NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

A gurguje ta leka asibiti ta basu Hjy Fatima hakurin ba zasu ganta da yamma ba ranar, ta koma gida ta ci gaba da hidimarta tsabtacce jikinta, al’adarta ce duk karshen wata bayan ta Kara period ta kanyi shaving pubic hair dinta da na armpit saboda koyi da addininmu da inganta tsabta, to yau ma hakan tayi.
Uwale ta rangada mata zanen shuku suka zuba har dokin wuyanta saboda gwargwado tanada yalwar suma ta kame da ribbon,tanada son kumshi sosai, shima Uwalen ta taimaka ta d’afa mata celotape da aka yiwa designs masu kyaun gaske kafa da tafin hannu sannan aka bi da natural lalen da aka kwabashi hade da turarensa tun safe don yai saurin kamawa, a takaice ranar take amaryar zan-zan, ta zama taba ka lashe.

Bayan ta ba Abdul abinci yaci ya koshi, sunyi sallah tare tunda baban nasa bai iso balle suje masallaci, hakan take yi duk ranar da yaron bai samu zuwa masallacin ba sai tasa ya rinka binta suyi sallar tare yana gani da koyon yadda ake gabatarwa.
Suna idarwa tayi mishi wanka ta saka masa ‘yar pyjamas sa ta yara sannan ta shiga tayi wanka ta fito ta kimtsa kanta, moderate kwalliya tayi da wata atampar Holland da aka dinka mata simple gown wanda tayi mata das tayi kyau da kirar jikin nan nata, tayi cas! Ba a batun kamshi a tattare da ita don ita ma’abuciyarsa ce, ya riga ya kama jikinta radam.

  'Yar muryar Abdul dake wasa a falo taji yana fadin "Abba oyo-yo."

 Ta fito daga bedroom dauke da murmushinsa "Barka da isowa." Ta fadi cikin ladabi.

Ya mika mata hannun damarsa “Assalamu Alaiki wa rahmatullah wa Barakatuhu.”
Cikin jin kunya ta mika masa nata hannun kana ta amsa sallamarsa, ya dan matse hannun kadan kana yace “Malamai sun mana koyi da yin hakan bayan yada sallama, yana kara shakuwa tsakanin ma’aurata. So ya gidan?”

Ta maida masa sallamar sannan tace “GIda kowa da komi lafiya, ya aka barsu Khalifa?”
“They are Okay alhamdulillah.” Ya amsa yana wasa da Abdul dake ta zuba surutu..

Sun jima da gama cin abincin amma bai daina santin farfesun kaji da dambun kifin na, ta rinka tsokanarsa tana dariya.

 Tsaye ta iskoshi cikin bedroom dinsa bayan ta kimtsa falon, ta taka a hankali zuwa bayansa ta kwantar da kanta tace "Menene naji kayi shiru?"

Ya juyo ya riko hannayenta yana kallonta, ya girgiza kansa “Kin canza min komi na rayuwata, me zance?”

Ta saki ajiyar zuciya “Bana bukatar fitowar wata kalma daga bakinka muddin na faranta ranka, zuciyata cike take da farin ciki.”

Ya sake girgiza kai “Ba zaki gane bane Rahima, but a bar maganar for now come here…
Da kalaman da yayi fada mata, but as long as tana kusa dashi yana kallon yadda tayi kyau ta tsaru tamkar wata ‘yar tsana ba zai samu natsuwar wasu surutai ba, ya kama hannunta guda ya rinka kallon desing din lalen da yai ram a tafin hannunta, ya kai hannun bakinsa yai sakar mata kiss, ta lumshe idanunta, bata ankara ba taji ta bisa shimfidarsu, kamshin turaren seduction, da kamshin turaren Haseeb mai suna Privacy suka hade da wanda ta shafa Eternity suka cakude gaba daya, ya rungumeta tsan-tsan tamkar wani yace zai kwace mishi ita.
Kamar a majigi suka rinka iyo cikin kogin so da kaunar juna, sai rada mata yake Uhibbiki Kaseeran cikin kunnenta, ta bude idonta da kyar ” Me hakan ke nufi?
Cikin shauki ya fassara It means I love you so very much Rahima, so da kaunarki sun shige min cikin jinina kamar yadda kwayoyin cutar nan da basu da magani kan shiga cikin jinin mutum.”
“To ni kuma in ce me Ya Haseeb? Saboda yadda nike jinka na rasa yadda zan kwatanta soyayyarka cikin zuciyata sai godiyar Allah nike dare da rana domin kullum adduata ya bani mijn da zan so ya so ni da zuciya daya ashe kaine amsar addu’ar.
Nan kishi ya motsa yace “kina nufin baki taba son wani ba harda marigayi?”
Ta danyi shiru tukunna kafin ta amsa “Na so Rabiu, irin son ‘yanuwa ko kuma ince irin miji da matan da suka tsinci kansu a wannan matsayi kaddara Allah ta gitta amma ban taba jin irin wannan tafasar kunar zuciyar ba sai haduwata da Kai.”

Ya kara rungumeta “Iam sorry dana bude miki old wound, na kasa daurewa ne.”.
“Na fahimceki Yaya and iam glad da kayi tambayar coz a karo na farko bayan rasuwarsa nayi maganarsa ba tare da zubda hawaye ba sai deep sad feelings, ko ba komi Uban dana ne, shi ya fara nuna min so da kauna har in mutu ba zan manta dashi ba.”

Ya nisa “Yes hakane, karki manta nima danuwana ne da muka shaku kwarai, akwai wata irin kauna tsakaninmu da Allah ya dasa Mana, I really missed him, kuma wallahi ban taba tunanin zan auri matar da ya aura ba, but da Allah ya shiryo mana hakan kullum adduata garesa yasa ya huta, Allah ya sanyaya masa, Ina rokon Allah yasa zaki haifa min wani Rabiun bada jimawa ba.”

Tace “Idan ma ba a samu ba ga Abdul Nan.”.
“No Abdul -Haseeb dana ne da yaci sunana, yanzun Rabi’u nike so yaci sunan babansa.”.
Tace “To Allah ya amince ya tabbatar mana da khairan.”

Saida gari ya waye Rahima tayi maganar kifaye yace “Ya dace ki fahimci dalilin da yasa na baki kyautar kifayen nan Rahima.”
Tace “Hhmmm ni ban fahimci komi ba Kai dai za kayi min bayani Dakta.”

“To naji, ya jikin kifi nan tarwada yake?”

Cikin rashin fahimtar inda tambayar ta dosa ta amsa “Tarwada ita kullum jikinta tsantsi da damshi ne ko tana cikin ruwa ko akasin hakan.”
Yace “Yauwa, ya jawota ya zaunar da ita bisa cinyarsa kafin yaci gaba da bayin “To Kinga kamar yadda halittar jikin kifi tarwada take haka Allah ya halicce ki kema exactly, kullum cikin ni’ima, duk namijin da Allah ya nufa da auren irinku to shi fa baida sauran burin wata ‘ya mace a duniya, kune irin matan da ake Kira “Sa’ida’, ba ruwanku da shaye-shayen magunguna da wasu matan keyi, ko kinsha ko baki sha komi ba mijinki zai matukar gamsu… Kinji reason dina na bada wannan kyauta, kuma daga yau duk gift din da zan baki wajibi ya danganci ruwa.. don nima kina ni’imtani, kin fahimceni, yanzun sai batun kyauta ta.”

Maganganunsa sun sa kunyarsa ta dawo mata sabuwa ta rufe idanunta, ya banbare da kyar.
Cikin shagaba tace “Don Allah ka rabu dani.”.
Yace “Ai kuwa baki isa ba, alkawari ki kai min wajibi ki cika sa.”
Tace “To me kake so?”
Ya amsa “Sai kin kalleni zan fada miki.”
Tana kallonsa yace Yourself

Hhhmmm wai don Allah da gaske ne da mutane ke cewa yawancin Doctors maza basa jin kunyar fadar magana? Saboda ita ga nata likitan nan Yana ta rikita mata kwanya da surutan da ko a mafarki bata yi zaton zai iya Fadi ba.

Dr Haseeb da Rahima sun ci gaba da gudanar da rayuwar aurensu gwanin sha’awa, aka bar masu fadin ya za ayi wa ya auri matar kaninsa baki ya mutu sai sha’awar su suke.

Sati biyu cif Dakta ya tabbatar da warkewar patient dinsa Hjy Fatima don haka ya rubuta musu sallama. Da kansa ya daukesu zuwa gidansa suka kwana guda sannan suka koma Maiduguri.

Ba su tafi ba Saida suka tabbatar zumunci Mai karfi ya kullu tsakaninsu tareda da alkawarin ziyarar su day zaran ya samu sarari inji likitan, sun rabu suna begen junan

Hutun da Rahima ta dauka ya kare sai batun komawa aiki, Daktan ya daka tsalle waje guda yace ba zata sabu ba Wai bindiga a ruwa, yadda ta shagwaba shi yana bukatar attention dinta sosai amma yace ta nemi sana’ar da zata yi don bai son ta zauna hannu sake tana jiran kullum sai anyi Mata.
Ta nemi shawarar iyayenta suka amince, ita da ‘yaruwarta Maryam suka hada jari suka aikawa Hjy Fatima ta fara turo musu turarukan wuta, na jiki, dana tufafi, har dasu lapayya. A sannu Ubangiji yasa musu albarka, kasuwanci ya habaka ya karbu wajen matan manya sai hamdala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button