
Kwatsam Zuwaira ta tada fitinar sai dai a hade su gida daya saboda kullum cikin zargin mijinsu na mata rashin adalci take, kuma wai ma Rahimar bin malamai take a nata tunanin ba haka kawai miji ke rawar jiki da ita ba.
18/09/2020, 19:13 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by jami
45
Tun daga Kan Hjy Kaltume, Maryam da Iyayenta babu wanda ya bata goyon bayan ta amince da bukatar Zuwaira ba balle shi kansa uban gayyar da yace duk abinda zata ce taje ta dade bata ba amma bai yarda tsarin ba sam.
Rahima tace a bata kwana bakwai tayi istikhara ta roki Allah zabi tukunna. Sarai yasan halin gimbiyar tasa don haka yace Kar ma ta san ran zai canza ra’ayinsa ya riga ya yanke shawara.
Ba Rahima bata amince da shawarwarin da aka bata bane, no bata san abinda gaba zata haifar ba, zaman nasu khairi ne ko sharri Allah kadai yasan gaibu, dalilinta kenan na dagewa tayi adduar saboda zuciyarta ta kasa tsayuwa waje guda.
Bayan satin taji ta natsu ta amince da batun hadasu din sai dai ta dage da adduar neman tsari daga dukkan sharri da fitinar dare da rana.
Tana tunkarar maigidan da maganar yai tsalle yace ba zai taba hadasu ba, ta kafe kan ra’ayinta ya kafe kan nasa taron taurin kai.
Ranar tana zaune taji sallamar su Umma da Hjy Kaltume Daktan na biye dasu ta girgiza Kai ta tabbatar shi ya dauko su kan batun nan da yaki ci yaki cinyewa.
Bayan ta gaishesu ta kawo musu abin motsa baki, bata bari sun fara magana ta tambayesu “Yaya karata ya kai ko?”
Hajiya Kaltume ta gyada kai “Har yanzun kaina a daure yake Rahima, na rasa dalilin da yasa kike son dauko fitina da hannunki ki kawi cikin gidanki, me ye zafi haka?
Ta sunkuyar da kai “Hajiya baku fahimce nu bane shiyasa kuke tunanin hakan.”
“Ina fa zamu fahimceki tunda ba muyi wayo da hankalinki ba.” Ummanta ta fadi a fusace.
Ta kalleta a raunane “Afwaan Umma haka nike nufi ba.”
Hajiya ta kalli Umma “Saurara mata tayi Mana bayani watakila ta fi mu gaskiya.”.
Sai a nan Haseeb ya tanka yace “In dai itace yanzun zata kashe miki jiki da lafuzanta ki amince da manufarta ko banza ba Kya ganin laifinta.”
Rahima ta kallesa “Shikenan Yaya bari in musu bayani idan basu amince ba wallahi na hakura, amma kafin nan ka fadu hujjojinka na rashin son hadamu din.”
Ya gyara zama “Hujjoji?, Halayyen Zuwaira ai ba boye suke ba, kuna nesa da juna ma ban tsira da korafinta na Ina rashin adalci tsakaninku ba, fitinar yau daban ta gobe daban Wanda da ina biye mata da tuni mun rabu.”
Rahima tace ” Kuna jinsa ko? To ai ni abinda ban son ya faru kenan, da can din ai da halinta baka rabu da ita ba sai bayan aurena? Ko Ni ce zanyi zargin dalilin wata ka rabu dani, daga nan Kuma kulalliyar gaba ta kullu tsakanina da yaranka har abada saboda mai zurfin tunani ne zai gane cewan gajiya kayi da halinta ka Kai makura ne silar rabuwarku, batun danne hakkinta da take yi ma zaman mu a tare zai sa ta gani idan ana zaluntarta din, Kai kuma za a rage maka yawan zirga-zirga tunda iyakinka na natse waje daya hankalinka zai fi kwanciya.”
Umma ta daka mata harara “Ai ba dai iya magana ba ‘yar ka iya, shi ba wadannan matsalolin suka dame sa ba.”
Yace “Ta fa san duk abinda nike gudu Umma.”
Hajiya tace “Rahima zaki iya zama da Zuwaira da halayyenta?”
Ta gyara zama tace “Sai maganar halayye muke Hajiya amma bamu tsaya munyi nazarin shin wane irin hali Aunty Zuwaira ke dashi ba kamar yadda masu ilmin sanin halayyan dan Adam suka kasa halayyen mutum har kashi uku.
Na farko akwai halayyen da basu gyaruwa kwata-kwata, misali irin halayyen da mutum ya gada daga iyaye ko aka haifesa dasu, to kowa yasan halayen Aunty Zuwaira ba gado ba ne don kowa ya shaidi martabatar iyayenta da sauran zuriyyarsu, ba kuma wadanda aka haifeta dasu bane.
Na biyu shine halayyen mutum da ake iya gyarawa Amma sai an Sha wahala sosai wajen yin gyaran, irin wadannan halayyen mutum kan tsiri yinsu ne a kan da dole ma’ana wani dalili ya tilasta wajen adopting canza original halinda aka san mutum dashi. Misali irin yanzun da yawancin maza kan bar wa mace takakihun hidimar gida, yau da gobe darajar sa na iya zubewa a idonta, ta daina ganin girmansa sabanin yadda take mutuntashi da can.
Na uku mutum Kan dauki halayyan da ba nasa ba da rana tsaka ko dalilin hulda da abokan banza, ko haka kawai ya halin wani ya rinka burgesa, irin wadannan gyara kawai suke bukata ba kuma za a wahala wajen gyarawan ba.
Ya kada kai yace “To munji mai falsafa cikin wadannan kashin da kika zano da wanne kika danganta Zuwaira dashi har kike shaawar zamanku tare? Kenan kina ganin zaki iya gyara halayyenta?
Rahima ta nisa “Sanin gaibu sai Lillahi, Ina adduar sanadiyyar zaman tare ta canza halayen nata.”
Hjy Kaltume tace “Da kyau Rahima haka ake son musulmin kwarai ya sowa kansa abinda yake so wa kansa, kin burgeni.”
Umma tace “Hakane Hajiya nima banki naki ba, tashin hankaline nike gudu.”
Rahima tayi murmushi “Kamar kin manta da halin diyar taki Umma, fitina ta kan kare ne Kan Wanda ya jawota, Ni dai goyon bayanku nike bukata sannan ku tayamu addua.”
Hjy Kaltume tace “Shikenan Allah yai miki albarka ya cika burunki na alkhairi.
Daktan ya wani kalleta yace “Naji duk kun goyi bayanta ne, to ni kam ina nan kan bakana, idan Kuma kun matsa na amince to Kar ayi kuka dani idan wani abu ya taso nan gaba “
Mahaifiyarsa tace “Wannan ne baka isa ba, ka tara ‘ya’yan mutane kace ba ruwanka.”.
Rahima tace “Rabu dashi Hajiya naji sharadinsa na dauka Allah ya kama mana.”
Ya sake kallonta a fusace yace “Yanzun sai ki fadi inda kuke son ku zauna tsakanin Dorayi da Galadancin.”
Ta girgiza Kai “Ba ni da wannan matsayin, Kai da Aunty Zuwaira kuyi deciding Ni ‘yar amshin shata ce.”.
Ya juya gasu Hajiya “Kunji amsar ta ko?”
Hajiya ta gyada Kai “Laifi kake son Dora mata dai amma gaskiya ta fada, tabbas zabi na gareku, ta ba Zuwaira girmanta da Kai kanka.”
Da yaga ba zai samu goyon bayan da ya zata ba dai ya amince cike da fargaba.
Yayi deciding kara gyara gidan da Rahima take saboda akwai filin da za a dora wani ginin sosai.
Ba bata lokaci aka fara aikin sake tsara gidan Daktan don zaman iyalinsa.
19/09/2020, 13:57 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by jami
46
An kammala komi na gidan Dakta har gashi Uwargida Zuwaira da tawagarta sun rakata tarewa a nata bangaren.
Yanuwanta da suka san mutunci sun shiga sun gaisa da Rahima aka taba barkwanci suka musu addua suka tafi, kawayenta kuwa sai shirmen da suka saba, hatta da falon Zuwaira Saida suka leko yanayin tsarin da Rahima ta yiwa nata suka dawo suka kwatanta irinsa, suna yo suna yar da maganganu don dai neman jidali.
Bata kula ba balle tasan Allah yai ruwan tsironsu, to Rahima a banza take miskila?
A wannan ranar Zuwairar ke da maigidan yadda ta shirya saboda Wai ta nunawa Rahimar ita ke da gida da maigidan ma gaba daya, to wace take yi dominta bata san arziki na bori ba.
To idan ba shiririta da neman zubar da aji irin na Zuwaira ba, kowaccensu sashen daban, sai ma kaso sanin halinda yaruwa ke ciki ne zaka leka inda take, sai kuwa idan sun hadu a general parlour na gidan, kowacce tana da masu aikinta to me ye na hana Kai sukuni?
Dawowar su Zuwaira yasa yaranta suka Kara shakuwa sa Rahima saboda tana jansu sosai a jikinta, ta hanyar kulawa da duk bukatocinsu ba gajiyawa, ga kokarin tarbiyyarsu da take yi tareda danta, to jama’a ko yaro yasan mai son shi.