NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

  1. Sun tashi cikin farin ciki da annashuwa tamkar basu suka kwanta cikin kunci da damuwa daren jiya ba. Bayan ta gama azkhar dinta ne ta nufi kicin domin hadawa maigida abincin kalacinsa da hannunta musamman da ya kasance tun suna gida ita mai sha’awar girke,-girke ce har sukanyi gardama da Maryam da ta kance Mai aiki zata rinka barin wa aikin komi saboda mene amfanin ajiyeta to in ba domin mace ta huta ba? Ta Kan cewa Maryam mene amfanina idan ba zan shiga kicin in dafawa rabin raina abincinsa ba bayan ko turawa na fadin the way to a man’s heart is through his stomach? Can Kuma ta tambayi kanta to ita so take ta shiga zuciyar Ya Haseeb ko kuwa shine rabin ran nata?
    Kafin ta shiga laluben amsa Uwale ta shigo ta rike baki”Me kuma zan gani Hajiya, don Allah ki fito ki barni inyi aikina.”

Ta juyo “Mun tashi lafiya Uwale? Ina hadawa Dakta abincinsa ne, ke sai kici gaba da namu dana baki.”
Tayi kasake alamun bata ji dadi ba.
Rahima tayi dariya “Saki fuskarki Uwale, ba fa na shiga aikin ki bane, bana Raina kokarinki bane, ladan nike kwadayi, bayan haka ban son in zama irinsu Mamin Sahabi na cikin littafin Anti Bilki Mai suna ‘yayan hutu’ Kinga dole in zage damtse in kwato zuciyar mijina hanyar da addininmu ya yarda dashi.
Uwale ta gyada Kai “Yanzun na fahimceki Hajiya, watau dai zaki Kar tsuntsu biyu da dutse daya, ga ladar da zaki samu wajen Allah don faranta ran maigida ga Kara samun matsayi a zuciyarsa, hakika iya girki na daya daga cikin abinda ke karawa mace martaba a idon maigidanta.”
“Yauwa kin gande kenan. Ai da kinji labarin yarinyar nan sai takaici ya kamaki kinyi Allah wadarai, bata iya dafa komi ba sai ruwan dumi, miji ya jibgo cefane amma ba katabus, ko da yake sakayar uwa aka samu da bata dage wajen nunawa diyarta yadda ake hidimar gidan aure ba.”..

Uwale ta marairaice “Kaico an kuwa tafka asara, to Ni yaushe zan fahimci labarin nan, sai dai ko in Zaki taimaka ki karanta min Hajiya.”

Rahima tace “Ba damuwa….
“Amma Ina fatan ba yau ko gobe za ayi wannan karatun ba ko Uwale?”

Muryar Haseeb da suka ji ba tsammani yasa suka yi tsit, sannan Uwale tayi karfin halin durkusawa ta gaisheshi cikin ladabi, ya amsa yana murmushi kana ya kalli Rahima “Me ake girkawane gidan ya cika da kamshi gashi har na kasa daurewa na biyo?”

Cikin jin nauyi tace “Yi hakuri, Uwale ce ta tsareni da surutu amma gani nan na kusa hadawa.”

Ya juyo wajen Uwale “Haka za muyi dake? Ashe kina Shirin komawa kauye.”
Duk da tasan wasa yake tayi saurin durkusawa “Tuba nike ranka ya dade ayi min afwaa.”

Ya kalli Rahima yana murmushin da ya kashe mata jiki “Sai in uwar dakinki ta amince.”

Tace “Na amince.” Tana kallon Uwale tana dariya a fakaice.
Ya juya ciki “Ba komi, but kuyi ku kare kinsan zamu fita.”

Yana wucewa Uwale ta dafe kirji ta nisa “Allah ya tsare, yau da mutanen kauye sunyi bakuwa.”

Rahima tace ” Wasa ce yake kin sani ai kinzo kenan shiga sojar baddakare, gashi naga alamun Mal. Hassan ya shiga cikin zauwarawa.”
Ta kama baki “Lah! Inji wa?”
Tace ,” In jini Mana, kinsan yanzun mutum ake kiwo ba dabba ba, Kuma kuna karkashina wajibi a gareni in sa ido inga yadda kuke gudanar da harkokinku inda yake da gyara a gyara ko da duk Kun girmeni, amma ku din amana ne a karkashinmu.”
Uwale ta jinjina “Tabbas a Kan Sami karamin da yafi wani babban kaifin hankali da hangen nesa, kina daya daga cikinsu Hajiya, gaskiya kika Fadi ya nuna ra’ayi nace sai nayi nazari shiyasa ban Kai ka shaida miki ba Uwardakina.”
Rahima tace “To ai auren shine darajarmu Uwale, Allah ya tabbatar da alkhairi.”

Karfe tara daidai na safe sun gama shiryawa. Dakta Haseeb ya fito cikin wata rantsatstsiyar shadda yar ubansu wace ake kira senators shadda amma Kuma an rinata ta fito kala biyu, ruwan danyen haki ne da gwaiduwar kwai, dinkin tazarce kamar ko yaushe sai maski take tana shining, ga wani kamshin turaren manya irin na kasaitattun mazan da suka amsa sunansu..
Rahima ta fito ta kallesa sai guda ta sadda kanta kasa saboda duk da ta saba ganinsa cikin irin yanayin, shigar yau ya Kara kwarjini da muhibba, a daya bangaren shima kallonta yake yana yaba tsarin shigarta, babban abinda ya burgesa ta bashi sha’awa shine les din data saka kalar gwaiduwar kwai ne, lapayya data nannade jikinta combination ne na deep green and yolk colours again, sai ya zama tamkar anko suka yi, takalman data saka kafafunta basu cika tsawo ba kuma ba flat bane, hade da yar karamar jakarsu an rubuta musu suna sweet heart
Bai iya tantance sauran accessories din data saka saboda jikinta rufe yake ruf, gashi duk da bata fesa turare a jikinta ba, tana matsawa kusa dashi yaji wani mayataccen kamshi na fita daga jikinta.
Murya a dushe yace “Mu je ko?”
Suka yi sallama dasu Uwale suka fita.

Motar da ya dauko yau jeep ce, Rahima ta kame a gaba yana tuki a hankali suna hira jefi-jefi har suka isa Galadanci.

Bayan sun gaisa da maigadinsa again suka shiga ciki, kofar falon Zuwaira a garkame yake, ya tsaya ya danna karaurawa, shiru har ya koma buga kofar ba a zo an bude ba, yasan kuma tana gidan don ga motarta nan a harabar aje motocin,moreover ma tasan da zuwansa din, takaici ya cika yasa hannu ya fara dukan kofar kamar zai balleta da karfin tsiya sannan aka bude.

Kishi! Kishi!! Ya turnuko Zuwaira ganin Haseeb da Rahima. Wani kololon bakin ciki ya tokare mata wuya,  bata taba zaton irin haka zata ji idan taga mijinta da wata ba, ashe fa aiki na baya she made a big mistake data bari akayi auren Nan( kunji jahila sai kace ita keda ikon sawa ayi ko hanawa) Kuma har a da tana ganin zata iya rabuwa da miji irin nata ba tareda abin ya dameta ba, amma Ina! Ta canza salon rawar domin kidar ma ta canza. Tana son mijinta ba Kuma zata iya hakura ta barwa wannan Mai auren cin amanar shi  ba? To wane mataki zata dauka yanzun? Sai dammarar kwato sa da karfin tsiya ko da masifa da bala'i, don Allah dubi abin takaici har yana wani dressing  kala daya da ita,taja wani dogon tsaki ta juya bata amsa sallamarsu ba balle tayi musu maraba har ma ace ga wurin zama.

Ya bita da kallo yace “Zuwaira haka Allah yace ki yiwa bakin ka?”
Ta juyo a fusace “Yanzu Kai ko kunya ma baka ji na ka taso tsohuwar matar kaninka da sunan Wai matarka”

Ya amsa “Ai ba wai matata ce saboda ba ke kadai zaki bada shaidan hakan ba har dimbin jama’ar da suka halarci daurin aurenmu, zaki zauna ku gaisa ko ah ah?”

Ta sake buga wata shegiyar tsaki tana harare-harare, ta zauna kan hannun kujera tana kada kafa.
Rahima sai kallonta take, a da can inda aka fito ta rinka girmamata a matsayinta na matar wan mijinta duk da cewan ba ta girmeta da wasu shekaru ne sosai ba sai girman jiki data fita sosai. A yanzun ma dole ta ci gaba da girmamata a matsayinta na uwargidan mijinta. Yes dole ne Aunty Zuwaira taji ciwon auren nan, dole tayi kishin mijinta, dole ta tsaneta to amma ita ya ta iya da ikon Rabbana? Da itace Zuwaira ba zata yi wani shirme da zai kawo raini tsakaninsu ba, idan ma kishin ne za tayi na ‘yan birni irin kishin matan da suka san kansu.

Ta zamo daga kan kujera ta rusuna “Aunty barka da kwana, ya kwanan su Khalifa?”
Ta galla mata harara tace “Ke Kinga idan kina son kanki da arziki karki sake yi min magana saboda kin zama baka Mai bakar aniya, ki auri kani ki dawo ki aure was ko kunya ba kiji ba. Yanzun ke kinyi abinda ya dace kenan? Idan namiji bai san yakamata ba ke baki san ciwon kanki bane da kika amince masa kuna raba abin Fadi a gari?”

Rahima ta dake “Aunty kina da damar fadin abinda kika ga dama don anyi miki laifi, Ni Kuma da kika gani na dauki kaddarar da bani na shiryowa kaina ba, tunda haka Allah ya tsara, haka yake son ganinmu, mun bi umurninsa, na rungumi mijina da hannu biyu, sai dai kiyi hakuri kema ki rungumi kaddarar.”

 "Ba laifinki bane inji Zuwaira da take ta sakar mata harara, duk cin mutuncin da kika yi min sayo min aka yi aka zube cikin gidana, sai dai Ina gargadinki da abu days karki sake ki shiga harkata kota yarana, idan kika yi min shishshigin da kike yiwa danginsu Dakta ranki zai baci ki gwammace ba ki amince kinyi tarayyar miji dani Zuwaira ba."

Haseeb ya gyara murya da yaga zata wuce gona da iri yace “Ba surutu ya kawo mu ba, idan keep n shirya ki taho mu tafi Yakasai.”

Ta kallesa a wulakance “Ban shirya ba, kaje na iskoka can.”

Ya fusata ya mike yace “Yanzun nan nayi niyyar mu tafi tare ko kin shirya ko baki shirya ba, karki maisheni mutumin banza, inace gudun haka yasa na kiraki a waya na shaida miki tun jiya?”
Ta tashi fuu ta wuce cikin bedroom yai kamar ya kyale sai Kuma ya kalli Rahima yace “Excuse me.” Ya bita ciki.

Tsaye ya iskota tana wani jijjiga tana tsuma wai ita masifa na cinta, yai sallama ya shiga duk da bata amsa ba. Ya tsaya a bayanta cikin wata masifaffiyar sansanyar murya yace “Zuwaira kiyi hankali dani, duk abubuwan da kike yi ba za suyi komi dani ba, kin san Ni, kin San halina, idan Kika sake Kika kureni ke za kiyi dana sanin da baida amfani, na kawo yarinyar nan ki zauna ku gaisa ku fahimci juna abu ya gagara, Rahimar wata ce da baki sani ba? Kina ganin shirmenki zaisa ta ga kimarki ta girmamaki? ke ganinki wannan haukar da kike wace bata da maganin daya wuce hakuri ne mafita a gareki?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button