace fiye da daya, amma ga mai son kyautatawa sai ya sauka wajen uwargidansa ko wace take da girki a ranar, a al’adance. To ke na kyautata miki, na dawo na sauka a nan,tsawon lokacin dana dauka tare dake kika nuna tamkar baki san daga inda na fito ba, babu maraban arziki balle nuna jin dadi da hamdallah ga Allah cewan naje na dawo lafiya, banyi fushi ba na zauna tare dake har zuwa yanzun duba time karfe nawa ne, sai kuma zan fita ki taso ki dasa min wasu tambayoyin da basu dace ba? Me ma kike nufin da wai can zan kwana? To yes can zan kwana, idan kin manta ne in tuna miki yanzu ku biyu na mallaka matsayin mata ne, hakkin Rahima ma ya rayata a kaina yadda naki hakkin yake a kaina, wajibi ne in sauke nauyin da Allsh ya dora min nata, tunda an daura ba na Nan, kwana uku zanyi a gidanta, kana in dawo ku ci gaba da raba kwana yadda kuke so wace ban kwana gidanta ba wajibi in lekata da safe don ganin lafiyarta, Ina fatar kin fahimceni, bani hanya in wuce.”
Wai saita saka kukan kissa ta kama shi gam ta rike “Sabida Allah nu kadai zaka barni in kwana cikin katon gidan nan?”
Ya girgiza Kai “Yau aka fara hakan? Idan ban barki kin kwana ke kadai ba ai ke kya barni ki tafi balaguronki ko, to meye na damuwa yau keda kike alla-alla ki samu kafar yawo?”
Taci gaba da kuka wanda a zahiri tana yine don bata masa lokaci, ya dago manufarta, ya yakiceta ya raba daga gefenta ya fita, ta bisa har waje yayinda direbansa ya taso ya bude masa mota, yace Mata “Saida safe.” Ya shige mota abinsa suka tafi.
13/09/2020, 23:21 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by jami
31
Mal. Hassan ya dagewa direba murfin gate ya wuce harabar da aka tanada domin aje motocin.
Uwale ce ta fara hango Maigidan ta tagar kicin yana gaisawa dasu Mal. Hassan bayan fitowarsa daga mota, direban ya bude boot yana fito da kayan dake ciki suka fara shiga dasu cikin gida.