
Tsaye take a tsakiyar dakinta daure da katon towel bayan ta fito daga toilet, ta dauko man shafawarta data hade da turaren miski ta fara shafawa tana maming wakar nan ta back street boys I don’t care who you’re , where you’re from, what you do, as long as you love meee
Kamshin dake fitowa daga cikin dakin ya fa fara dukan hancinsa, Yana isa daf da kofar yaji 'yar karamar muryarta na maming wakar da yake son shima, ya kara kutsa kai Yana sallama amma bata ji ba sabida ta shafa'a tunanin maigidan fa na iya shigowa ya ganta ba sutura a jikinta, idan ya ganki fa, ba mijinki bane wata zuciyar ta bata amsa..
Bata ankara ba kawai taga mutum a gabanta, taja da baya a firgice ta bude baki zata buga ihu..
Tafin hannunsa yai saurin sawa ya rufe bakinta tareda yi mata magana a hankali”Me yasa kika cika tsoron tsiya ne?”
Ta saki numfashi jikinta ba inda bai rawa, ganin haka yasa ya janyota garesa ta langabar da Kai, kafafunta sunyi sanyi da ace bai riketa ba zata iya kaiwa kasa.
Haseeb ya kara mannata a jikinsa har tana jin bugun zuciyarsa, ta dago a hankali tana kokarin kubcewa Amma baiyi niyyar rabuwa da ita ba, wani abu take ji Wanda bata taba experiencing ba…
Ya tallabo gemunta don ta kallesa, hasken da taga kwarar idanunsa na fitarwa yasa tayi saurin rufe nata idanun, yayi mumushi “Wai wace irin kunya ce haka da taki karewa?”
Tayi shiru ta Kara rumtse idanun.
“Rahima bude idanunki ki kalleni.”
Ta girgiza Kai ta Kara cusa kan nata cikin jikinsa tana shakar kamshinsa.
Ya sumbaci tsakiyar kanta, warm lips dinsa suka haifar mata da kasala, ya sassauta rikon da yai mata da niyyar kissing dinta…
Wayarsa dake cikin aljihunsa ta fara sound na alamun an kirasa, ya share bai daga ba harta tsinke, aka sake kira, kamar ba zai daga ba again, ya tuna matsayinsa da irin aikinsa na ceton rayukan al’umma, nan da nan ya fiddo wayar ya daga yana sauraren mai kiran, kusan minti biyar kana ya aje ya tsaya yana kallon Rahima data koma gefen gado ta zauna, ya matso ya tsugunna a gabanta..
“Ina fatan lafiya.’. Ta furta da taga yanayin damuwarsa.
Ya dafa gwiwarta “Dr Kabir ne ya Kira cewan mun Sami wata patient daga Maiduguri tun dazun Kuma yayi iya nasa kokarin babu canji so zanje mu gani may be sai anyi mata surgery don jini ne ya shiga kwanyarta sanadiyyar accident da tayi.”
“Subhanallah Ubangiji ya bata lafiya, me zan taimaka maka yanzun don ka hanzarta shiryawa ka tafi?”
Rahima ta Fadi cike da tausayin matar da bata sani ba
Ya mike tsaye cikin zafin naman nan nasa “Ki dai tayamu addua please, sai na dawo.”
Zuwa karfe 12: am Dr Haseeb da sauran likitoci hudun da yake jagoranta sunyi nisa da binciken kwakwalwar patient din, sun Kara daukar awa uku cur kafin su ciwo kan problem din a inda ya yanke shawarar ba sai yayi mata surgery ba, abubuwan da suka yi mata zai taimaka jinin ya rinka gangarowa ta hancinta ana zukewa har yayi clearing.
Bayan nurses sun Kai patient din dakin jinyar kuma ya shiga ya dafa kanta ya dade yana karanto adduoin samun shifaa gareta, wannan al’adarsa ce ga patients din sa Kuma Ubangiji na amsar adduoinsa yasa a samu waraka ko da an yanke teammanin samun waraka.
Mijin maras lafiyar ya rasa irin godiyar da zai yiwa Dr Haseeb tunda ya shaida masa she’s out of danger. Kwarai Alh.Ahmad Sharif ya yaba da kwazon gwarzon likitan musamman ganin irin dedication dinsa kan aikinsa, gaskiya he’s very committed to his job.Dr Haseeb ya maida kansa bawa wajen geagwarmaryar ceton rai ko neman lafiyar duk maras lafiyar da aka kawo asibitinsa.
Wata damuwa da Alh Shatif ya gabatarwa Daktan shine cewan basu San kowa a garin Kano ba labarin asibitin kawai suka ji ya dauko matarsa suka yo gaba, tunda satinta biyu da yin hadarin, bayan kukkujewa da tayi nan da can ne sai ta fara sumbatu Kuma, barci yai kaura daga idanunta, sai anga sauki abu ya dawo, so wasu ne suka basu shawarar su kawota wajensa.
Daktan yace ksr ta Sami damuwa harkar accommodation, asibitin sunyi tanadin guest house dab da asibitin saboda irin hakan.Batun hidimar abinci kuma zaisa matarsa ta aiko.
Alh Ahmad Shariff ya fara zuba godiya Daktan ya katse shi cewan musulmi duk inda yake danuwan musulmi ne, Kuma shima an taba taimakonsa.
15/09/2020, 18:50 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
36
Rahima ta kalli agogon dake manne a bangon dakinta, dare ya fara tsalawa, karfe daya harda wasu mintoci amma shiru maigidan bai dawo ba.Ta saki ajiyar zuciya auren likitan kenan, wata rana ma can zai kwana that’s why ake son matansu su kasance masu hakuri da dangana. Ta juya gefe, ita ta rasa dalilin da idanunta suka kekashe ta kasa barci bayan na tattare da gajiya. To me ya hanata barci kuwa illa tunanin da ace maigidan bai fita da yanzun suna tare watakila ma a shimfidarta? Oh ni Rahima, shin Ina kunyar Ya Haseeb ya tafi ne har nike irin wannan tunanin?Anya kaunar da nike masa zata boyu kuwa?
Barci ya fara fisgarta tana kokarin bude idanu amma ina! Sarkin karfin ya dauketa…
Har ya shigo cikin gidan ya shiga dakinta bata sani ba, barcinta yai nisa, yayi kamar ya tasheta ya fasa. Duk da barci take ta Kara yi masa kyau da kwarjini, bai iya tantance tsananin bugawar da zuciyarsa keyi, shin dalilin matsanancin sha’awarta ce ko kuwa so ne ya fara surfafar zuciyar?
Tunda baida amsa a lokacin, ya matsa kusa yasa hannu ya gyara mata hannunta data lankwashe tareda shafa kanta a hankali. Jikinta yai dumi amma ba na rashin lafiya ba, duk yadda yaso ya daure abu ya faskara ya duka yai kissing chicks dinta, ta dan motsa kadan taci gaba da barcinta kan dole ya cije ya nufi dakinsa ya kwanta.
Qira’ar qur’anin da take yi ya bashi tabbacin ta jima da tashi, shima sai da ya kare nasa ya nufo dakinta yai zaune bakin gadonta yana jiran har ta kammala ta shafa adduointa sannan ta mike cikin natsuwa ta isa dab dashi ta tsugunna. “Ina kwana, ya kaga mai jinyar?” Ta fadi a hankali.
“Lafiya lau, jiya ban dawo ba sai muka tabbatar bata cikin wani hadari, insha Allahu zata sami sauki.”
“Ubangiji ya amince ya bata lafiya, nima da har na tsaya jiran dawowarka unfortunately, barci barawo ya dauke Ni ban farka ba sai asubah.”
“Yes ai ma shigo na samu kinyi nisa sai na kasa tashinki saboda you were sleeping like a baby, looking so beautiful and innocent, naji kamar in zauna kawai in yita kallonki.”
Kunya ya kamata “Lah daka sani ka tashe Ni…
Ba wani jin kunya ya kalleta yace “Kinsan abinda zai faru da na tashe ki?”
Ta mutu a zaune.. Wai me ke damun Ya Haseeb ne yake zaro zancen da bai dace ba?
Nauyin jin kalamansa yasa ta kasa dagowa.
Ya girgiza Kai yana murmushi yace “Ba ni da amsar maganata kenan?”
Ta daga kai alamun amsar sa.
Yace “Hhmmm ashe zan zo in fara adduar Allah ya rage miki jin kunyar saboda idan baki saki jikinki dani ba ya za muyi zaman auren kenan?, I mean if you’re not free with me ya Zaki lakanci halina, in san naki Kuma?”
Tace “I will try my best.”
“Yauwa haka ya kamata, yanzun taimakonki nike nema kan patient din da aka kawo jiya…. Ya zayyane Mata halinda suke ciki da irin taimakon da yake son yi musu.”
Rahima tace “Ba damuwa Allah na taimakon Wanda ya taimaki wani.
Bari inje mu shirya musu breakfast sai in shirya mu tafi tare?”.
Ya amsa “Okay, godiya nike.”
Sun isa asibitin kenan Allah ya nufi Hjy Fatima da farkowa daga barci daidai maigidanta Alh. Ahmad ya shigo cikin asibitin suka hadu da babban likita a nurses station, ya mikawa likitan hannu suka gaisa, Daktan ya tambayesa “Ya kwanan patient din tamu?”
Alh. Ahmad ya washe baki yace “Ai naga abin mamaki jiya kamar wani magic wallahi tunda kuka gama dubata baiwar Allah nan ta samu natsuwa tayi barcinta lafiya, ba buge,-buge, ba wasu ‘yan surutai da take yi a can inda aka fara dubata.
Dr Haseeb yace “Alhamdulillah, yanzun tunda mun samu tayi barcin fiye da awa shidda, brain din ta zama relaxed, yau zamu sake sakata cikin na’ura mu bincika sosai ko da wata matsala a San matakin da zamu dauka, idan iyakar problem din da muka riga muka gani jiyane kawai, mun shawo kanta tun jiya din ma said mu jira karin samun sauki, Allah yasa mu dace.”
Ya amsa “Ameen Dakta, muna fa godiya sosai Allah ya Kara hasken ilmi.”
Yana magana ya kalli Rahima yace “Ikon Allah ga wata kamar ‘yaruwa.”
Dr Haseeb ya kalli matarsa, ba shakka irin shigar nata ce tayi ta nannada lapayya, tayi kama da bare-barin, shi ko bata saka shi ba takan yi masa kama da matar kasar Chad. Ya sake bin ta da ido, ya juya yaga yadda Alh.Ahmad ke wani washe baki, kishi ya turnukoshi har yaji mamakin kansa, ya gyara murya yace “Wannan amaryata ce Alhaji ta shigo wajen ita patient din ce at least taji ko akwai abinda suke so tunda ku baki ne.”