NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Dakta ya dawo dauke da wata ‘yar torchlight a hannu yana haskawa, yana shigowa ya maida kofa ya rufe, ya Kara tabbatar da duk windows ma rufe suke sai yan ragar da iska ke shigowa tunda ba kura, yace “Yanzun Malam Hassan zai kunna gen gidan yayi duhu ko?”
Ba amsa, ya haska ya ganta a kudundune, ya karisa yace “Rahima mene kuma ke damunki yanzun?”
Bata dago ba ta amsa “Wallahi Allah ya hakicce ni da tsoron tsawa sa wal .. bata karisa ba, aka buga wata tsawar ratsa–tsa-tsa…walkiyar ta gilmo cikin dakin, ta saki pillow ta cakumeshi ta rike gam tana makyarkyata…

Dariya ta kama shi "Ni ban taba ganin matsoraciya irinki ba, maimakon ki rinka karanto adduoi sai ki rinka boye fuska?"

Ta Kara cusa kanta a kirjinsa tace “Me zan karanta?”
“Ya kwantar da ita tukunna ya fara rada mata “Cewa za kiyi tsarki ya tabbata ga Allah Wanda tsawa take tsarkake shi da yabonsa da mala’iku don jin tsoronsa
A hankali ta rinka maimaitawa har taji tsoron ya gushe, to sai Kuma me? Sai fahimtar halinda take ciki, gaba daya jikinsu manne suke, kunya ta rufeta, ta nemi juyawa ya rada mata Kin San hukuncin matar data juyawa miji baya ko
Bakinta ya mutu, magana ta gagara sabida yanayin data tsinci kanta ciki, jikinta yayi likis, kasala ta rufeta, tunda ya gane ta bada kai bori ya hau, daman ya riga ya hau tudu, gangara kawai yake nema, sun hade su n manne da juna, sun shiga rudani, gaba daya ji sukai tamkar basu taba wani rayuwar aure da kowa ba sai yanzun.
Suna cikin yanayin ana ci gaba da zabga ruwan sama, tuni Rahima ta manta tsoron tsawa da walkiya, shi kuwa addua yake yana kara godewa Allah daya nufesa da auren daya daga cikin matan da ake Kira SA’IDA

Lokacin da ruwan ya tsagaita barci ya rinka fisgarta ta rinka mashalo ita ba barci Mai nauyi na ita ba a farke ba yayinda ya rinka kallonta cike da so da kauna maras misaltuwa.

 Cikin dan barcin daya sure ta tayi mafarkin tana tsaye bisa wani tsauni tareda Haseeb da Rabi,'u, zuciyarta ta cika da murna da farin cikin ganinsa, ta matsa da hanzari domin ta kamo shi amma tana isa kusa yaja da baya, ta sake bin sa, ya tsaya ya riko hannunta ya matsa kusa da Haseeb shima ya rike hannunsa ya hada da nata ya manne yace "nagode daka rike amanar dana baka, ka rike matarka da kyau...ya juya gareta yace 'Ke Kuma ki bi mijinki zaku kasance cikin amintattun  masoya da suka samu ingancin aure..

Mamaki ya hanata magana sai kokarin riko shi take yana ja baya har ya bace daga nan wani mashahurin haske ya lullubesu ita da Haseeb ..
Ta farka babu inda jikinta bai kyarma saboda gigita, tunda ya rasu bata yi mafarkinsa ba sai yau, ta rumtse ido ta karanto Allahumma innee a’uzu bika min sharri maa ra’ayta fee manaamee wala yadhuru nee fee deeni wa dunyayaa

Nan take yasa hannayensa ya rungumota in a warm hug, cikin matukar kulawa yake son jin me ya tsorata ta, ta fada masa mafarkin da tayi, yayi shiru tukunna yaja numfashi ya saki kana yace “Ki daure ki sanyawa zuciyarki salama kan marigayi, nima Dan uwanane Rahima, amma ba zan so ace duk lokacin da muke tare zaki rinka kawo batunsa ba.”

Taf! A takaice yai misunderstanding dinta kenan, to a ganinsa da gangar take yi ko me yake nufi?
Nan take ta cika, ta zare jikinta ta zuro kafafunta zata sauka daga kan gadon ya dago “Ina zaki?”

Ta ci gaba da daure igiyar night dress dinta “I just want to be alone.” Ta mayar.
“Okay zo amshi key don na rufe kofar.”

Ta juyo da niyyar amsa, ya janyota ta fada jikinsa ya riketa gam ya lakace hancinta “A takaice ba kiji wa’azi ba kenan, don ke ba juya bayan ma za kiyi ba, guduwa za kiyi, Rahima baki da kirki. Ni bada wata manufa nayi miki nasiha ba, kiyi tunanin idan da bani Kika aura ba wane namiji ne zai yarda kuna tare kina maganar tsohon mijinki ko a mace ko a raye.?”
Ta langabar da Kai “Ya kayi min muguwar fassara baka fahimceni bane in dai Kuma ba kishi ne ba.” Ta karisa tana boye fuskarta.

“Hhmmm kunyarki ai na karyane in har zaki iya min Zuciya daga na fada miki gaskiya, in Kuma kishin ne Ni ya dace ma inyi fushin dake Rahima amma sai kika bugeni kika hana min kuka.”

Ta saki sa sanyar ajiyar zuciya “Kayi hakuri danu Yaya ba zan sake bata maka rai ba, but you should understand me Nima tun farko kace min auren nan dole a gareka to ya za kayi expecting barin tunani bayan nasan banda wani matsayi a zuciyarka data wuce “yar amana?”

Yayi shiruu! Lalle baki shi kan yanka wuya, yasan abinda zai fadi amma bai San illar da furucin zai haifar ba.
Rahima ta iya ramuwar gayya, shi tun ranar daya Fadi kalmar ma ta manta bai yi tunanin kalmar dole zata ja masa problem ba, gashi magana zaran bunu ce data riga ta fito ba a maidata ciki.Ya muskuta yace “Yes na tuna na furta hakan but wallahi is a mistake, i was under pressure at the time ba hakane cikin zuciyata ba, kinsan duk muutum ajizi ne ki yafe min.”
Tace “Matsayin nawa kawai nike son sani saboda ina cikin duhu.”
Ya kada Kai ” Wannan akwai ki da kure amma ba komi gidan kika taras tunda na lura halayyar mu daya.”
Tayi murmushi “Wace ni da irin halin manya?”

“Hhmmm tsokanace ma abin? To tashi muyi wanka asubah ta karato tunda kin hanamu barci.”
Kinji namiji wai nice na hana masa barci, ta Fadi a zucci..
Bata yi aune ba taji an sureta an yi cikin toilet da ita, ya direta cikin bath, yai tsaye yace “to bismillah ki inyi miki ne?”
Ta rufe ido “No nagode.”
“Dube ta da anyi magana kice kunya alhalin baki da dama.”

  Bayan ya dawo masallaci ya zauna suka yi karatun quranin tare suka yi azkhar dinsu suka shafa adduoinsu..

Ya rinka mata wani irin kallo yana nazarinta, ya tabbatar wannan lallasausar jikin nata mai kama da jikin mage yai mata tsami ko’ina…
Ta dago taga yanayin kallon da yake mata, suka hada ido tayi saurin saurin sauke nata kasa, ita dai wani bala’in nauyinsa take ji. Hhmmm har ga Allah ta gwammace yayi magana komin kankantarta da yin shurun nasa da Allah kadai yasan abinda wannan kwakwalwar tasa mai kamar computer take kirfa masa.
Ta sake satar kallonsa har zuwa lokacin ita yake kallon, ya nutsar da idanunsa alamun cikin zurfin tunani yake, da yaga shi take kallon itama yai mata signal, idanunsa sun koma tamkar na mai jin barci, nata sukayi luuu …
Da za a tona zuciyar kowanen su tsantsan so da kaunar junansu ne suka mamaye ko’ina amma sun kasa furtawa juna, hhmmm zuciya na so baki yaki fada kenan inji Aunty Hadiza Bungudu. Da baki zai daure ya taimaki zuciya ta amayo cutar data addabeta da sun sami saukin kuna da tafarfasar da take musu a daidai lokacin. Amma tunda dukkansu kowa naji da kansa sai a rinka kallon-kallo a jira har zuciyoyin su cika su tumbatsa….
Tare suka sauke sansanyar ajiyar zuciya, kasancewarsa namiji yai ta maza ya danne tukukin hayakin soyayyar da ya nemi fitowa waje ya koma kirjinsa ya cika yaci gaba da radadi, ya Kira “Rahima?”
Ta dago ido da kyar domin ita kadai tasan abinda take ji, jiransa kawai take ya furta wani Abu yaji sirrin zuciyarta amma tunda bai shirya ba ta dake, ko ba komi a matsayinta na mace ta rike martaba da darajarta har sai ranar da ya gaji ya bara.

Ta kanne tace “Ka kirani kuma kayi shiru..
Ya sake yin shiru sannan yace “Kin San anjima zan koma gidan Zuwaira ko?”
Bata yi tsammanin kalmar da zai fadi ba kenan, da taji ba warning kishi ya taso ya lullubeta ta shiga jan innalillahi wa Inna ilaihirrajiun domin kishi masifa ce, sannan ta amsa “Yes na san ka”idar ai.”

Ya kura mata ido don ya lakanci wani abu yace “Ni fa dadi na dake kenan iya zance.”.
“To me nace daban?”
Ya naji a bar zancen, batun asibiti ki bari Saida azahar ki tafi sabida ki kwanta ki sami hutu, batun breakfast ma ba zan ci komi ba for now.”
Ta kallesa “Wai don me?”
“You ve filled my apetite, na Kuma gode Allah ya saka miki yai miki albarka.”
Ta juya baya don kunyar jin kalamansa, yai murmushi, Nima kwanciyar zanje inyi amma in my bedroom muddin Ina son ki huta din.”
16/09/2020, 23:42 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
40
Bata farka ba saida akayi kiran sallar azahar cike da mamaki, rabonta da samun lafiyayyen barci haka ta manta.
Saida ta gama kimtsawa tsaf ta nufo kicin wajen Uwale, bayan sun gaisa take tambayarta Yaya ya tafi asibiti ne ban ganshi ba.”
Uwale tace “Ya jima da fita ai Hajiya, shine ya ban umurnin Kar na sake na tasheki sai kin farka don kanki.”
“Ikon Allah ta Fadi, to ya batun abincin su Hjy Fatima?”
Uwale tace “Tuni an gama aikin sabida tun jiya Alhaji yace in kwana da shirin hada musu abincin Karin kumallo, to har na ranar ma na gama an kai tun dazun, wannan zaman ma da kika ga nayi jiran fitowarki nike in damka miki sakonki in tabbatar da kin ci.”..
Rahima ta kalleta “Ban gane ba, anyi yamma da kare,meye na wani tilastani cin abinci gaskiya ban jin yunwa.”
“Ai kuwa zaki daure kici ko dan kadan ne, na dau alkawarin tabbatar da hakan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button