
Zuwaira tace “Nima naga hakan zai fi gaskiya don a kyaleka kayi ta haushi kai kadai kamar wata karya da takaici sosai.”
“Ai ke Zuwaira na rasa abinda yasa kika lakewa namiji kwara daya tal yana wulakanta ki sai kace shine autan maza, yana sonki zai miki kishiya kuma ma matar kaninsa?”
“Hhmmm zaki gane bane Husaina, sai wata zuciya tace in rabu dashi wata ta rinka kwadaita min irin dacen da nayi dana sami miji irinsa, ke wallahi Dakta fa gwarzon namiji ne, duk macen data dandani zumarsa ba zata iya rabuwa dashi ba ( kunji sakarcin banza, ahir dinku mata wajen tona sirrin aurenku. Tuni ya dace Zuwaira ta fahimci manufar kawarta a kan mijinta ko don yadda ta kan rinka kyaun likitan ko yabon halinsa da sauransu, sakarcinta ya hana, to gashi tana Kara kwadaita mata shi, Allah ya ganar da ita) my
To gashi dai ta bata shawara kamar kullum ko zata dauka oho.
Kafin Daktan ya dawo da yaranta tayi wanka ta kalelaita jiki ko’ina ta zauna jiransa…
Yana tuki yana dan waigen yaran nasa guda biyu da Allah ya bashi, duk sunyi barci, tausayinsu ya kamashi, su dai kam ba suyi dacen uwa ba, gaba daya ya sabo su ya shigo cikin gidan ta wuce dasu dakin barcinsu ya shimfide, ya tofa musu adduoi ya rufi musu kofa ya wuce bedroom dinsa yai kwance ya rufe ido yana nazarin al’amurran rayuwarsa da irin destiny dake playing role hanya daban-daban.
Ya kalli agogo, karfe sha daya saura na dare, tasan zaiyi wuya ace Rahima tayi barci by now don macece mai son raya dare da ibada, son jin muryarta ya tsananta a garesa ya kasa daurewa, nan take ya zaro wayarsa ya kirata.
Tana dagawa ya fara tambayarta “Ya kin taho da Abdul din?”
Tace “Eh ya biyoni da kyar may be don bai ganka bane, Ni na rasa dalilin da yasa bai son zama a wajena.”
“Karki damu kanki kinsan Dorayumi is a new place a gareshi, zai saba a hankali, be patient with him.’
Daga nan duk sukayi shiru, ba abinda ke bakanta masa rai da ita irin miskillancin ta, ko shi kadai take yiwa hakan? At least he has done his best ta bangarensa wajen kokarin sakin mata fuska ya aje nasa miskillancin but taking ta warware, me take son yai mata Kuma? Wani dogon tsaki ya fito daga bakinsa, Mata ko!! Idan mutum ya biye musu sai hallakar dashi wallahi, but shi din ya riga ya amincewa zuciyarsa yana son matarsa, son da ya kebe a wani bangaren na zuciyarsa, may be idan taji hakan ta dan rangwanta masa...
Zuwaira ta sallama ta shigo,bai daga ido ya kalleta ba har ta zauna, ta dauki ‘yan mintoci ba tace komin ba itama, shi Kuma yaci gaba da maganarsa “Mu kwana lafiya, I will call you again.”
Ya ajiye wayar ya juyo kan Zuwaira yace “Kinga idan ba maganar arziki ta kawoki ba don Allah ki sarara min ga hanya ki fita ki ban wuri kaina ya dau zafi already.”
Ta sadda kanta kasa “Zuwa nayi in baka hakuri, don Allah da Annabinsa ka yafe min.”
Yace “Idan nayi hakurin na yau, sai kuma na yaushe, anjima, gobe ko jibi? Kuma ma hakurin me kike bani, mun riga mun saba, zaman auren kawai muke tamkar wasu jahilai.”
Ta muskutta “Ni dai nace ka yafe min ba don halina ba.”
“Me Kika yi da kike neman yafiyata, Ni a was Nike a rayuwarki don ban san matsayin da kika ajeni ba.”
Ta dago cikin hanzari “Ya zaka ce haka, matsayin mijina mana.”
Yace “To su Kuma abokan da kike dasu na waje matsayin me suke a gareki?”
Ta fara kuka” Ni fa wallahi tallahi ban taba tarayya da kowanne namiji ba, wadanda muke huldar business dinmu kadai ne muke communicating dasu.”
“Ni ban tambayeki kuka ba, to su din kuma muharramanki ne? Zuwaira ki ji tsoron Allah, ki sani komin dadewarki a duniya Zaki tafi lahira, Allah zai tuhumeki abubuwan da kika aikata a duniya. To wai tsaya ma tun farkon aurenmu nasan ke din mace harija, duk kokarin sauke hakkinki ki kan nuna ke ba a gamsar dake ba, tun a nan na fara tausayinki, bayan wannan ke din nan fa ban aureki cikakkiyar mace ba, for whatever reason hakan ya kasance gareki ban sani ba, that’s why ganin yadda kike huladarki da abokan naki yasa ni zargin.
A wancan lokacin mutuncin dake tsakanina da mahaifinki yasa na share, na danne zuciyata har addua na rinka yi kar Allah yasa in rinka ganin bakinki ko rashin martabarki, ba don haka ba da tuni mutuncinki ya gama zubewa a idona, ke kinsan virginity darajar diya mace ce amma na ci gaba da zama dake da halayenki na rashin da’a amma kawaicina da hakuri bai sa kin gyara ba, sai kika kara shiga harkar kawaye masu zugaki kina shiririta, kina zaton ba don su Khalifa sunyi kama dani ba Zan karbesu ne a matsayin ‘ya’yana?
Nace idan ma halink ne yau da gobe bata bar komi ba ai. Daga nan saboda daurewa yawon gindi kika je kika daure mahaifa wai ke karki haihu ki tsufa da wuri, kika kara samun lasisin yawon. Kullum cikin nasiha nike a gareki amma ko a jikinki, Zuwaira ban rageki da komi ba, ba rashin abinci ba sutura, ba rashin kudin kashewa, iyayenki na kokarinsu a kanki to ashe duk ba muyi miki gwaninta ba, kince kina son ki nemi na kanki na mara miki baya don nima ban son tauye hakkinki, kuma no matter how much muke baki, is good ki nemi na kanki din saboda halin yau da gobe, but sai kika zake in the process, ke kinsan wanene ni, ni ba mazinaci ba ne, Allah ya kaddaro min auren Rahima kin kasa kwantar da hankalinki sai shirme da hauka kike wadanda ba zasu hanani komi ba balle su sani illa ma ki Kara zubda mutuncinki a idona. But ki sani kin kaini makura, saura kiris in dau matakin da zai baki mamaki.”
Tayi kasake tana saurarensa, to me ya fadi Wanda ba gaskiya ba? Babu, tayi tsumi ta muzanta, to ai shi daman komi kake aikatawa Allah na ganinka da lokacin da zai kama ka a hannu…
Amma Allah ya sani da zuciya daya ta auri mijinta don tana matukar son abinta, amma ba a a nan gizo ke sakar ba, tun kafin ta auri Haseeb kawarta a boarding school ta fara bata ta in the process of lesbianism, ta saba a haka har suka gama school, sai kuma wani tsinannan saurayinta ya nemeta ba tare da sanin kowa ba, har iyayenta, tun kafin taga Haseeb.
A gaskiya tafi danganta lalacewarta da wadannan mutum biyun da suka taka rawa wajen gurbacewar tarbiyyarta duk ta taso da shagwabar nata, iyayenta sunyi kokarin gyara tarbiyyarta ta fandare ita ala dole yar gata, kuma yan uwanta kaf ba haka suke ba..
Ta kalli mijinta da wutsiyar ido taga latsar wayarsa kawai tunda ya gama mata magana, in banda sharrin shaidan wace mace ce zata sami miji irinsa tayi mishi rikon sakainar kashi? Wallahi ko personality dinsa kadai ya ishi mace jin sha’awarsa balle a Kai ga kyawawan halayensa, ba domin shawarwarin da Husaina ke bata ba da tuni ta daina abubuwan da take yi ta rungumi mijinta, to amma ko yanzun lokaci bai kure ba, but Kashi! Inda zata sami cikas dayane, wannan auren da dauko. Sai dai kuwa ta kadata tayi gaba ta bar mata mijinta idan kuma taking fita za taga sharri kala-kala, ba zuwa wajen boka balle Malam, Zuwaira bata bin malamai duk iya shegenta, wannan sai Husaina.
Tasa hanni ta shafi lallausar suman kansa “Kayi barci ne?”
Ya wani dago kamar wace ta cije shi, “Menene Kuma?”
“Na rokeka gafara ne banji kace ka yafe min ba .”
Na yafe miki Zuwaira Allah ya yafe mana gaba daya amma ki roki gafarar Ubanginki kan zunuban da kika dauka da niyyar ba zaki sake aikata kwatankwacin su ba, idan kuwa kinsan ba zaki bari ba, no need ma kiyi istigfarin don Allah ba abokin wasan kowa bane, ai kin gane?”
Tace “Wallahi har ga Allah ba zan sake ba, don Allah ka tayani addu’a.
Yace “Kullum cikinta muke, muma ajizai ne Allah ya yafe mana dukkan kurakurenmu.”
Tace “Ameen.’
Ya juya baya domin turaren data fesa hawa kansa yake, karfinsa yai yawa har ji yake kamat zaiyi amai.”
Ba da son ransa ba ya rinka tuna sansanyar kamshin turaren Rahima Wanda ya kama jikinta radam, turarenta har wani kashe jiki yake...bai gajiya da shakarsa..
Ta matsa kusa dashi ta shafa bayansa ta kira sunansa “Dakta?
Ya amsa
“Ni kuwa haihuwa nike so.”
Wata sabuwa inji yan caca! Ba tareda ya waigo ba yace “,To Ni ke bada haihuwar, da can Kuma nina hanaki? Ai kin fini sanin abinyi sai ki hada da addua.”.