
Ta mike “Naga idan na biye miki ba zani gidan Shafa’atun da nayi niyya ba, bari in hanzarta kafin maigidan ya dawo yace ya fasa barin fitar.”
“To a dawo lafiya Hajjaju.”
Ta saka hijab dinta har kasa ta nufi sashen Zuwaira tukunna, ta tsaya ta rinka sallama shiru Kuma tasan tana ciki tunda ga motar ta nan. Al’adar ta kenan da duk zata fita zata shaidawa Makwabciya, kazalika idan ta dawo don gudun faruwan wani abu ga Kuma sauke hakkin zama tare, ta juya ta tafi abinta.
Ko awa guda bata yi ba ta dawo gida saboda sam Daktan bai so ya dawo gida bata nan duk runtsi, tana matukar gudun zuciyarsa.
Bata yi fushi ba data dawo gida ma ta sake shiga wajen Zuwairan shima tayi sallamar shiru
har ta juya taji an bude kofar falon, ta dawo ta tsaya “Sannu da Aunty, daman fita zanyi na leko mu gaisa in fada miki but har naje na dawo ma.”
“Oho ai banji knocking ko sallamar naki ba ina cikin toilet ina wanka.”
Sai a lokacin Rahima ta bita da kallon yadda ta fito ba riga a jikinta sai towel data ratayo a wuyanta, ta jike gashin kanta sharkaf da ruwa har tana wani girgizashi ruwan na fantsamawa Rahima a fuska.
Tace “Ayya tunanina bai kawo hakan ba ai..
“To ya na iya ai nima wankan dole ce ta kamani yanzun, ni wannan hidima na Dakta ta fara isata.”
Rahima ta wani kalleta ta sakar mata matsiyacin murmushinta tace “Ashe daman ke kika koya masa haka Aunty, da na sani ai da tuni na kawo kararsa wajenki don ni din raguwa ce.”.
Zuwaira ta zuba mata wata uwar harara tare da tsuki gaba daya ta juya ta rufe kofarta garam, ita kuma ta karisa sashenta tana dariyar wautar Zuwaira, a tunaninta don ta nuna tana tare da miji zai daga mata hankali ko da ace gaskiya ce balle tasan ba hakan bane, ko ce mata akayi jima’i kadai ne jigon rayuwar aure oho.
Ba wani dadewa Daktan ya dawo, bayan sun dan taba hira take tambayarsa ko ya leka Hajiyarsa?
Ya amsa “Sai zuwa dare in Sha Allahu.”
Tace “Dazun dana kirata a waya naji alamar bata jin dadi ko ta gaya maka?”
“No kin san ba zata fadi ba sai dai mutum ya fahimci akwai damuwar.”
Ta kallesa, fuskar nan a murtuke, maganar da yake yi dai kace tilas sai kawai tayi dif itama, to ta riga ta lakance sa da zaran miskillancin nasa ya taso ko yana cikin bacin rai ta lura mood dinsa ya canza ta kan ja jikinta sai ya nemeta.
Shirun da tayi kuma bai masa dadi ba ya kalleta ya kau da kai, ya sake juyowa ya jefo mata tambayar “Rahima me ya faru tsakaninki da Zuwaira take fada min surutun wofi?”
Kunji kuma wani daukakkiyar, ba dai mganar da suka yi ne dazun ta zama abin korafi ba….
Da yaji bata tanka ba, ya cire glass dinsa, ta dago ta kasa kallonsa cikin kwarar idanu, ta juyar da Kai gefe yace “Ba ki ce komi ba.”
Tace “Saboda ban san amsar bane tunda a sanina ba muyi fada ba just magana ce tayi na bata amsa ko ance wani Abu ya faru beside hakan?”
“Look Rahima shirmen nan na guda tunda kuka dage zaku zauna tare na amince dole and you know how much I hate the idea amma Kika nace gashi nan yanzun kusan 6 months kuna tare ba zaman lafiya balle a samu piece of mind da kike ikrarin za a samun.”
“Ni fa har yanzun ban fahimci manufar maganganun ka ba, karata ta kawo ko me?”
“No, na dai yi zaton sanin halin Zuwaira da kika yi zai hana biye mata shiriritar ta.”
Ta danyi murmushi “Idan ranka ya baci afwaan ba za a kara ba. Kamar yadda na fahimci halinta tun ranar dana fara ganinta, na lakanci tana cikin mutane extrovert, wadanda masu sanin halayen Dan Adam suka ce yawancinsu akwai su da shishshigi, karancin basira, wasu su hada da karya da kwadayi, son shigewa gaba kan al’amurra ko wanda bai shafesu ba, su Kan nunawa jama’a sun san komi irin yadda take nuna min, ni Kuma idan naga zata kureni sai in nuna mata ba hakan bane, nan muke samun tangarda. ..
Yace Fahimtar banbancin halayenku ita mai yawan surutu ke Kuma introvert nasan ba wani dadin zama za kuji da juna ba.”
Rahima tace “Ni kuwa sai Ina ganin har ta fara canzawa, cikin dabi’unta marasu kyau na lura sun ragu sosai. Ka dai ci gaba da yi mana addu’a wata rana sai labari l.”
Ya nisa yace “Gaskiyar Kuma nima na lura da hakan but na kasa accepting cewan zata canza, Allah yasa ta dore.”
Rahima tace “In Sha Allahu, duk ranar da Allah ya ganar da ita influence din kawayenta ba alkhairi bane zata natsu.”
19/09/2020, 22:40 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by jami
48
Dakta yai shiru yana kallon matarsa yana yaba halinta cikin zuciyarsa.
Hakika yaga canji wajen Zuwaira, tun yana mamaki har ya daina yaci gaba da sa ido yana lura da dabbin dabi’un data bullo dasu, misali gabatar da sallar asubah ba tareda makara ba shine babban canjin da yai masa dadi a ransa,ta rage yawo kusan rabon da tace zata bukin kawa ko aminiya ya manta, business din ma yayi sanyi ba kamar da ba, yaranta suna samun kulawarta sakamakon ganin irin kaunar da Rahima ke yi musu da yi musu tarbiyyar kwarai, shi kansa yasa mata dokar hana kaisu ko’ina da sunan a barsu can, sai dai a kaisu su gaida kakanninsu da yanuwa direba ya dawo dasu. A gaskiya problems din da yake fuskanta da ita sunyi sauki sosai thanks to beloved Rahima, matsalar data rage yanzun shine yadda Zuwaira ta shafawa idonta toka taki amincewa zuciyarta matsayin Rahima na da can da wanda Allah ya kawota a yanzun, sai dai inda yake jin sanyi Rahima ta daure kowanne cin Kashi da Zuwaira ke mata, inda take Burgesa ma duk iya masifar Uwargidanta ba dai kaji bakinta ba, sai dai na Zuwaira wace takan Kara masa gishiri tace anyi alhalin ba ayin ba.
Ta dan bugi hannun kujerar da yake Kai tace “Lafiya kayi shiru haka cikin zurfin tunani?”
Ya juyo ya dau glass dinsa ya manna a fuskarsa ya sakar mata lallsusar murmushinsa yace “Just thinking of how lucky iam to have you in my life.”
Tayi dariyarta mai fitar da kyawawan jerin hakoran ta cikin shagwaba ta “Ya Haseeb kenan, godiya nike sosai.”
A can cikin dakinta Zuwairan Dakta ta zauna tana cizon yatsarta cikin damuwa domin kissar data shiryawa Rahima kamar kullum bai yi wani tasiri ba. Gaskiya yarinyar akwai dan Karen wayo, duk wani plan data shirya don taga downfall dinta sai dai ya wargaje ko ta wargajesa cikin ruwan sanyi. Gaskiya da sake lale, ba zata zauna ace Rahima ta kwace mata miji ba. To me rage, me yai saura? Matar da babu irin kissa da kisisinar da bata kware a Kai ba, matar data iya hilace miji ta hanyoyi daban-daban?
Sai dai ita kanta ta amince Rahima mace ce Mai matukar ladabi da biyayya halayen da kowanne namiji ke so wurin matarsa, to ko wadannan halaye basu isa su mallaka mata mijinta ba? Ga yadda taji labarinta tun aurenta na farko Rahima bata yiwa mijinta musu, duk abinda yace fari ne zata tas kuwa koda kuwa baki ne za tace yafi nono fari. Bayan haka ko taso ko taki Rahima macece mai hakuri mai son zaman lafiya da kowa bata son tashin hankali sam amma bata daukar raini, to ita yanzun ya zata yi? Tas ta gama amfani da magunguna da Husaina ta kawo mata bata ga wani canji ba, Husaina bata da mutunci ga wata gurguwar shawara da take bata wai ta rabu da Haseeb, hhmmm da ne zuciyarta ta rinka gigin yayo mata wannan mummunar tunanin, but ta rabu dashi ta auri wa? Ina zata sami kamarsa? Ita kuma don sakarci ta rinka daukar shawara…
Zuwaira ta muskuta a gado taci gaba da tunani, to yanzun data gane kuskuren biyewa Husaina wane mataki ya dace ta dauka don mallake zuciyar mijinta irin Rahimar?
Gidan malamai? Ta girgiza kai, no ba ya cikin dabi’a ko tsarinta, tayi saurin kawar da wannan, bata yarda da yawon gidajen bokaye Rahima ta shigewa Haseeb zuciya tayi daram ba, to meye sirrin? Inganta tsabtar jiki da tufafi da muhalli ko kuwa iya sarrafa dadad’an nau’ikan abinci? Kai ah ah wadannan kadai basu isa su mallaka mata zuciyar gwarzon namiji irin mijinta ba. To ko kuwa kamun kai da rike mutuncinta ne silar suka zama silar zama ‘yar gaban goshin sa?
Shin Ina zata gano sirrin don itama ta kwatanta taga ko zata ci riba tayi nasara mijinta ya rinka kaffa-kaffa da rawar jiki da matar da a da yake nuna ita din dole ce tasa ya aureta?