
Alhajin ya gintse dariyarsa har dai daya lura da canjin fuskar Daktan, ya gyara tsayuwarsa yace “Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi da albarka cikin auren, sannu Hajiya.”
Ta amsa a darare saboda itama taga yadda mijin nata ya hade gira, miskillancin ya taso kenan ta fadi a zucci. “Ina dakin da pateint din take?” Ta tambaya aka nuna mata.
Soyayya gamon jini, haka Allah shi ke hada mutaneya sanya kauna tsakaninsu. Mintoci kalilan da shiga Rahima wajen Hjy Fatima Allah ya hada jininsu,bayan sun gaisa suka Dan fara hira a hankali kafin su saki jiki tamkar sun taba haduwa.
Rahima ta zuba mata abincin kalacin data kawo musu ta rinka bata a hankali tana ci bayan ta taimaka ta jingina mata pillow ta zauna.
Hjy Fatima farar mace ce doguwa Mai jiki, kyakkyawa ce, tana da tsagen bare-barin a fuskarta sunyi mata kyau..
A haka mazajen suka tarad dasu suna hira. Hjy Fatima ta kalli mijinta dauke da murmushi a fuskarta “Alhaji kaga matar Dakta ta zama kanwata ko, me zamu cewa wadannan bayin Allah, da miji da matan kirkinsu ya Kai!”
Alh Ahmad yace “Ki bari kawai, wallahi na rasa irin godiyar da zanyi, wannan dawainiyar sai dai Allah ya biya.”
Ta gyada Kai a hankali “Sai Kam addua garesu kawai.”.
Dakta Haseb ya matsa kusa da gadon patient din ya dau file dinta dake sargafe yace “So Hajiya ya jikin naki, da kika farka akwai jiri ko ciwon kai?”
Ta amsa “Alhamdulillah tunda na farka banji komi ba gaskiya, sai dai dan nauyi kadan da naji kan yayi min.”
Ya gyada Kai “Yes is expected, shima zai bari a hankali don haka kar kice za kiyi garaje a bi a hankali ko? “
“Toh Dakta mun gode sosai, na Kuma gode da ka hadani da kanwa ta muamman.”
Ya kalli Rahima yai murmushi sannan yace to za kuyi min afwaa ku tsahirta mu duba patient please.
Rahima kije office dina ki jirani.”
Ta yaba kwarai da tsarin office dinsa, komi tsaf-tsaf, ya kawata office din da hoton shugaban kasa Dana gwamna masu ci yanzun, sai hoton marigayi Sani Abacha again, still da karamin Aquarium dauke da wasu kananan kifaye kala uku Kuma kwara ukun tal kyawawa dasu suna ta yawo cikin ruwa.
Bisa tebur dinsa frames ne guda 4 kanana masu dauke da pictures din Hjy Kaltume, su Khalifa da Abdul dinta, Bata yi mamakin ganin hoton Abdul ba don irin shakuwarsa da yaron.
Ta gaji da zama ta mike taje gaban aquarium din Nan ta dibi abincin kifayen nan ta rinkka zuba musu tana musu magana.
Ya bude office din a hankali ya shigo, bai tsaya ba sai a bayanta yace “Sorry though naga kin samu abokan hira.”
Ba damar ta juya saboda yayi kusa da ita sosai, ta amsa “Tace yes na samu friends, sunada sunaye kuwa?”
Ya Kara matsawa har kafadarsa na gogan kanta yace “No na bar miki wannan aikin.’
Ta girgiza Kai “Ni dai a bar min wadancan na gida, ka rike wadannan.”
” Toh naji, idan na kirasu da sunan colours dinsu, yellow, red and green ba laifi ko?”
Ta daga kafada “Okay, idan sunyi maka, Zan Kira nawa piece, blessing& comport
Yace ” Gaskiya ban yarda ba ai wayo kikai min.”
Tayi murmushi kawai.
Yace” Shikenan sai me, Ina zamu yau?”
Tace “Kace gidan su googo da Malam zamu, na rokeka ka ajiyeni gidan Maryam har ka manta?”
Ya sauke numfashi “Na tuna hakan za ayi but ya zaki yi da sabuwar Auntyn ki?”
Tace “Maryam zata kawo ni asibitin daga nan ta ganta sai in sameka a nan mu koma gidan, ba zaka je gidan Aunty Zuwaira ba?”
“Yes na kirata ma bata jin dadi.”
Tace “Subhallah, Allah ya bata lafiya,don Allah ka gaida min ita.”
Yace “Je ki sallami kawarki ki taho mu tafi.”
Rahima ta koma wajen Hjy Fatima ta Bata hakurin cewan zata tafi ta dawo zuwa dare.”
Tace “Ba komi zuwa lokacin ma insha Allah yanuwanta sun iso don suna hanya.”
Suka Kara yi Mata godiya itada mijinta ta fito ta isko Daktan suka shiga mota suka fito daga asibitin.
15/09/2020, 22:31 – Anty saliha: ..RAHIMA,..doc by jami
37
Daktan da Rahima sun kewaya gidajen da suka ce zasu tafi daga karshe ya ajiyeta gidan ‘yar uwarta ya wuce gidan Zuwaira.
Alh. Abbas ta fara karo dashi a kofar gida kafin ta shiga ciki, bayan sun gaisa ya fara mata barkwanci "Daman kuwa Ina Shirin tahowa gidanku amsowa abokina magani.".
Tayi dariya “Kai dai baka rabo da ban dariya, Daktan ne ma zai bashi magani?”
Yace “Yes idan anyi masa ai an rage masa zafi.”
Tace “Ko dai a Kara masa.”
A cikin gida sun jima suna hira da Suwaiba da Maryam, inda Rahima ta basu sha’awa sam taki amincewa suyi hirar Zuwaira, duk inda suka bullo saita kauce, to ribar me zata ci idan taci naman ‘yaruwarta musulma a cewarta.
Saida suka kebe, Maryam ta tabota “Ke ina labari, ya canza kuwa?”
Rahima ta nisa “Sosai ni har tsoro yake bani, ya canza ya rage daure fuskar, sai dai na kasa sakin jikina dashi gaskiya.”
Taja tsuki “Ai tsiyarki kenan, don me ba zaki saki jiki ki sakata ki wala da mijinki ba alhalin yana sonki tun kafin a daura aurenku na fahimci kuna son juna, amma kuna abu kamar wasan yara? Anyway kuka sani.”
“Ni kuwa dadi dake wutan ciki, Ina amfanin garaje? Sannu bata hana zuwa ai.”
Maryam ta zaburo “Amma a dade ba a Kai ba kuwa a rinka kallo ana hadiyar miyau, look Rahima nasan rawar jiki da saurin bada Kai na ragewa mace kima a idon namiji, inda yawancin maza ma Kan fassara hakan da rashin kamun Kai ga ita macen. Idan nace kamun kai Ina nufin natsuwa a gaban masoyi cikin kowanne hali da kuma cikin jama’a, rashin natsuwa na zubar da mutuncin mace, natsuwa kuwa kara mata daraja yake yi a idon jama’a da masoyinka.
Duk da ya kasance wannan muhimmin al’amarin ne a rayuwar Mata, ba a son mace ta kasance miskilan gaske kar kuma ki zama mai sakin fuska, ba a son mace ta zama mai yawan washe baki tana dariya ba natsuwa a yayinda ta zama ba mai daure fuska ko da yaushe ba, ta dai zama tsaka-tsaki.
Rahima ba nace kiyi masa shishshigi bane din hakan nasa kiyi saurin gundurarsa, dole ki rinka kina ja da baya amma ba kowanne lokaci ba, lokacin da kika lura miskillancin sa ya tashi sai kin kebe sai ya warware.
Karki zama mai tsananta kwalliya fitar hankali, Kar Kuma ki kasance kazamiya. Ki tabbatar da kina faranta masa rai, kina bashi shawarwari na gari, ki zama Mai danne fushinki idan ranki ya baci, ki yawaita bashi hakuri idan ya nuna kinyi masa laifi koda kuwa kece da gaskiya. Ki zama Mai lura da hidimomin da suka shafi hakkokinsa na gida da waje, ban ce ksr kija masa aji ba don mace kike amma aja a hankali sannu sannu don namiji tamkar yaro yake ko da suka Raina mu sai dai bamu so juya su ba, ba boka ba mallam, ah ah ko alama, so da kauna, ladabi da biyayya, hakuri, yi nayi bari na bari sai su mallaka miki mijinki a tafin hannunki don duk namijin da yai dace da macen da take tsare masa wadannan dabiun y dace ya kyautata mata shima ya guji bacin ranta yadda take gudun nasa don yasan ya ajiye matar kwarai cikin gidansa unless ya zama butulu wannan Kuma Allah ba zai barsa haka ba zai fitar miki da hakkin ki.
Ke din karki zama Mai danne hakkinsa, idan ma wani laifi ne gara ya fito daga garesa. Idan kin daure Allsh SWA zai daukaka darajarki.”
Raf-raf-raf! Rahima ta tafawa Maryam “Yanzun Kam babu mai kama ki da laifin karatu ba amfani cikin marubutanmu naji sai gaba yake yi, nagode ‘yaruwa, zanyi iya kokarina da taimakon Allah.”
"Oho na dai fita hakkinki, ni yanzun ma Dakta nafi baiwa laifi.'
Ta bude baki “Wane laifi Kuma?”
Ta muskuta “Ah to ba namiji yake ba sai yace kule ace masa cas! Ko sai zuciyoyinku sunyi bursting?”
Rahima ta jinjina “Wane irin bursting Kuma?”