
"Abincin baida suna ne wai?" Inji Rahima cikin curiousity.
Uwale ta duka ta duka ta bude oven ta fiddo sauran naman da suka ci tareda Dakta daten jiya ta aje mata a gaba, kana ta dauko warmer dauke da soyayyen dankali da plantain ta hada mata, ga flask cike da ruwan shayi, ta koma ta jingine.”
Ta dago “Wadannan abincin duk zan zubawa cikina? Tirkashi, to miko plate in zuba miki naman.”.
Ta wani zaro ido ta daki kirji tace “Wa Ni? Don Allah rufan asiri Hajajju wace ni da cin abincin da Alhaji yayyi da hannunsa?”
Rahima ta zaro ido “Da gaske?”
Ta gyada Kai “Wallahi shi ya gasa naman nan jiya, don ma Kar in ga abin banbarakwai tafiya yayi can sashensa sai kamshi naji kawai yana tashi, da ya fito yai min kashedin Kar in fara in fada miki, na kame bakina…
Rahima ta jinjina, wane irin mutum ne shi wannan Ya Haseeb? Bata taba ganin namiji kamarsa ya wani tube ya shiga kicin ba talkless of ace ya bata lokacinsa dafa abinci especially idan yanada mukami ko kudi, Ya Haseeb ya nuna mata yana da difference da wasu mazan, shin sai yaushe zata fahimci hatsabinin mijinta?
Sai bayan azahar direba ya sauketa a asibitin, bata ga motar sa so bai cikin office dinsa kenan, ta wuce ward din su Hjy Fatima, suna ganinta suka yi mata caa suna tsokanarta ya gajiya?
Tace “Ta me Kuma?”
Falmata tayi dariya “Kunji fa wai mu zaki maida kifin rijiya, alhalin Dakta da kanshi yace ayi hakuri za kiyi lattin zuwa saboda kina hutawa, to in ba hutun gajiya ba na menene?”
Hjy. Fatima ta riko hannunta tace “Kyale Falmata kinji, na lura ita da Maryam basu da wani zance sai irin wannan.”
Rahima tayi murmushi "Ai su experts ne."
Sun ci gaba da hirar gida Maiduguri, Rahima na sha’awar culture dinsu sosai, taji yadda suke hada turaruka na jiki dana tufafi na daki na tsugunno, daga karshe dai sunce ta bari a sallamesu Daktan ya amince suje ta gano garin Tasha mamaki…
Suna idar da sallar la”ar ta dauko wayarta ta Kira Aunty Zuwaira. Bugun farko ta daga wayar,tana jin Rahima ce ta buga tsuki zata kashe. .
Tace “Don Allah karki kashe just na kira in miki sannu da jiki ne.”
A can bangaren Zuwaira ta amsa “Kin dai Kira kiji ko muna tareda Dakta, to gani nan bisa cinyarsa.”
Tana jin haka ta aje wayar tayi zugum cikin zurfin tunani.
Suka lura da yadda ranta ya baci, suka tambayeta dalili ta fada musu, Falmata tace "Kina wasa da kissar mata kenan kin yarda da hasashenta?
Hjy Fatima tace “Da alamu ai, wallahi idan baki tsaida hankali da tunaninki ba zata rinka kulla miki makirci tana hadaki da mijinki a banza.”
Rahima tace “Gaskiyarki, hhmmm ni da har kuri Nike yiwa Maryam cewan zan iya zama da kowacce kishiya.”
“Ko yanzun ma karki canza ra’ayinki, ki tsaya Kan akidarki duk rumtsi, ki rabu da ita tayi irin nata.”
Tace “Insha Allah, sai dai fa kishin nan dana fara ji shi zai wahalsheni, ko mijina na farko nan taba jin matsiyacin kishinsa haka ba.”.
“So ke haifar da kishi kanwata, Don da kike yiwa Dakta yafi wanda Kika yiwa dan uwansa so dole kishinsa ya rinka bijiro miki amma Kar ki bari kishin ya raunana yarda da amincin da kuke yiwa juna ke dashi balle ya samu daman ruguje ingantaccen ginin tubalin soyayyar juna da kuka aza.”
Rahima tace Insha Allahu zanyi yaki da shaidan don Allah kadai yasan kudurina Kan Aunty Zuwaira.”
Suka ce to Allah ya cika miki burunki na alkhairi.”
17/09/2020, 16:21 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
41
Sai karfe biyar ta bar asibiti ta koma gida ta fara Shirin abincin dare, ba a dade ba Daktan ya dawo ya zarce falonsa, ta bishi can ta gaishe shi. Ya dago daga latsar wayar dake yace “Kiyi hakuri tunda na fita ban kiraki , Ina tareda wasu friends dina ne.”
Tayi dan murmushi “You dont have to explain yourself to me, ba komi. Tayi shiru zuwa can ta kallesa “Uwale ta bani sakonka na ci nagode, but don Allah karka shagwabani, ni ya dace in rinka shiga ina yi maka .”
Yayi dariya a takaice “Anya! Zamu shirya da Uwale kenan, ita da nace sirrine.”
“Hhmmm! Kana ta ja min aji Ya Haseeb, I am puzzled..
Yace “Ba dai kin yaba ba?”
Ta gyada kai “Sosai kuwa, just yadda aka yi hakan nike son ji.”
Yace "Karki damu kanki kan wai na shiga kicin, na saba tun Ina karami, Hajiya ce sila, kasancewa na namiji bai hana ta koya min hidimomin cikin gida ba, musamman aikin kicin, to ni kadai ta mallaka,ina tausayinta sosai, kaunar da nike mata yasa bana iya zama inga tana kai kawo ita kadai ban taimaketa ba, no, Ina kwadayin zama da nagari, abin alfahari gareta, don haka komin kankantarsa lokacin dana samu bana karatu muna tare a kicin, tare muke girki, na iya gyaran gado, wanke-wanke dasu shara tunda ni nike mata, ta nuna min cewa ba mace kadai take da hakkin kula da cikin gida ba, akwai lalurar rashin lafiya, wata macen ma ko ka aureta bata iya girkin ba, kinga a nan ba sai mutum yaita bacin rai ko yawon zuwa sayen abinci ba. Ta nuna min hanyoyin dogaro da kaina, na amfana sosai Rahima.
Gani da kyan-kyani in kin lura sam bana iya cin abincin sayarwa, a jami’a ma da kaina nike girka abincihar friends dina suka ce da catering na karanta, to ba wannan ne burina ba, sha’awa ce kawai da yanzun na zama Hotel manager. Yanzun haka akwai friends dina da suke managing manyan hotels din kasar nan.
Tunda nike ban taba cin abincin da yai min dadi Kuma na gamsu ba kamar na Hajiya ba, to sai naki wanda na ci hankalina kwance cikin jin dadi, shine nace bari a ramawa kura aniyarta.”
Ta jinjina “Lalle Allah ya sakawa Hajiya da alkhairi, ya kara maka jin kai da tausayinta, kaima yasa ka samu masu yi maka biyayyar.”
Ya bita da kallo cikin jin dadi, shi dai a ko yaushe yana jin dadin adduoin da take masa, ya sakar mata murmushinsa mai kashe mata jiki yace “Thanks so much my dear Allah ya saka miki da alkhairi.”
Ji tay kamar an zare mata lakka, ita har fargaban irin kallon nan nasa take saboda ya fara takan zama tamkar wata zombie ce. amma tasan maganin abin, ta daga Kai ta kalli agogo tace “Naga shidda saura kwata ba yanzun zaka wuce gidan Aunty ba?”
Ya Kara nutsewa cikin kujera “Korata kike?”
Ta girgiza Kai “Wai Kar a shiga hakkinta.”
“Naji zan tafi but ban tashi tafiyar ba.”
Tace “Allsh ya baka hakuri, ya batun Abdul, ina son inje in dauko shi.”
Ya gyada Kai "Yes nima nayi tunanin a dauko shi ya dawo nan ya natsu wuri daya, a rinka kaishi Yakasai din during weekends."
“Idan kayi min izni in tafi in dauko shi anjima.”
Ya bata rai “Sai dai direba ya kaiki bana son kiyi driving da dare, ku tafi da Uwale ta gaida Hajiya da Mairo daga can ku shiga asibiti.”
“Tayi shiru “To laifin me Kuma tayi yake ta wani magana fada-fada, hhmmm miskili kafi mahaukaci ban haushi, yanzun zai saki fuska, anjima ya daure tamkar bai taba yin dariya ba.
“Amshi wadannan.” Ta dago taga yana mika mata wata ‘yar jaka.
Ta sauka daga kan kujerar ta durkusa tasa hannu biyu ta amsa “Nagode.”
Ya kalli rolex dinsa ya mike “Ni zan tafu Kar a sake korata.”.
Tayi murmushin karfin hali “Haka dai kake gani, bari in dauko sakon su Khalifa.”
Ta ruga ta dauko wata jakar leda ta mika masa, Ina gaida yaran da Auntyn da jiki.”.
“Sai na kira.” Ya fadi a takaice
“Karka damu kanka Yaya in don Ni, mu kwana lafiya.”
Ya tsaya kawai yana kallonts, shi a ganinsa ma alla-alla take ya bar mata gidan tana korarsa don rashin damuwa da al’amarinsa, bai san daurewa take ba, na ciki na ciki.”
Har ya saka kafa daya a kofa zai fita ya fasa ya juyo gareta “Zo amshi nayi mantuwa.”..
Ta tako ta iso gabansa, ji kawai tayi ya rungumeta yai mata kyakkyawar kiss da numfashinsu ya balaguro na dakikoki kafin ya saketa, ya fita ya barta a tsaye.
Ta girgiza kai da yai mata dum ta taka a hankali ta koma kujera ta zauna tayi jum har saida ta daina ganin jiri-jirin da bugawar zuciyarta ta haddasa mata, hankalinta ya dawo jikinta, cikin natsuwa ta dauki gift din da ya bata ta fara ciro wasu kananan cards da wani sansanyar daddadan kamshi ke fitowa daga garesu, ta ajiyesu gefe, ta dauki wani gift din da aka yi wrapping ta bude tacu karo da wani karamin box mai kyaun gaske na glass, to ba dan akwatin ba abinda ke cikine ya burgeta, cike yake da ruwa taf, kasansa kananan kifaye ne da mami wota a tsakiyar ruwan, ta kurawa gift dinshi ido cikin tambayar why zai bata kyautar Nan, meya hadata da *Mermaid* Kuma?, Ga Kuma wani key holder da aka yiwa design na wasu kifaye biyun manne da juna jikinsu nata walkiyar ruwan ruwan azurfa, daga jikinsu aka rubuta sunanta wanda sai an kura ido za a gani.
Ta ajiye wadannan bisa cinyarta ta dauki cards din ta bude tana karantasu daya bayan daya, kalaman da aka tsaro cikin na karshen yafi daukar hankalinta, ta sake karantaea a fili I enjoyed your company so much, that I will like to enjoy it again, I never knew that you could give so much fun… I used to think that you’re always shy
Kamshin turaren Impression ya cika mata hanci, jatta hannayenta kamshin turaren Ya Haseeb suke, ta mike ta adana cards din kana ta yiwa dan box dinta na fishes mazauni kan bedside drawer dinta.
17/09/2020, 16:22 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by jami
42
Yana shiga gidan da sallamarsa ta doka tsaki ba amsawa ba sannu da zuwa balle yaji sanyi a kokon ransa. Bai kula ba Kai tsaye ya wuce sashensa ya gama abinda zaiyi ya sake fitowa, yaransa na zaune a falo suka rugo ya rungumesu “Dama kuna cikin gidan Nan?”
Abdul ya nuna uwar “Mummy ce ta hanamu fitowa.”
Yace “Ba komi, baku tambayi Dan uwanku Abdul ba “
Nan da nan suka ce “Ka taho mana dashi ne Baba?”
Ya girgiza Kai “Ah ah amma ga sakonku inji Aunty Rahima.”
Har suna rige-rigen karba, suka zazzage kayan kwalam din da ta ciko musu leda dashi suka baje kowanne ya dauki abinda yake so ya fara ci, Zuwa ta mike ta fisge na hannun kowanne ta zubar tasa kafa ta tattake sauran tana tsiya ” Aikin banza da wofi, ni za a nunawa yarana iya hila, Kai ka gaya mata ‘ya’yanka basu cin irin wannan da za a kwaso tarkacen banza kayan zawo a kawo musu?”
Yaran suka fashe da kuka, ta bisu zata bubbugesu ya kamasu ya rungume, bai ce da ita komi ba sai rarrashinsu yake “Me kuke son ci yanzun?”
Khalifa yace Ice cream?
Yace “Okay ku zo mu tafi a sawo.
Tana ganin sun fita ta biyo bayansa “Ni ban yarda wani ice cream za a sayowa ba, can din dai zaka koma.”.
Tankawa yabawa, ya saka yaransa a mota yaja suka sake fita gidan.
Tana ganin haka ta ruga cikin gida ta dau waya ta dannawa aminiyarta Husaina kira, tana dauka ta fara “Ke ni fa nayi yadda kika ce banga alamar zai canza ba, wallahi ko a jikinsa bai kulani ba, ya mai sheni wata mahaukaciya.”
Husaina tace “Tunda hakan bai tasiri ba, ba zamu ciwo kansa ta hanyar tsiya ba kenan, yanzun ki kwantar da hankalinki itama ki nemi shiryawa da ita Amma ba farad daya ba don karta dago manufarmu, data saki jikinta dake sai mu far mata.”