NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Zuwaira bata kaunar kusancin yaranta da Rahima ko miskala zarratin, da taga tayi kokarin rabasu ya faskara sai ta shaidawa abokiyar shawarar nata. Husaina ta buga kirji tace “Zauna ki saki baki galala kamar wata sauna bayan ta mallake miki mijin ta hada da ‘ya’yanki kina zaune sokoko ta mallake zuciyar yaranki tas, an fada miki da bakin hura wuta wannan yarinyar ke zaune a gidan Nan?”
“Da alamun kamshin gaskiya a batunki Husaina, nima zargina kenan don wallahi ko kaffara ba zanyi ba, ba haka kawai Dakta ke rawar jiki da ita ba, ke baki ga yadda take juyashi ba fa, Daktan da bana ganin tsadadden murmushinsa sai na sha ruwan dala amma ko waya yake da ita haka zaki ga yana wani rausayar da Kai Yana zuba murmushi sai kace wani sick lover boy.”

Husaina ta kyalkyace da dariya tace “To ai ba murmushinsa kadai ba shi kanshi tsadadden ne Zuwaira, yanzun dai meye shawara?”

“Kinji kuma, ke din dai nike saurare.”

Husaina tace “Ya zanyi dake yanzun,kince ke ba zaki shiga malamai ba, to ki zauna ta saki a tafin hannunta ta murza ta juya son ranta, mu dai idan da malamai da bokaye a duniya mun gi karfin tsara balle irin wancan da aka dauko miki, ke Kika yi sake tun farko amma ai ba ajinki ba ce.”

Zuwaira taja dogon numfashi “Ai yanzun dole mu san matakin dauka that’s why na neme ki.”
“Karki samu damuwa ‘yaruwa, kin yarda ko wane irin taimako na kawo miki zaki yi amfani dashi ko?”

“Me zai hana kuwa Husaina shakkun me kike?”
Husaina tace “Ai dole in jinjina kar kisa in kashe kudina a banza alhalin kin san samun su da wuya.”

Zuwaira tasha mur tace “Ke fa problem dinki kenan in dai batun kudi ya taso alhalin ni Ina kashe miki kowacce irin lalura ba tareda jin kyashin komi ba, ke kuwa in dai za ki yi min Abu sai kiji tamkar naman jikinki zaki diba.”

Nan take Husaina ‘yar bariki ta share wannan batun cikin dabara tunda tasan gaskiya aminiyarta ta fadi tace “Wasa fa nike miki, amma da gaske kinsaj business din mu yaja baya Kuma mijina ba irin naki bane da yake sakar miki dala kina fantamawa yadda ranki ke so, nasa Dan banzan makon tsiya, hannun nan nasa a dunkule tamkar na “yan dambe.”

Zuwaira ta tuntsire da dariya “Oh sharri ma za kiyi masa Kuma? Ai kuwa Yana kokarinsa shima.”..
Ta tabe baki. “Me Kika sani game da mugun halinsa, ke ni fa auren ma na gaji har na nemi ya sauwaka min, in gutsire igiyar auren in yi gaba in sami Wanda ya dace dani.”

Ta zaro idanu “Ke Husaina ki rufaea kanki asiri, Ina ke Ina wani rabuwa da mijinki yanzun, wa zai wani aureki yanzun bayan ga ‘yan matan Nan ma suna yawo a titi a mashinshini?”

Ta gyada Kai “Ai da kika ganni da agenda ta, na riga na shirya komi jiran lokaci nike in gabatar miki..”

“Toh! Al”amarin ba sauki kenan to Allah ya nuna mana alkhairi.”

Tace Amin “Bari inyi azama Kar Malam ya fita sai kin ganni.”

Tsakanin matan Daktan biyu zama yaki dadi,ta kowanne bangare Zuwaira bata da dama. Matsalar farko da Rahims ta fara karo da ita daga uwargidan nata itace gasa, Zuwaira irin matan nan masu shegen gasa, duk abinda taga Rahimar tayi sai ta kwaikwaya, ko silifas ta lura Rahima ta canza itama saita saya, balle a kaiga su kayan jiki ko na gyaran gida.
Wasan wasa rashin mafadi, gasa idan ba na nuna bajinta wajen bautar Allah bane ya zama shirme.

A ka dawo Kan abinci, a kullum mai aikin Zuwaira na yaeon gulma sa sunan tana zuwa wajen Uwale ne amma su sun San yar leken asirin uwardakinta ne, duk abinda yazo taga ana girkawa a sashen Rahima zata nade taje ta fesawa uwardakinta musamman idan Daktan wajensu yake, ita Kuma ranar nata girkin saita wanke tukunya ta kwaiwayi irin Wanda su Rahimar suka yi ta sake dafawa. Sai ayi rashi dace, Wanda akayi dominshi ba zai ci ba, Zuwaira ta fara bala’in hatta abincin ta ya daina ci sai na Rahima.

Tunanin bai kawo mata dalilin rashin cin bai rasa nasaba bai dade da cin irin nau’in abincin ba kazaliza method da aka hada ma ba guda ba.

Rahima ta gaji ta yanke shawarar aikawa Zuwaira ko me ta dafa. Uwale ta kalleta galala tace “Ni fa kina bani mamaki, yaushe ne Zaki yarda da kishiya har dai wace bata kaunarki har da batun Kai Mata abinci? Kin san ba zata ci na saidai ayta asara kawai.

Rahima tace “Uwale kenan Ni ban dauki Aunty Zuwaira kishiya ba, abinci kuwa ko taci ko Kar taci na sauke nauyin da Allah ya dora min matsayinta na makwabciyata.”

Ta rike haba “Makwabciya kuma Hajiya, ina makwabciyarki itace Hjy Shafa’atu mai shigowa wajenki din nan?”

Rahima tace “Makwabta sun kasu kashi uku ne Uwale, akwai mai daraja ta daya, ana nufin musulmi danuwa da kuke da danganta da juna
Makwabci Mai daraja ta biyu shine wadanda baku hada komi amma Allah ya hadaku zama unguwa daya, ka zo , na zo kamar ita Hjy Shafa da kike batu..
Mai daraja ta uku shine makwabcinka da ba musulmi ba.

To Kinga zan iya Kiran Aunty Zuwaira makwabciyata Mai m daraja ta daya kasancewarta musulma, ga Zumuncin dake tsakanin yaranmu, ga shi muna auren miji daya, muna zaune karkashin mutum guda, ko da a ce ga dakina ga nata ne sunan mu Makwabta Uwale.
Tunda hakan ne wajibi a garemu mu kyautatawa juna don gudun fushin Ubangiji mu Kuma tsira daga cikin mutanen da Allah ba zai karbu tuban su ba matukar sun mutu basu gaggawar gyarawa ba, shin kin san cewan an ce daidai da abinci mai kyau makwabci ya dafa ya ba makwabcinsa Kar ya cinye shi kadai?”

Uwale ta gyara zama “Oh gaske naga baki damu da wulakancin da take miki ba kullum idan kin shiga gaisheta, har a zuciyata nace ko dai tsoronta kike ne? Kuma ga wannan kwaikwayon naki da take yi kullum..

“Abu Mai kyau mutum keyi har wani ya gani ya yaba ai, inda taga mummunar abu nikeyi ai ba zata yi ba komin gasar ta kuwa. Bayan haka sanin nauyin da Allah ya dora mana a Kan juna yasa nike share wulakancinta, inyi biris da shirmen ta sabida nasan abinda nike kwadayi, itama rashin sanin ko biris da sanin yasa tayi sakaci shaidan yai rinjaye a kanta amma Ina adduar Allah ya ganar da ita, muma ya Kara mana fahimtar.
19/09/2020, 18:21 – Anty saliha: ..ˆRAHIMA..doc by jami
47

Uwale tayi ajiyar zuciya “Ameen Hajiya, gaskiya zama da mai ilmi babban nasara ce a rayuwa saboda karuwar da mutum zai yi, yanzun gashi na karu da sanin abubuwan da tunda nazo duniya ban sani ba, dole in kara himma a makarantar islamiyyar da na shig, amma Hajiya taimaka ki fada min su wanene Allah ba zai amshi tubansu ba idan suka rasu suna aikata sabon da suke yi basu bari ba?”

“Uwale nima ilmin nawa cikin cokali ne, amma yanada kyau komin kankantar ilmin mutum ya sanar da wadanda basu sanin ba suma su amfana sai Allah ya baki lada ya kuma kara bude miki kwakwalwar ki kara ilmantuwa don kiji dadin yadawa jama’ar musulmi.
Wadannan mutane bakwai da malamai suka yi mana bayani sune na daya shine Mai bata hakkin makwabtaka, na biyu masu yin luwadi, na uku wadanda suke matse al’aurarsu har sai maniyi ya fito musu, na hudu masu saduwa da dabbobi, na biyar namijin dake saduwa da matarsa ta duburarta, na shidda Wanda ya hada diya da uwa yana saduwa dasu, (irin bala’in da yai yawa yanzun cikin al’umma, uba ya rinka neman diyat da ya haifa) na bakwai mai yin zina da matar makwabcinsa.”
Uwale ta jinjina “Ashe aiki na gaban rago bai zo ba balle ya wuce, wallahi duk ilahirin jikina ya mutu likis, Lalle muna da sauran aiki jawur, in hakane kuwa Allah kadai yasan ladan da kike kwasa kin barmu baki sake sai dai mu take ciki da abinci mu koshi, kwanya ta toshe da miyar kuka da ruwan goro.”
Rahima ta kyalkyace da dariya “In don wannan karki samu damuwa tunda muna da likitan kwakwalwa, ya bude ya kwashe miyar.”
Ta kwalo ido “Rufan asiri Hajiya na koya a hankali.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button