
Habiba tace ” Da fa masoyinta Alhaji ita taki bashi damar ya fito dama ya riga mijin Rahima magana.”
“Ahaf ai ban sani ba da an tuntubesa aji in ya shirya a hada auren ‘yan tagwayen naki mu huta.”.
“Ka shirya auren ‘yan mata biyu lokaci daya a wannan zamanin namu?”
Ya amsa “Yo me zai gagara? Nufa duk shigi da ficin kasuwancin da nike yi dominku ne, rufin asiri alhamdulillah don Allah ke yiwa bawansa, idan har batun auren Maryam ya tabbata naji nata masoyin ya shirya to ba shakka tare za a hadasu ayi sha’anin insha Allahu, a shirye nike, Allah zai rufa mana asiri.”
“Kamar inyi guda Alhaji saboda jin dadin maganarka, Allah ya Kara budi ya karemu daga sharrin makiya.”.
Ya amsa “Ameen bari in dan kwanta in huta kafin a Kira sallah.”
03/09/2020, 10:52 – Anty saliha: A turo shaidar biyan bank ta wannan Number 08034243456, Nagode
….RAHIMA..doc by jami
6
A dakin ‘yan matan Rahima ce kwance bisa doguwar kujera ita Kuma Maryam na kishingide gefen katifarsu rike da wani littafi mai suna Tun Ran gini ran zane Rahimar nata magana Maryam bata kulata har ta gaji ta fisge littafin tace “Wane irin wulakanci ina magana kamar ba dake nike ba?”
Ta juyo “Sai hakuri ‘Yaruwa na tsunduma, kinsan yadda karatun littafan nan suke, idan kina yi sai mutum ya rinka ganin abin a zahiri, Kinga Sa’adatun nan ji nike inda nice ita ba zan wulakanta Sagir ba tunda Ina sonsa.”
“Maryam sarakunan soyayya inji Rahima, kinsan nayi kokarin kwatanta irin soyayyan abu yaci tura, wallahi ban san yadda ake yinta ba.”
Maryam ta tashi zaune tace “Rahima batun naki nayi ne, soyayyar dake tsakaninku da Rabiun fa?”
Ta saki ‘yar ajiyar zuciya “In gaskiyar kike so, ban taba jin faduwar gaba don na gansa ba balle ma ace na kidime na rasa sukuni sabida rashin ganinsa, that’s why nike ganin kamar hauka kawai kuke keda Abbas, infact zakewarku tayi yawa.”
Maryam ta gyara zama “Babu zakewa a sha’anin soyayyarmu, bari inyi Miki misali donki fahimce Ni, kin karanta littafan Aunty Saliha ai, tun daga kan *Wani jinkiri, Zumuncin Zamani da Son Zuciya da wannan din nan, ko yaushe ina kwatanta soyayyarmu tamkar nasu Faruk da Surayya ne har nike ganin haka rayuwar aurenmu zata kasance domin ni din nan na karantu na dau darussa da dama cikin littafan, yadda nike ji daahi hakan yake ji dani, meye aibun mu?”
Rahima tace “Ban ce akwai aibu ba fa ina Miki bayanin duk shakuwar da mukayi da Rabi’u ban taba jin kwatankwacin abubuwan da taurarin littafan Aunty Salihar ke ji ba dangne da mazajen da Allah ya hadasu ba, shine nike tuhumar anya na san so dinma kuwa ko kuwa in tambayeki shin menene so dinnan ne?”
Ta tafa hannu “Allah ya kawo mu, Rahima baki san so ba, duk zancen Rabiun da kike kururuwar iblis ne?”
Ta bude ido ta lumshe tace “Ba shakka da na dauka kyakkyawar hulda da shakuwa irinta abota da mukayi da Rabi’u shine shine son da ake fadi, Saida na yawaita karantun littafan nan naga yadda kuke tafiyar da al’amarin naku soyayyar dole na fara doubting, anya are we right for each other?”
Maryam ta kyalkyace da dariya “Is too late to be having second thought.”
Ta buga kirji “Ina! Ba abinda zuciyata ke nufi ba kenan ba, na riga na amince da Rabiu dari bisa dari zan Kuma aureshi insha Allah, duk da cewan bashi cikin tsarin mazajen dana yiwa kaina sha’awar aure amma ya na iya da ikon Allah.”
Taja tsuki “Tun farko na rasa dalilin amince masa.”
“To da in auri wanda ban sani ba gara wanda muka saba, muka san juna, and with time zan kaunace sa “
Maryam tayi shiru kafin tace “Nasan halinki Rahima kusan ince fiye da zatonki, tun tasowarmu Ina lura dake da dabioinki, ke mace ce miskila, hakan ya haifar miki da rashin son kula kowa sai lokacin da kika bushi iska da kanki, sau nawa samaru ke approaching dinki su kyale ki dole saboda rashin samun fuska daga gareki, da yawansu sunyi min complain, suna sonki amma kinki kulasu har muka kare secondary baki da saurayi, da muka shiga B.U.K ma batun gudane baki canza ba. Na dade ina mamakin yadda kuka lakewa juna keda Rabiun naki, don naga ko wanne namiji bai isheki kallo ba. Shin kinsan Umma ta taba tsareni kan batunki har cewa tayi tana tsoron ko kina tareda wani bakin aljani ne mai saki gudun maza? Don in kwantar mata da hankali ba shiri na bata labarin Rabiu duk da nasan babu alakar soyayya cikin zuciyarki game dashi, mind you ban san abinda ke nasa zuciyar ba.”
Cikin tausayin Ummar tasu Rahima tace “Allah satki Ummana, ni kaina wallahi na fara jin tsoron kaina tun bai dameni ba na fara damuwar tunda mace nike Maryam Kuma inada masoyan nan amma ko kusa har zuwa yau dinnan banji Ina son wani ba, infact sai ji nike na tsani duk namijin da zai bude baki yace yana sona.”
Maryam ta bude baki “Naso in fahimci hakan amma banyi tsammanin yai nisa haka ba to ko dai gaskiyar Umma ne a fada mata ta tashi tsaye?”
Tayi saurin fadin “Ko kusa ba zan tayar mata da hankali ba ai ina addua gashi Kuma Allah ya amsa tunda ya hadani da Rabi’u kuma har cikin zuciyata na amince dashi matsayin mijina, zanci gaba kuma da adduoin, na sani ko nan gaba soyayyar da za muyi a rayuwarmu ta zarce nasu Surayyar, Kausar, Laila da Saadatun da kike magana?”
Tayi shewa “Abin nayi ne, Allah ya rayamu inga wannan ranar, ni kuwa dana aikawa Aunty Saliha suga yadda mai gudun maza ta shiga cikin kogin soyayya mai wuyar fitar.”
Rahima tace “Ni har kin tuna min tambayata baki ban amsa ba, shin meye so?”
Ta daga mata hannu “Ina! You’re an amateur in love ba zaki fahimci komi ba saboda baki dandani Zaki, daci da sauran abubuwan data kunsa ba, amma nayi miki alkawarin duk ranar da Allah ya dasa miki wannan baiwa a zuciyarki, kika tsunduma ciki sosai, zan baki amsar, ke dai roki Allah idan zai zo ya taho da sauki don irinku ne masu zakewa kuga tamkar kowa bai iya ba sai ku.”
Rahima ta daga hannayenta sama “Ya Allah ka dasa min so cikin zuciyata.”
Maryam tace “Ubangiji ya amsa don alkawari yayi babu bawansa da zai daga hannu sama ya rokesa face ya biya masa bukatarsa, sai mu jira lokaci da saukar ijabarsa, kin gani zan shiga wanka, Abbas zai taho anjima.”
03/09/2020, 13:41 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by Jami
7
Rabi'u Yakasai ya gama shirinsa tsaf, yau shigar doguwar riga yayi dinkin tazarce ta yadin shadda mai ruwan kasa-kasa, taji guga sai sheki take yi, ya kwafa hula kube kalar kayan, ya feshe jikinsa da sauran turaren da Ya Haseeb ya kawo masa tsaraba wata tafiya da yayi, kamshi ya bude cikin dakinsa dake soron gidansu, ya saka takalmansa cover wadanda tun la'asar ya baiwa shoe shiner kwangilar gugarsu, ya fito ya maida kofarsa ya rufe ya shiga cikin gida wajen Hajiyarsu.
Tana ganinsa ta washe baki tace “Dan auta kenan wannan irin shiga hala wajen diyata zaka?”
Cikin kunya ya durkusa ya gaisheta da yini kana ya amsa “Eh wajen Rahima zani mu karike shirye-shirye, Ya Haseeb yace in kai masa kiyasin abubuwan da suka rage ya bani yasan ya gama da hidimar.”
Hajiya tace “Gaskiyane, an gode masa Allah ya Kara budi, kaima ince ko kana yi masa adduar?”
Yace “Duk rana ta Lillahi Hjy, tsakaninmu dashi adduar ce kadai abinyu don ko godiya nayi masa sai yaita fada.”
Tace karka fasa don nasan yana jin dadi, tashi ka tafi Kar dare yayi kace Ina gaisheta.”
Har ya mike ta tsayar dashi ta bude wata Jakarta ta fiddo sabbin kudi ta mika masa bandur na dubu biyu ‘yan naira ishirin tace “Amshi ka Kai mata.”
Yasa hannu ya karba Yana tambayar “Ina kika sami sabbin kudi haka?”.
“Sai kaji inda suka fito? To kyautar Yayanku ne ya bani Ni Kuma na ajiye maka.”
Rabi’u yai tsaye shiru..” Kinga Hajiya ko kusa bai dace ba, ya zai miki alkhairi don ki amfana sai ki bani, gaskiya ba zaiji dadi ba.”
Ta hararesa “Kai zaka tafi ka fada masa ko wane, to idan ma baka karba ba Hayatu ya taho ya amsa tunda shi kullum cikin neman karin na cefane yake.”