NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ta kwantar da kanta a jikinsa ta sassauta murya “Ka taba ganin mace ta haihu ita kadai, yaushe rabon daka kusance Ni?”

Haseeb ya dafe Kai! Allah wadaran naka ya lalace, shi bai taba ganin mace maras kunya irin zuwaira ba, duk da ya saba da halinta na rashin iya danne maitarta, yau abin yai masa wani iri, ko don ‘yan kwanakin da yayi da Rahima ne, yana son mace mai kunya, yana jin dadin yadda take jin nauyinsa, mace mace mai kunya abin so ce, duk yadda taso da bukata sai an kai ga rarrashinta ta bar mijin da rawar jikin, Kai Allah ya shiryi Zuwaira, abinda akace kunya na daga cikin yankin imani.
Da taji ya Kyaleta ta kuma Kara rungumarsa tace “Kasan dai hakkina na kanka ba mai sauke min shi sai kai, kuma zaka rantse da Allah kwanaki ukun da kayi a wancan gidan haka kayi salin alin ba abinda ya wakana tsakaninku sai Ni don na nemi hakkina ka ja min rai?”

Cikin deadly voice yace “Nayi warning dinki daga yau idan zaki magana karki sake kawo min batun Rahima..
Ta marairaice ta narke a jikinsa “Afwaan ba zan sake ba. “
Ya dago ya kalleta tun daga sama har kasa yaji shi kansa kyamar kansa yake ji but wajibi sauke nauyinta da Allah ya dora a kansa, ya tashi zaune yace “Ji nan please je kiyi wanka, Kuma idan domina kike shafa wannan turaren don Allah ki canza bana so, ki tabbatar da kin teafe kitson attachement din nan, ki yanke wadannan akaifar da kika bari kamar ta masu cikin kare idan ba haka kuwa sai dai mu hakura da juna.”

Nan da nan ta amince “Wallahi dyk zanyi abinda kake so, amma ban dade da yin wanka ba sai na sake wani yanzun?
Ya gyada Kai “Manufata kenan, idan ba zai tuwwu ba okay my kwana lafiya.”.

Ta zabura ta duro daga Kan gadon ta fada toilet…..
Haseeb ya bita da kallo ya mike tsaye ya fuskanci alkibla ya daga hannayensa sama ya fara jero addua “YA Allah kasa yau ya zama mafarin shiriyar wannan baiwar taka saboda kai ka halasta saki amma kana kyamar yinsa, ya Ubangiji kar ka kaddareni aikata abinda idan nayi Al’arshinka zai girgiza, Allah ka karamin hakuri da juriyar zama da ita, ka bani ikon yin adalci tsakanin matana, Ya Allah ka shirya Mana zuriyyarmu idan zaka Kara Mana ka bamu masu albarka shiryayyu salihai masu shiryarwa, ka gafarta mana dimbin zunubanmu, ka yafe Mana baki daya.” Ameen.

Ya shafa kenan ta fito ta ganshi a tsaye, ta dauka ita yake jira, da sauri ta isa garesa ta kwantar da kanta bisa kirjinsa, yasa hannu ya rungumeta, ko adduar da yayi ne yasa zuciyarsa ta rage radadin tsanarta?
18/09/2020, 00:18 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
43

Kiran sallar farko ya zame jikinsa ya shiga yai wanka tareda alwala ya fito yai shirin zuwa masallaci, tashim duniya Zuwaira bata motsa ba hakan ya fita ya barta, ya nufi dakin yaransu ya tashesu suka yi akwala ya tafi dasu masallacin..
Har suka isar suka dawo bata farka ba sai juyi take a gado, yai mata tsaye saida yaga ta sauka ta shiga wankan ya Kyaleta, a gurguje ta gabatar da sallar ta koma gado taci gaba da barcinta, ya kalleta yace “Allah ya shiryeki.”
Bai tsaya jiran wata Mai aiki ba da kansa ya hadawa su Khalifa breakfast suka ci tare dashi, ya shiryasu ya kuma kaisu makarantar ya ajiye ya dawo gidan bai sake bi ta kanta ba ya koma falo yai zamansa.

Ya dauki ‘yar redio ya kunna, but sauraren kowanne programme ya gagara saboda daidai lokacin tunanin Rahima ya kutso masa, al’amurranta suka rinka masa yawo cikin kwakwalwa, ya saki wani dan murmushi, kasa daurewa yayi ya zaro wayar ya danna mata kira.

Ta rufe Qur’aninta kenan Kiran ya shigo ta daga ta sallama ta gaisheshi har da dan rusunawa kamar tana ganinsa.
“Ya kwanan su Aunty da Yara?” Ta tambaya .

“Lafiya kalau Ina Abdul?”
“An kaishi school.” Ta amsa a takaice ta kuma yi shiru..
Hhmmm bai san dalilin da yasa da yaji muryarta yake daburcewa ya kasa furta kalaman da ya shirya zai fada mata ba, and she’s not helping matters sai tayi shiru ta barsa yana kame- kame.

A nata bangaren kwarjinsa ke haddasa masa increased na heart beat wanda hakan ke sa ta kasa magana.
Yaji shirun zaiyi yawa ya gyara murya yace “Jiya bamu gama zancen mu ba.”
“Wane zance kenan?”
“Zan tuna miki on one condition, kin yarda zaki bani abinda nike so?”
Ta gyada Kai “In dai bai fi karfina ba insha Allah.”
“To baki ce komi ba, Kinga kifayen?”
Ta sake amsawa da “Na gani sunyi kyau nagode sosai but still Ina cikin duhu, rashin fahimtar ma’anarsu.”

“Zan miki bayani idan na shigo anjima kadan.”
“Ina ce a asibiti zamu hadu kawai.”.
Takaici ya kamashi, Lalle yarinyar nan bata kaunarsa, dubi yadda ya kwanta ya tashi da tunaninta a rai amma ji irin reaction dinta da ya kirata.”
Yace “Okay mu hadu a can din ba problem.”
Sai karfe hudun bayan la’asar ya kirata suna cikin hira dasu Hjy Fatima.”

Kamshinta kawai ya isar masa da sakon ta shigo office din nasa, ya juyo yana kallonta, taku daya ana biyu yaja ya tsaya a gabanta, yai niyyar embracing dinta, ko me ya tuna ya fasa, daidai lokacin aka kira wayarsa ta office, ya juya ya dauka ya fara magana. Tsawon mintoci Yana ta magana daga harshen turanci ya koma larabci, *Hal anta bi khair?* Ya tambaya ashe patient dinsa ne daga Riyadh yaji sauki ya murmure, Daktan ya ci gaba da magana taga zasu dauki lokaci, ta fita ta basu wuri, tana fita ta shiga ta yiwa su Hjy Fatima sallama ta koma gida.

A ranar kuwa Zuwaira ta kasa gane kansa, yayi zamansa a falo shida Yara har suka yi barci ya maishesu ciki ya dawo falon yaci gaba da latsar wayarsa..
Ba wani abu ke cinsa ba illa tunanin Rahima, zuciyarsa kamar ta fashe , wannan wane irin bala’ine?
Ya dace ya shareta dalilin abinda tayi masa tayi tafiyarta ta barsa but ya kasa daurewa why? Ya yanke shawarar tura masa sako but muddin ta gani bata yi responding ba bayan ya tona mata sirrin zuciyarsa zai kyaleta sai ta ne me sa don kanta.

Nan take ya rubuta mata *Lokacin da zaki karanta sms dinnan, ki tabbatar tunaninki ne ya addabeni, may be in kasance cikin murmishin da na kanyi duk lokacin da tunaninki ya bijiro min cikin kowanne yanayi a ko'ina nike ko me nike yi Kuma.

Bayan kin karanta warannan kalaman, ina fatar zaki fahimci matsayinki a gareni a yanzun da anjima, da har muddin rayuwa even if it’s for a blink of an eye. Kiyi murmushi domina yayinda kike ci gaba da hidimominki don zan kasance cikin tunaninki.*

Zuciyarta ta cika fak da murna da farin ciki duk da bai furta ainihin kalaman da take son ji ba wadannan ma kadai sun isa Mai hankali ya gane *So da Kauna * aka dunkule waje daya.
Fahimtar inda ya dosa yasa ta maida masa martani kamar haka:
Daga awoyin da muka rabu ina fatar ka sakani cikin ruhi da zuciyarka ya kasance ko rufe idanu kayi Ni kake gani cikin tsananin tunaninka da irin wannan ci da zuccin saboda nayi matukar maraicinka, ban ki a ce a yanzun Ina tare dakai cikin raina, zuciya da ruhi ba.

Ya rasa me zai ce da ita don dadi, hakika Rahima ta fahimci manufarsa fiye da zatonsa, ashe daman m shi take jira ya bara kafin ta tona nata sirrin zuciyar, me wayon tsiya ya Fadi a fili yana murmushin farin ciki..
Ba bata lokaci ta sake aika mata Hakika nayi maraicinki kamar in janyo sauran time din da zamu kasance tare, ashe kewar masoyi ukuba ne..
Ta maida masa reply Tawa kewar ta zarce taka Ya Haseeb.
Karki damu zamu magance su duka, sai ince sai mun hadu..
Ta rubuta Waiting for you with pleasure.
18/09/2020, 15:48 – Anty saliha:…RAHIMA..doc by jami

44

  Ranar d zai koma gidanta Rahima ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kara tsabtacce ko'ina cikin gidan ya ci gyara tamkar ranar aka kawo ta, komi yayi fes, ta bangaren abinci ta shirya masa light food ta dafa masa mai suna "Muhammas' abincin larabawa ne yana yanayi  da cous-cous, hade da farfesun kaji, a gefe ga dambun kifi, banda drinks na kwali, ta hada masa lemon tatacciyar abarba da gwanda kana ta saka kwalbar favorite drink dinsa 'Blue fruit cikin fridge yai madaidaicin sanyi.

Kwanaki biyun da yayi gidan Zuwaira sun bata damar canza tsarin bedroom dinsa ta kawata dakin barcinta da nasa da furanni masu kyau, daga gefen window ma ta aje wasu tukunyar live flower dake fitar da natural kamshi saboda iska da hasken rana dake taimaka musu.
Sabon duvet ta baza a saman gadonsa,banda soft blanket din dake gefe koda ana bukatar lullube jiki idan sanyi yai taso, ta feshe gadon da turare Mai suna seduction kana ta feshe dakin gaba daya da Natural fresh air (pot pouri), ta kunna Air condition sannan ta koma ga suturar sa da ya saka ya cire kafin barinsa gidan, alreday an wanke su tas an goge, jerasu kawai tayi cikon wardrobe dinsa, da kanta wanke inner wears dinsa ta goge ta feshesu da turare suma ta jera komi a mazauninsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button