NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

 Rahima na can cikin bedroom dinta bata San bidirin da ake yi ba, kwance take rigingine ta kifa littafin da tsananin tunani ya hana mata karantawa a fuskarta kamar tana barci, zurfin tunanin da take yi ya hana jin sallamar da Dr Haseeb yayi.

Ya dauka barci take ya Kara sallama har sau uku bata motsa ba, ya matsa ya shiga cikin dakin, taushin rug din ya hana mata jin takunsa, saida ya kai daf da gadon da take kwance, yaji sautin wata waka dake fita a wayarta, ta wasu samari da su Kai masa suna I don’t care who you’re
Ya tsaya bisa kanta yai mata kallon tsaf cikin dakikoki……

Jikinta ya bata lalle ana kallonta, daidai lokacin ya duka ya kai hannunsa ya cire book din data kare fuskarta, daidai lokacin suka shaki kamshin juna, Rahima ta kai hannunta zata cire book din, already nasa hannun ya sauka a kafadarta. Ganin wanda yake tsaye kanta ta yunkuro ta tashi zaune a tsorace.
Ba tareda yayi magana ba ya maidata kwance ganin yadda ta razana, tana ta kokarin fahimtar what’s happening is real ba mafarki ne ba, tayi kokarin magana but shock ya hanata, shima a kidime yake don da za a auna jininsa a lokacin za a ga ya hau saboda bugun da zuciyarsa keyi very fast. Ya gyara muryar da zama very low yace “Sorry I didn’t mean to scare you.’

Ta saki ajiyar zuciya yayinda ta sake yunkurin tashi ta zamo kafafunta yaja da baya kadan still yana kallonta, ta cije tace “Sannu da zuwa, afwaan ban ji shigowarka ba, ya hanya?”

Ya amsa “Alhamdulillah ya gida? Idanuwansa na kanta ya lura da kananan kitson da aka tsarawa sumanta da suka sauka har bayan keyarta kafin ta lalubi dankwalinta ta rufe kanta.
Yana tsaye yana ci gaba da yi mata kallon kurilla harta mike ta gyara rigarta ta lalubi mayafi ta rufa kana ta fara kame-kame tace “Abinci na can dining ko sai kayi Sallah ka huta tukunna?”

Ya bi da kallo ya share tambayar bai amsa ba saboda ya fahimci so tayi ya juya ya bar badroom din shi Kuma kamshin dake fita a hankali ya haifar masa da wani irin natsuwar da yasa yaji yana son zama cikinsa.
Amma tunda yaga a rude take, bari ya hakura har ta samu natsuwa. Ya kalleta “Zan shiga dakina for now inada wasu calls before magrib.”

Rahima ta nufi kicin ta taradda Uwale da Haladu nata shirya kayayakin da ya taho dasu, sun aje komi a mazaunin da ya dace, suna gamawa Uwalen tace “Hajiya zamu sake dafa wani abincin ne?”
Ta kada Kai “Ah wadanda muka yi suna cikin warmers ai ba abinda suka yi.”

“To ke fa? Naga kina son tuwo har na dora ruwan zafi?”

Ta girgiza Kai “Ba Zan ci ba gaskiya sai dai ko ke, amma nagode da kokari.”

Uwale ta dafa cikinta "Ai nima din a koshen nike alhamdulillah."

Rahima tace Shikenan “Zan shiga inyi sallar magrib sai anjima kenan.”

Ta bude baki “Saida safe dai Hajiya, maigida ya dawo wane hira za muyi yau?”

Ta girgiza Kai “Uwale kina son shige mun hanci amma zan fyato ki.”

Tayi saurin durkusawa “Wace Ni uwar dakina, yafe min, amma kinsan gaskiya na Fadi.”

Ta shiga tana dariya “Hhhmm naso in ganki da kuriyarki Uwale, kin cika ban dariya.

Wasu masu shigowa gidan Rahima suna korafin wai tana sakewa da ‘yar aikinta da yawa, ita kuwa mace ce mai ba kowanne irin mutum darajarsa, ta Kan dauki kanta ita ba wata tsiya bace, bata wulakanta na kasa da ita saboda sanin kowacce halitta da irin darajar da Allah yai Mata, tsakaninta da masu aikin gidanta,, mutunci ne da girmama juna.

Ta dade da idar da sallar isha’i amma ta kasa tashi daga sallayarta.

Kamar yadda yaji kamshin dakinta hakan ya cika nashi dakin tun daga falonsa zuwa bedroom, komi ya Burgesa, tsarin yai masa daidai. Hhhmmm ya kasa zama sai tunani, shi bai ma san yadda zai bullowa wannan auren nasu ba duk da ya rungumi auren nan da hannu biyu. To ai ba nan gizo ke sakar ba, ganin irin dari-darin da ta fara yi dashi, to ai shi din ma bai saki jiki da ita ba although ya tabbatar da zasu gina rayuwar aurensu kan kyakkyawan kudiri saboda ya amince da ita duk da babu wata akaka ta soyayya tsakaninsu.
Ya ji shuru bata fito ba, ya dau waya ya kirata cewan yana son ganinta a falonsa, kafin ta fito ya kagu da son sake ganinta da tsarin kwalliyarta, tayi masa kwarjini kwarai a fuskarsa.
Bata fito ba saida ta saka hijab, ta isko shi tsaye gaban aquarium ya gama baiwa kifayen dake ciki abinci, ta danyi murmushi, ashe ra’ayinsu ma dayane wajen kaunar kiwon kifaye..
Bayan ya amsa sallamarta ba tare daya dago ya kalleta ba yace “Zauna mana.”
A natse ta zauna a takure tana kara yaba tsarin falon likitan, idanunta suka Kai kan babban hotonsa dake manne a bango da hoton tsohon shugaban kasa Sani Abacha.

Shima din yazo ya zauna kujerar dake fuskantar ta yana kallonta ta kauda Kai, ya sauke ajiyar zuciya “Kin san illar tunani kuwa?” Ya tambayeta
“Tunani yin kansa ya keyi ai balle Kuma idan mutum nada reason na yi din.”

Yace “Hakane, but na Kira kine muci abinci.”
“Ni na koshi gaskiya.”
Ya ci gaba da kallonta kanta a kasa dai ya ce “Ya za muyi kenan, bana cin abinci Ni kadai Kuma Ina jin yunwa ke Kuma kin koshi a cewarki, in hakura kenan?”

Tana jin haka ta dago suka hada ido, zuciyarta ta buga da karfi saboda tun saninta dashi bata taba ganinsa ba glass ba, da ya cire sai ta fahimci yafi kyau da kwarjini, his gazing eyes sai haske suke yayinda yake kallonta….

Ta lumshe nata idanun ta budesu da kyar tamkar Mai shirin yin barci, Daktan yaji tsigar jikinsa ya tashi, shawa’awar amaryarsa ya diran masa a kahon zucci Wanda yasa ya manta da matsayinta na da can sai matsayin matarsa.

Cikin rashin kuzari dalilin kasalar data taso ta lullubeta ta mike a hankali ta nufi dining table ta kwaso warmers din data jera ta maido su gabansa ta ajiye a bisa carpet kana tace “Ina rokon arziki ka sauko kaci komi kankantarsa. karka kwana da yunwa.”

“Bana magana biyu Rahima, as long as ba za muci tare ba na hakura.”

Ba yadda zata yi dole ta sauka ta zuba musu abincin a plate guda bisa umurninsa. Tafdijan ita bata taba cin abinci da namiji plate daya ba, ko Rabiu kuwa, dole haka ta daure cikin jin nauyi ta rinka tsakalar abincin, shima ba wani ci yayi ba sai uban nacin kallonta da yake duk ta tsargu kamar ta tashi da gudu ta bar falon.
14/09/2020, 17:50 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami

  1. A takaice tare suka ci abincin suka gama ya tayata kwashe kayan zuwa kicin, niyyarta ta shige daki ta kwanta yace yana son magana da ita..
    Suka koma falon suka zauna, tsawon lokaci bai ce komi ba, shi fa problem dinsa kenan, banbancin su day Rabiu karara ne yaushe shi zai tsaya yana jan aji kafin yai magana? Duk kokakarinta na avoiding tunanin Rabiu yaci tura. To wai me zai gaya mata nema yake wani shan kamshi kafin ya furta?
    Ta rinka motsi da kafafunta don ya gane ta matsu bai kula ba. Ita bata taba ganin mai kyuyar magana kamarsa ba, ashe kuwa za ayi zaman kurame, don idan takamarsa miskillanci gidan ya taras. Shin ko nauyin abinda zai fadin yake? Zuciyarta ta bada dam! Ba dai yana tunanin irin kusancinta da marigayi ya kasance tsakaninsu ba. Tafdijan!
    Aiki jawur!! Tunanin hakan ya haifar mata da damuwa maras misali, hawayen data rinka kokarin dannewa suka kubce suka fara gangarowa,sheshshekar kukanta ya zaburar da shi daga duniyar tunanin da ya tafi, nan take zuciyarsa ta shiga kuna don ya fahimci zubar hawayenta bai rasa nasaba da halinda suka tsinci kansu a ciki na Mata da Miji wanda iya dakewan mutum sai ya bara.
    Sai dai shi ya daukarwa kansa alkawarin rike Rahima da danta bisa amanar da kaninsa ya damka masa, yayi saurin ciro white hankerchief cikin aljihunsa ya share kwallar da suka ciko masa, ya zabura ya mike ya nufi fridge ya bude ya dauko fresh milk ya tsiyaya a 2 cups ya matsa kusa da ita ya mike mata 1cup “Sha madara ya sanyaya miki zuciya.” Ta karba ta kurba sanyin ya ratsa makoshi ya shiga cikinta, ta rumtse ido ta bude sannan ta sake kurba kadan ta rike sauran a hannunta…
    “Rahima ya kira so, softly,. kamar ta cikin kunninta ya rada mata sunan har tsigar jikinta na tashi, ta kasa amsawa, ya sake Kira ta daga masa Kai alamun tana jinsa…tausayinta ya kamashi yayinda yaci gaba da magana kamar yanayi da karamar yarinya “Don Allah ki daina kukan nan, i hate to see a woman crying. Ina rokon ki kwantar da hankalinki kan al’amarin nan da Allah ya kaddaro mana, ba da yin mu bane, rubutaccen al’amarine Ubangiji ya kutso da hikimarsa ta wajen Hajiya, mu Kuma muka yi mata biyayya don bamu isa mu kauce abinda yai nufi a garemu ba, don haka hakuri da tawal’u ya dace muyi da duk wani tunani da ba zai haifar mana da komi ba illa damuwa. Nasihar sa ya shigeta sosai ya haifar mata da karin fitar hawayenta, ya kalleta “Oh my God! Ya furta cike da damuwa yayinda ya taso da hanzari ya iso gareta, ya mika hannu tamkar zai rugumota, ya taka burki yayi reverse tareda girgiza kai ya shiga yawo a falon yana ci gaba da rarrashin ta.

Kamar yana Kara mata volume, cikin kukan tace “Nasan kaddara ce amma wallahi na kasa daurewa…

Yayi saurin dakatar da ita “Karki bari bacin rai yasa ki kauce hanya ki kai ga sabo please, tunda har kin amince a barta a haka mu ci gaba da adduoin Allah ya yaye mana kuncin dake tattare damu, ya karemu daga dukkan sharri ya kuma tabbatar mana da alkhairin dake cikin aurenmu.”

“Ameen ya Hayyu ya Qayyum.” Ta amsa murya can kasa
Yayi dan murmushi yace “Nagode and in Sha Allah nayi miki alkawarin you’ll never regret this marriage, yanzun kije ki kwanta ki huta kin sha aiki yau, gobe in Sha Allah zan daukeki muje gidan Zuwaira mu dauketa muje wajen Hajiya, in lokaci bai kure ba mu wuce har wajen su Umma da rijiyar Lemu da Galadanci.”
Tace “Duk yadda ka tsara hakan za ayi.”
Yace “Ki dai yi tunani, oh sorry na hanani dukkan wani tunanin da zai saki kuka, no more tears.”

Ta amsa “Zanyi kokarin daukar shawararka, nagode.”
“Ni ne da godiya ai, sai da safe kenan.” Ya amsa mata wannan karon fuska a sake.

Tace “Allah ya tashemu lafiya. Nan ta barshi tsaye ta wuce dakinta.
Maimakon su kwanta kamar sun hada baki, kowanne daura alwala yayi cikin daki suka fara jera nafiloli da adduoin samun ingantacciyar rayuwar auren da tsabtatacciyar soyayya, kowanne yaiwa marigayi adduar samun rahamar Ubangiji sannan kowa ya kwanta barci.
14/09/2020, 17:51 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button