
To ki sani idan muka fita muka je gidan Hajiya, ko gidanku ko nasu Rahima kika kika ki kama kanki za kiyi mamakin matakin da zan dauka a kanki, and yanzun na baki only 5minutes ki shirya ki fito ko ranki ya baci.”
Yana gama maganganunsa ya fita. Ta tsaya tayi shiru na yan dakikoki kafin ta zabura ta fara Shirin dole domin tabbas tasan halinsa, zai iya Kyaleta tayi masa duk cin kashin da zata yi amma duk ranar data kai shi makura sai ya juye mata ta rasa gane kansa, duk iya kissa da dabarar ta bs zata ciwo kansa ba sai ya gaji ya sauka don kansa.
Sannan wani abin takaici sannu cikin ruwan sanyi yake gasata, ita tunda take dashi bai taba daga muryarsa da sunan fada ba, sai dai ya kara zama cool. Tayi kwata, wallahi Haseeb green snake ne.
Duk caba adon da tayi da wani jan material Mai sulbu yana shaking a jikinta bai burgesa ba, tana fitowa ya mike Rahima ta bi sahu, har zasu fita ya tsaya ya kalli Zuwairan “Su Khalifa school suka je ko Ina kika tura su?”
Ta sassauta murya “Suna school, daga can zasu wuce gida.”
Yasa Kai suka bi shi.
Hhmmm su Zuwaira ashe wargi wuri yaka samu.
14/09/2020, 22:44 – Anty saliha: ..ˆRAHIMA..doc by jami
34
Uwargida ta zauna gaba, amarya na baya, angon na tuki a sukuni, babu mai magana cikinsu duka har saida ya furta cewan akwai tsararbar da ya taho dasu a boot na Mahaifiyarsa da iyayensu kowanne da ledarsa.
Rahima ta saurara taji Zuwaira tayi godiya bata yi ba, ta bude baki tace”Mun gode Allah ya Kara budi.”
Adduar ta yiwa maigidan dadi saboda bai taba yiwa matarsa ko iyayenta wani alkhairi tayi godiya ba, infact ita kullum gani take tunda yana aurenta wajibi ne yayin, idan yayi Kuma ba wani gwaninta ne a gareta ba balle har tayi godiya ta dora da addua irin yadda Rahima tayi masa ba, dadin da yaji yasa ya kallota ta mirror yace “Ameen nagode da addua. Cikin sakin fuska.
Hakan ya Kara sa Zuwaira tsuke fuska.
Suka Yakasai Hjy Kaltume ta tarbesu da murna da farin ciki, abin gwanin shaawa, suna gama gaisawa ta fara yi musu nasiha, ta fara da Uban gayyar cewan ya rike matansa da zuciya daya tsakani da Allah, yayi kokarin kwatanta adalci tsakaninsu, yaji tsoron Allah, ya tuna da mata da 'y'yansa amana ce a gareshi, yasan Allah ba zai barsa ba muddin yaci amana ko zaluntar wata.
Ta juyo kansu tace “Ku Kuma kin zauna lafiya, ku rike mijinku fisabilillah, kuyi biyayyar aure yadda Allah ya umurceku dayi, ku sani aure ibada ne don haka ku tafiyar da rayuwarku da bin dokokinsa. Ke Zuwaira ki Kara hakuri, ki rike girmanki karki sake a rainaki, ki daure ki sanyawa zuciyarki salama, ci gaba bai samuwa sai inda aka yi hakuri.. idan ma an zalunceki ki kayi hakuri Allah zai saka miki ..
“Dole a bani hakuri Mana tunda an riga sn zalunce ni, in gaskiya ne me yasa aka rasa wace za a hadashi da ita sai matar Rabiu?” Zuwaira ce ta katse maganar sarakuwarta…
Hajiya da Rahima suka bude baki cikin mamaki..
Shi Kuma ya juya a hankali ya kalleta “Kinsan nayi warning dinki ko? Saboda nasan hakan zai faru, to wallahi idan Kika sake ce tak na nuna rashin mutuncin Mahaifiyata na gama aurenki tun a nan ba sai mun matsa ko Ina ba.”
“Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun to ba a gabana ba, ba gidana ba, Kuma ban amince ka karya kadarin aurenku ba.”
A fusace yace “Hajiya zan yi mata hakurin komi a duniyar nan amma banda wulakanta min ke, sam ba zan taba yarda da wannan rainin wayon ba, idan ba rashin kunyar banza ba ta kalli kwarar idonki tana fada miki wadanan surutan, yau na Kara tabbatar da baki San mutunci ba, baki San darajar na gaba dake ba.”
Hjy Kaltume tace “Wallahi in don Ni na yafe kaima Kuma kayi hakuri, kasan bacin rai ne.”
“Bacin rai da akayi mata mene? Aure ne nayi duk abinda za kice kin dade, na auri matar kanina, aurene muke yi ba zaman banza ko?”
Sai anan Rahima ta tanka “Don Allah kayi hakuri a bar mahanar.”
Ya gyara zama “Daga yau kowaccenku ta sani ban hada Mahaifiyata da kowa ba a duniya, haka ina kaunar ‘yan uwana kaf fiye da zaton kowa saboda haka duk wace taga ba zata iya kaunarsu ko girmamasu ba zama dani ba dole bane.”.
Hjy Kaltume ta nisa “Ka cika mita, batun ya wuce ai, ina Kara horonka da kayi hakuri a matsayin Wanda ya tara, muna tayaku addua kullum Allah ya albarkaci rayuwarku.”
Har zuwa lokacin Zuwaira bata ce ayi hakuri ba, to bashi cikin policy dinta sam sabida a ganinta laifin me tayi? Daga fadar gaskiya kawai a dake ka a hana maka kuka a kan me?
Sun baiwa Hajiyar tsarabarta wadanda suka kunshi duk abubuwan da yasan tana so ne ya karo mata kasancewar daman bata rasa komi ba.
Daga nan gidansu Rahima suka nufa, Umma ta kasa rufe baki don murna, nau'ikan abinci ne aka jera musu na tarbonsu, gefe kayan sanyi ne da ababen motsa Baki, Umma akwai iya tarbon baki...
Alh. Mamman na gida don haka bayan ya tsaya sun gaisa dasu Zuwaira yaja Haseeb suka koma soro suka shimfida tabarma ana gaisawa.
Suna Nan har aka dauko Abdul daga makaranta yaga babansa ya daka tsalle ya haye jikinsa yana murna.
A cikin gida Zuwaira tayi kasake tana kallon yadda ake nunawa Rahima so da kauna irinta tsakanin da da iyaye, ita Kuma tana basu girmansu, ta kanta domin da ita gani take ai ‘gata ce a gidansu ashe gatancin Rahima shine gata Kuma ya dama nata ya shanye don ko ba komi gatan bai zamar mata wauta ba balle cuta.
Tun tana daure fuska har ta gaji ta saki, to Umma macece mai harka ga iya zama da mutane, ta nunawa Zuwaira su basu iya hauka ba.
Suma sunyi murna da tsarabar bakin sunyi godiya sosai.
A rijiyar Lemu aininhin Mahaifin Rahima ya nuna Haseeb ba surukinsa bane, Lauratu ce tace ita kam surukutat za tayi da likitan, daga karshe duk da kunyar Rahima da yake ji bai hanata kebewa yai mata nasihohi ba kana ya hadasu yai musu addua, da kyar suka amshi tasu tsarabar suna sa albarka
A gidansu Zuwaira kuwa sai ta canza, basu dade da shiga gidan ba ta nunawa Rahima cewan gidan ubanta ne ta wuce gaba ta barta, Rahima ta saki fuska tamkar ta taba zuwa, suma iyayen Zuwaira da ‘yanuwanta sun mata kyakkyawar tarbo, suka karramata.Tayi mamakin ganin ingantattar tarbiyyar sauran yaran gidan, kenan kan Zuwaira aka samu zakka. Ganin irin yadda iyayenta suka amsheta da hannu biyu yasa tayi kudurin zama lafiya da diyarsu duk iya fitinar da zata tayar don sunyi mata halacci, sunyi musu nasihohi da adduoin suma.Abdul ya lakewa yan uwansa da suke gidan, suma din kakansu yace su bi iyayensu gida.
Zuwaira tayi kwatakyas data ga irun tsarabar da mijinta ya jibgowwa nata family din, duk inda suka fito nasu bai Kai na gidansu yawa ba, yayi hakan ne sabida yawan da suke dashi amma ba dominta ba…
Sai karfe goma na dare suka koma gidansa na Galadanci inda ya mikawa kowa nata tsarabar dana Yara.
Sun tashi tafiya Uwargida ta hade rai, Rahima tayi mata sallama ta amsa a ciki bata kula ba ta rike hannun Abdul su tafu yaron ya cije shi wajen su Khalifa zai kwana, suma suka ce ki dai a barsa wurinsu, ko su bishi dorayi su kwana can, Rahima tace a tarkato mata su tafi can gaba daya.
Zuwaira najin haka tace “Gaskiya ba inda zasu.”
Yaran suka sa kuka, uban ya wuce cikin bedroom dinsu ya kwaso kayansu ya tasa su a gaba su ukun ya saka a mota kana ya cewa “Rahima ki tafi ku shiga mota Ina zuwa.
Taja hannayensu suka fita waje.
Tana fita ta fara yarfa ruwan bala’,in don me za’a kwashe mata yara ya kai gidan wata, Kuma ba’a tambayeta izni ba.
Ya kalleta “
“Gidan watan da kike ikrari gidana ne, yarana ne akwai wanda ya isa ya hanani daukarsu ne tunda can naso su kwana?”
Ya barta baki bude yai gaba, su kuwa Yara sai murna suke.
15/09/2020, 12:01 – Anty saliha: ..RAHIMA…doc by jami
35
Suna shiga gida Uwale ta taimaka mata suka yiwa yaran wanka tayi musu Shirin kwanciya sannan ta kaisu dakin da aka kebewa Abdul ta shafe kowannansu da azkhar din kwanciyar barci, suka kwanta, ta sakayo musu kofa ta koma dakinta ta fada wanka itama.
Tana gama wanka ta dauro alwala, Rahima ko yaushe cikin alwala take dare da rana, ko ya karye zata sake wata saboda malaminsu ya fada musu muhimmancin yin hakan, Wanda ke kwana da alwala mala’ikun rahama Kan bi kowacce kafar gashinsa suna yi mada addua da neman gafara, sannan duk wani shaidanin maridin aljani ba zai kusance shi ba, haka shaidan la’ananne zai nisance shi.