
"To in baku ba ya za ayi ina so Ina kaiwa kasuwa?"
“Allah ya shiryeki a bar batun Ni dai.”
A nan suka hadu suka dafa abincin da zasu Kai asibiti, Maryam ma tace tana neman ladan.
Karfe takwas na dare suka koma asibiti harda Alh. Abbas inda suka taras da ‘yanuwan Haj.Fatima sun iso lafiya.
Matafiyan uncles dinta ne su biyu da kanwarta Falmata wace zata zauna tareda ita har ayi sallama.
Lokaci kankani matan suka zama tamkar 'yanuwa, Falmata sun sarke da Maryam, ita din zawarci take kuma bata taba haihuwa ba a inda ta fiton, Hjy Fatima kuwa yaranta hudu, maza uku mace guda, bata da kishiya, sai ma dalilin wannan hadarin ne da yaso ya zama kamar ta samu tabuwar kwakwalwa dangin miji suka fara batun ya nemi wata matar, bai dai saurari kowa ba a lokacin hankalinsa tashe yake yana neman wa matarsa uwar 'ya'yansa hanyar da zata samu waraka, bisa dukkan alamu Kuma an dace.
Sai karfe goma saura Alh Abbas da Ahmad Shariff suka shiga cikin ward din, Abbas yacevwa Maryam ta taso su tafu gida akwai alamun hadari ana walkiyya.
Da jin hakan Rahima ta mike itama tace zata bisu su ajeta kawai tunda har zuwa lokacin Daktan bai dawo ba.
Koda suka ajeta basu tsaya ba saboda hadari na shirin tasowa, Maryam ta leko kai ta windo tace “Ya za kiyi yanzun na sanki da tsoron ruwan sama.”
Rahima tace “Kin cika tonon silili saida safenku.”
Ta shige gida Kai tsaye dakin Uwale ta wuce ta sameta har ta kwanta, ta tashi zaune “Oh a gaisheki Hajiya sai yanzun?”
Tace “Ke dai bari, yau ma zirga-zirgan muka sha duk na gaji, wanka kawai zanyi in kwanta.”
Uwale tace “Ga garin ma da alamar ruwa za ai Mana.”
Ta wuce tana fadin “Allah ya bamu Mai albarka, mu kwana lafiya.”
Kasancewar ta gabatar da sallolinta cire kayan jikinta kawai tayi ta fada wanka, inda Saida ta cika bath din taf da ruwan dumi, ta zazzaga bath salt a ciki, ruwan ya dau kamshi da kumfa Mai sulbu, ta shige ciki tayi wanka ta fito ta gabatar da alwala ta fito. Ta goge jikin da yayi smooth, bata shafa mai ba balle wani make up, just turare ta mutstsuka a jikinta ta saka cotton night dress tana tunanin may be weather din yai sanyi a dalilin ruwan saman da taji yana shirin saukowa.
Tayi adduointa ta kwanta, ta dauki wani novel ta bude ta fara karanta shafi guda ta rufe, hirarsu da Maryam ne ke mata yawo a kai.
Ba shakka gaskiya ta fada mata hakika son mijinta ya mamaye zuciyarta ba karya, yanzun ne ta Kara fahimtar maanar so da kaunar wani, watau da shirme take, to Allah yasa ba tana abin nan da hausawa ke Kira son ma so wani ne ba.
Ai da kuwa wahala ta ganta, oh oh Allah Mai yin yadda ya so, ya dauke kani ya hadata da wa to Amma a wane babi take cikin zuciyarsa?
Ta zabura ta tashi, tunda ba amsar zata samu ba is better ta tashi ta gabatar da sallah ta Kara addua.
Ta shafa kenan taji dawowar Haseeb.
16/09/2020, 06:08 – Anty saliha: RAHIMA…doc by jami
38
Ya shigo ya sameta kan sallaya, mamaki ya nuna a fuskarsa amma yace “Kin ganni sai yanzun ko? Kiyi hakuri.”
Ta kada Kai “Ya Mai jikin?”
Ya amsa “Da sauki malaria ce ke damunta.”
“Allah ya saukaka, ba wani abinda kake so don kwanciya zanyi?”
Yace "Akwai, but kiyi min hakuri inyi wanka please.".
Ya fita yana tunanin why ta daure fuskarta tamau haka, ba dai kishi ke damunta ba itama, idan hakane zaiyi farn ciki don alama kenan na kamu da son sa kamar yadda yake jinta a zuciyarsa.
Bayan fitarsa tayi kasake! Lalle ma namiji sai a barsa kawai, ji yadda ya shigo yana mata wani shan kamshi sai kace in laifinne bashi yayi mata ba ya dawo Yana tabarmar kunya. . That’s why fa Ubangiji yace ba zasu iya adalci ba sai dai su kwatanta.
Hhmmm Kar shaidan ta xugata tana zargin abinda bata gani ba ance ko zato zunubi. Tausayin Zuwaira ma ya tsirga mata dole fa ne baiwar Allah Nan tayi kishin mijinta…
Ya sake dawowa ya ganta zaune inda ya barta “Har yanzun adduar ake ne?”
“Ah ah”. Ta amsa a takaice.
Yace “Allah ya karba mana amma da kin matso nan ko haka zan rinka maganar kina can Ina Nan?”
Ta mike cikin rashin karsashi ta dawo dab da gadon da yake zaune a kai ta zauna.
16/09/2020, 22:25 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
39
Ya kalli yadda ta wani takure a gefensa ya girgiza kai yace “Rahima ya dace ki fahimci matsayinmu na ma’aurata, meye kike dari-dari?”
Tayi shiru bata amsa ba, yaja numfashi yace “Gobe idan Allah ya kaimu kwanaki ukun da aka tanadar mana zasu kare sabanin kwanaki bakwai na auren budurwa. Wadannan kwanaki Kuma ba an kebe sune kawai don ango da amarya su hole ba kadai, ah ah ana son miji ya koyar da matansa abubuwan da ya lura bata sani ba dangane da addini ko zamantakewar auren ma gaba daya.
To alhamdulillah! a ‘yan kwanakin da muka yi tare nasa ido kan yanayin ibadarki abinda na gani abin yabo ne sosai, sai dai duk da haka wajibi ne gareni in miki wasu tambayoyin kan addinin don sauke nauyin dake kaina, kin fahimce ni?”
Ta dago kai ta amsa “Na fahimta, me kake son sani?”
Ya gyara zama “Ki karanta min suratul fatihatul kitaab, ki fada min farillan alwala, sallah da sunnonin su.”
Ta nisa tukunna kafin ta da basmalla ta kare karatun kana taci gaba da jero wadanda ya bukaci sanin.”
” Masha Allah Rahima, na godewa Allah da ya nufeni da aurenki, Allah yasa diyanmu su amfana da ilmin da ya bamu.”
Ta amsa “Amin ya Hayyu ya Qayyum, nagode da yabawa.”
Daktan yayi dan murmushinsa kafin yaci gaba "To bayan wadannan akwai 'yan abubuwan da nike son in Kara miki kwarin gwiwar ci gaba da aikatawa, alal misali na lura kina yawaita alwala ko yaushe, yana da kyau matuka, ko kina cikin tsarki ko jinin haila domin Manzon Allah SAW yai Mana nuni cewan duk Wanda ya kwanta da alwala ya gabatar da azkhar din kwanciyar barci akwai mala'ikan dake bin kafofin gashinsa jiki yana kwance a karkashi da duk ka motsa ya roka maka gafarar Allah, abu na biyu ki kiyaye salar kiyamul lail, ki rinka raya dare da ibada sabida mafi yawanci jahilai masu sihiri cikin duhun dare suke aikata surkullensu, to su can suna shirmensu ke kuma kina bautar Ubangijinki.
Na lura ke mai yawan addua ce, to idan zaki roki Allah ki rinka masa fadanci kina masa kirari da tsarkakakkun sunayensu mafi soyuwa a garesa, wadanda idan aka kirayesa dasu zai amsa, idan aka nemi jin kansa dasu zai yi jin Kan, idan aka nemi yayewar tsanani zai yaye..
Ki tabbatar da kafin ki fara kowcce adduar kin fara gabatar da shimfida, watau istigfari da salatin Manzon Tsira, idan kin kare kuma ki sake rufewa da salatin.
Idan zaki yi addua ki rinka girmama rokon, ki daukesa da muhimmanci, ki rinka na ci, sannan ki dunkule bukatarki ki roki Allah Kai tsaye, ki yawaita tuba da yin adduat tare da sauran jama'ar musulmi Kar kiyi ta rokon ke kadai. Babban muhimmin abu game da addua shine tawali'u da rage aikata sabo da tarar lokuttan da aka yi nuni ana amsar addu'ar. Misali idan cikin dare ne tsakiya da karshensa don ance a wannan lokacin ne Ubangiji ke tashi da kansa yana Kiran Ina me neman biyan bukata in biya masa.. Kinga Wanda duk ya dace da wannan lokaci yayi kyakkyawar sa'a.. Akwai farkon asubah da karshenta, sai lokacin da mutum ya fuskanci abokin gaba wajen yaki, lokacin saukar ruwan sama, bayan kiran sallah da tsakanin kiran sallar da tada ikama, ko ki fuskanci alkibla ki rokesa, amma inda Ubangiji yafi amsar addua shine yayin da bawa ya kaskantar da kai cikin sujada ya roki Mai dukan zai amsa. Saboda haka yanzun ma ki tashi mu gabatar da sallar nafilar da ma'aurata keyi mu nuna godiyarmu ga Ubangijinmu da ya kaddaremu yin wannan aure, mu rokesa ya tabbatar mana da dukkan alkhairinsa ya kade mana kiwanne irin sharri.
Ta mike tsaye ta saka hijab dinta suka natsu, ya shiga gaba ta bi bayansa suka gabatar da nafilar, bayan sun idar ya juya gareta ya dafa kanta ya sake rokan Ubangijinsa alkhairinta da neman tsari daga sharrinta, daga nan ya umurceta da suka karanta suratul Ikhlas kafa 3 ko11 suyi taswili zuwa kabarin Rabiu, iyayensu da dukkan musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.
Duk hakurinta ta kasa danne zuciyarta tunanin Rabi’u da mahaifiyarta da bata taba sani ba a rayuwarta. Kuka take Mai tsuma zuciyar Mai saurare, hankalinsa yai dubu ya baci, ya fara rarrashinta “Rahima kiyi hakuri Allah ya gafarta musu, meye na zubda hawaye bayan munyi musu addua shi suke matukar bukata daga garemu”
Hawaye ya rinka kwaranya daga idanunta, ya mike tsaye cikin damuwa ya kamata suka shiga toilet “Ki Yi hakuri ki daina kukan nan haka, wanke fuskarki.” Ya umurceta.
Tayi abinda yace, suka dawo dakin, ya zaunar da ita a bakin gadon ta zuba tagumi, ya fita dakin, zuwa can ya dawo dauke da babban tray dauke da warmer da plates da kwalin mango juice dana fresh milk da cups ya dire a gabanta yace “Kinga ni yunwa nike ji tun rabuwarmu ban ci komi ba, sauko mu ci abincin.”
Bata musa ba saboda itama yunwar take ji, cikinta kamar an washe mata tas!
Ta bude warmer din, gasashshen nama ne irin Wanda ba’a bari ruwan jikinsa ya kafe dinnan, sai kamshin kayan yaji, ga tumatur da albasa an yanka kanana, miyaunta ya tsinke tun kafin ta saka yanka daya baki,, ai tana taunawa Saida ta lumshe ido saboda dadin naman, Maggi da gishi sun kama radam…
Kallon reaction dinta yake yana murmushin nan nasa, sai da yaga ta sake taunawa ta hadiye yace “Yaya, yayi dadi?”
Ta gyada Kai “Don Allah a ina aka samo ne?”
Ya girgiza Kai “Sai mun cinye za kiji.”
Ta zage taci naman nan har ta fi shi, ya zuba mata madarar ta shanye tayi gyatsa tayu hamdallah harda sude hannu.
Suna karewa ta yunkura zata kwashe kayan, ya dakatar da ita da “No yau aikina ne, bari in Kai in dawo in baki labarin inda na samo naman.”
Ya fita ta bi bayansa da kallo tayi zugum. ‘Anya wannan rawar jikin da Ya Haseeb keyi yau baids wata manufa can karkashin zuciyarsa kuwa? Ah to ta gane mana, cin nama banza ne da dare balle ga ango da amarya?”
Ba’a jima ba aka dauke wutar lantarki sakamakon kakkarfar iskar data taso hade da saukar ruwa mai karfin gaske hade da tsawa mai firgitarwa, ga walkiya na gilmowa har ta cikin window dakinta..
Rahima ta tsorata ba shiri ta haye bisa gado ta kudundune kanta cikin pillow tana salati.