
Kafin ta samo amsarta ya dace tasan ita macece , tasan martaba, kima da darajar da Allah yai Mata, to idan ta zubar da mutuncin nata tuntuni fa, yanzun ne take son tattaroshi ta kwaso ta zama equal da Rahima fa duk da hausawa sunce mutunci madsra ba a barinsa a kwashe duka?
Nan take hawayen nadama suka fara gangaro mata, tabbas mijinta yai hakurin zama da ita, da wani ne da tuni ya koreta amma ya daure ya riketa duk da yasan illolin dake tattare da masu irin halinta, oh ni Zuwaira Allah ka shiryar dani hanya madaidaiciya ka hana min ci gaba da aikata sabonka,ka yafe min dimbin zunuban dana jibgawa kaina.
Babu wani abinyi yi a gareta illa ta roki mijinta gafara kana taci gaba da istigfari, tsayuwar dare da azumin nafila ko Ubangiji zai ji kanta ya yaye mata matsolinta, ciki harda rokon Allah ya mallaka mata zuciyar mijinta, to bangaren Rahima fa? Ya zan dole ta ajiye duk wani kishi da kyashi da hassadarta su zauna lafiya ko ta Kara samun haske daga gareta wadanda zasu gyara mata al’amurranta.
An dade da fara Kiran sallar magrib kafin ta dawo hayyacinta tayi hanzarin dauro alwala ta gabatar da sallar kana taci gaba da istigfari har aka Kira isha’i, ta mike ta gabatar ta sallame ta yi adduoinnta ta shafa.
Kafin maigidan ya dawo daga masallaci ta shiga wanka ta fito ta canza ado ta fito da kayan abinci, tana harhadawa ya shigo falon tareda su Khalifa harda Abdul, suka zauna suka ci abinci suka kare, bayan sun wanke baki da hannu ta kallesu tace “Kun ga ku tafi sashen Aunty Rahima ku ce Ina gaisheta “
Yara suka dubeta galala Kuma basu tashi ba to basu taba ji tace hakan ba,Saida ta maimaita suka mike cikin farin ciki, Khalifa ya kama hannun Abdul yace “Mama mu kwana a can?”
Ta gyada Kai”Manufata kenan, oya, ku wuce ku bamu wuri “
A guje suka fita sunata murna, shi kuwa yana zaune tamkar baiji diramar da suke yi ba duk da kasancewar yaji dadin furucinta ba zai nuna ba domin gudun ko halin neman maganar ce nata ya taso ko da wata manufar ta aikata hakan.
Ta bude baki zata yi masa magana kenan sallamar Husaina y katseta, kafin ayi mata iznin shiga ta shige, masifar kamshin turarenta mai shegen hawa kai ya da doki hancin Daktan, yai saurin mikewa, ita Kuma ta rusuna cike da ladabi na kissa ta gaishe tana wani kashe murya sai kace karuwa, ya amsa a dakale ya nufi sashen sa.
20/09/2020, 12:08 – Anty saliha: …ˆRAHIMA…doc by jami
49
Husaina ta kalli tace “Ni dai da sa’a nike, duk lokacin dana taho sai in tadda Oga na gida.”
Takaicin furucinta yasa Zuwaira shan mur, a zahiri kuma ta gaji da irin dirar mikiyar da aminiyar nata ke mata, bata taba zuwa gidanta sai ranar girkinta ta kuma tabbatar da zata sami Daktan a gida me take nufi? Kalli irin shigar data yi ma, har tana wani rausaya murya kasa -kasa don zata gaisheshi….
Husaina ta mike kafafunta ta kalli ‘yantsun hannunta da faruttan da suka ci adon jan farce ta yaba da kanta tukunna sannan ta tabo Zuwaira “Meye matsalar naga kinyi shiru fuska a daure”
Zuwaira ta kalleta a shagube “Wace irin matsala bayan kin shigo kin ganni muna zaune lakadan muna hira da mijina!
Ta kura mata ido na dakika guda “Zuwaira kenan ni banga hakan ba yanayin murtuke fuskar da yayi, da kyar fa ya amsa gaisuwata, shine kike ban mamakin rabuwa dashi ki huta tunda ba kanin tsohonki ba ne.”
Kalamanta sun yiwa Zuwaira daci amma ta daure tace “Ba zan rabu da mijina ba Husaina tunda Ina son abina.”
Tayi wata 'yar shewa irin tasu ta 'yan duniya tace "Aiki ya ci sai ki kawo kudin biyan Malam."
Zuwaira ta tabe baki “Ina ce sai an ga fa’idar abu ake biya?”
“To a cewarki komi normal sai ki biyani.”
Zuwaira ta gyara zama ta kalleta daidai ta mika hannu ta dauki cup din da Daktan yasha lemo bai shanye ba shigowarta yasa ya aje cup din ya fita, ta Kai bakinta kenan Zuwaira ta kabe cup ya fadi ya fashe.
A fusace ta zabura “Kan uba! Wane irin iskancine kike ji ne yau?”
Zuwaira ma ta zaburo ta mike a fusace “Ha ki nan babbar ‘yar iska da kike neman raina min hankali, ki rasa cup din da zaki sha lemo sai wanda mijina yasha a ciki?”
“Ke din ce babbar ‘yar iska har yaushe kika san darajar mijin da kike kuri dashi, yanzun me Kika san mutuncinsa?”
Maimakon amsa mari Zuwaira ta shararawa Husaina..tace ki sake kirana ‘yar iska kika yadda zanyi dake…
Husaina ta rike kuncinta ta saki ta dunkula hannu ta sakarwa Zuwaira a ciki, ba sai dambe ya kacame ba, nan Mai aikinta ta saka ihu ta ruga sashen Rahima ta fado mata tana kuka.
Rahima da Uwale suka rugo a guje, inda ta shiga tsakiyar aminan sa idanunsu ya rufe saboda masifa ba su ga zuwanta ba, wani cup din Husaina ta raruma ta wurgi Zuwaira dashi ta kauce bai sameta ba sai Rahima ya yanketa daidai saman girar ta.
Jinin da suka ga yana zuba yasa suka daina masifar, Husaina ta suri Jakarta ta barta gidan a guje, Zuwaira da Uwale suka yo Kan Rahima suna mata sannu, nan take dai aka dauko first Aid kit aka wanke ciwon aka tsaida jinin kana aka rufe da plaster.
Jikin Zuwaira yai sanyi sosai ta shiga cikin damuwar abinda zai faru da zaran maigidan ya dawo.
Rahima ta lura tace “Don Allah ki kwantar da hankalinki tsautsayi ne Wanda ba a sa masa rana.”
Ta kalleta cikin jin nauyi sabida irin surutan da Husaina ta rinka barbadawa da gayya kuma tasan Rahimar da yaran gidan ma sunji (masu musu aiki) tace “Don Allah Rahima kiyi hakuri ki yafe min.”
Rahima ta kalleta cike da tausayi “Wallahi ban rikeki da komi ba Aunty Allah ya yafe Mana m baki daya ya tsare gaba.”
Suka dan zauna na ‘yan mintoci kafin ta mike tace “Zamu koma can sabida ba kowa sai yara, mu kwana lafiya.”
Zuwaira ta amsa “Nagode a sanyaye.”
Ya dawo rai a bace dalilin yaje gidan Hajiyarsa ya shaida mata lalle zai rabu da Zuwaira muddin ba zata daina hulda da kawaye irinsu Husaina ba, ya taraa Hajiyar bata jin dadi dole ya kyale duk bai ce komi ba but yai deciding washegari zai kaita asibiti don ta samu proper care, ya dawo gida a fusace.
Ya shige bedroom dinsa bai ga Zuwairan ba, ya gyada kai ai yasan ba zata dumfareshi ba yanzun tunda bata da gaskiya.
Zuciyarsa ta rinka kuna, ya shiga yai wanka ya fito abin na cinsa a rai kiranta yayi ta waya.
Kafin ta iso ya Kai ya komo cikin bedroom dinsa ita kuma tana can cikin fargabar masifar da zai mata, ashe Zuwaira ana tsoron manya, ko can wargi wuri yassamu.
Ta sallama ta shiga tayi kamar ba zata zauna ba ta canza shawara ta dofane a gefen bedroom chair, yai kai ya dawo yai mata tsaye a gaba ba tareda yace uffan ba, ta rinka satar kallonsa da wutsiyar idon. …
Haseeb ya dan baya ya juya mata baya ya tambayeta “Zuwaira Ina son baki zabi wanda in kin riga kinyi an yi an gama, ba yi hakuri balle na tuba. Shin kina son zama dani ko ah ah??
Cikinta ya bada kulululu kamar mai jin zawo, cikin makyarkyatar murya tace “Me ya kawo wannan maganar Dakta?”
Cikin muryar data tsani yai mata magana yace “Amsa zaki bani ko nima tambayata kike?
Ta Kara kidimewa “Ah ah wace ni, yi hakuri, wallahi Ina sonka Dakta, ban taba son kowa ba sai ke, ka yafe min. ..
Ba wannan amsar nake son ji ba.”
Ta gyara zama “Ina son zama da Kai har muddin rayuwa.”
Ya numfasa ya zauna yace “Ba na jin zaki sami wannan daman ta bangarena as long as za kici gaba da mu’amala da kawayen banza to zan sauwake miki aur…..
Bata bari ya karisa ba ta mike zumbur tasa hannu ta rufe bakinsa tana kuka “Don darajar iyayenka karka furta, don kaunarka da Annabin rahama ka yafe min… Ta durkushe a gabansa ta dafa gwiwoyinsa tana rasgar kuka tana masa bayanin yadda suka yi da Husaina bayan fitarsa ..
Jin an ambaci Rahima ya mike da sauri “What! Iskancin naku ya wuce kuyi a waje har cikin gidana har ku nemi kassara min mata ta?”