
“Ka saurareni don Allah laifine na riga na aikata, nayi kuskure but nayi nadamar dukkan abubuwan da na aikata tuni, inata istigfari dare da Rana, na gane illar kawancena da su Husaina na kuma janye daga gareta data lura ne ta kara shige min amma wallahi bada yawuna tazo gidana ba.”
Ya numfasa “Ba dole tazo gidanki ba tunda tanada manufarta Wanda a da banyi niyyar fada miki ba sai kin gane da kanki but tunda ta fiki wayau da iya siyasa ko in ce duniyan cin zauna Ina zuwa.”
Ta koma gefen gado ta zauna tana sharar hawaye, ya wuce Kai tsaye ya bude wardrobe dinsa ya bude wani safe da key ya ciro wata katuwar envelop ya mika mata yace “Duba contents din nan kafin inje in dubo Rahima in dawo.
Ta karba gabanta na faduwa, ta rinka zaro pictures dinsu ne da Husaina wasu da abokan huldar kasuwancin nasu tana jinjina Kai, don ita ta manta ma anyi wadannan hotunan don bata basu mahimmanci ba.
Da alamun kowa yai barci a sashen Rahima sai ita kadai dake zaune a falonta rike da dan karamin littafin adduar Nan Al-Ma’asurat tana karantawa.
Ya isa gareta bayan ta amsa sallamarsa, cikin kyakkyawar kulawa yace “My dear Iam so sorry.”
Ta sakar masa murmushi Mai kwantar da hankali “Haba karka damu isn’t all that serious.”
Hannunsa yasa ya taba jikinta, wuya da goshinta, ya rike tsintsiyar hannunta ya duba pulse, saida ya tabbatar temperature da vital sign normal ya saki ajiyar zuciya yace ” Kiyi hakuri su Zuwaira sun saka ki cikin shiriritar su.”
Tace “Dakta duk misulmin kwarai yasan kaddarori da jarabawar rayuwa, fatan mu Allah yasa mu ci jarabawar.”
Yace “All the same sai na sa an daure wannan matar.”
Ta bude baki ta sauka kasa gwiwa biyu tace”Haba Dakta kana son ayita zuzuta zancen kenan, don Allah ka bar magnar a rabu da ita kawai in don ni”
Yasa hannayensa ya dagota “Kin san ba laifinta gareni kenan ba?”
“Kamar Yaya?”
“Could you believe matar nan messages ta rinka turo min harda letters wai don Allah in aureta?”
Rahima ta zaro ido “What? Kiji min maras mutunci taci amanar Aunty Zuwaira take nufi?”
Ya gyada Kai “Why not tunda ita Auntyn taki bata san ciwon kanta ba?”
Ta jinjina “Taf mutum sai Allah, Allah ya tsaremu da sharrin mugun mutum.”
“Ameen ya Azeez, gobe in Sha Allah zan Kai Hajiya asibiti mu dan binciketa tana bukatar kulawa ta musamman.”.
Tace “Yakamata gaskiya, Allsh ya bata lafiya yasa ba wani serious problem bane.”
Ya mike kana yace “Insha Allah ba matsala.”
Yai mata sallama ya koma wajen Zuwaira ikon Allah.
21/09/2020, 15:53 – Anty saliha: ….RAHIMA…doc by jami
50
Zuwaira ta zauna turus tana karanta takardun da wai wace ta dauka da suna aminiyar ta aikowa mijinta, ta girgiza kai cikin dimuwar ganin irin kalaman soyayya da bata zaton Husaina zata iya bayyanawa wani ba balle mijinta.
Hhmmmm abin tambaya ma a nan tun yaushe Husaina ta fara karakainan turowa mijinta sakonni, tabbas wannan dalilin na daya daga cikin reasons din Haseeb na dagewa cewan ta rabu da Husaina, ita kuma saunar bata gane komi ba sai kara cusa kanta take gareta tana badadi da sirrin mijinta a duniya.
Yanzun ta fara regrtting watsi da nasihohin da mijinta da iyayenta ke mata tana watsu dasu.
Kaicona ni Zuwaira! Ga batun da Iyayenta keyi nan cewan idan basu isa su fada mata taji ba duniya zata yi mata hankali cikin ruwan sanyi gashi ta gani.
Oh oh ya Haseeb yaji da ya fara ganin sakon wannan maras mutuncin? Hmmmm ita tasan halin mijinta ko a mafarki ba zai ji sha’awar Husaina ba, rikon addininsa da kamallarsa zasu sa Allah ya tsare fadawa sharrinta don idan ance ta kai sunansa gidan malamanta ba zata musa ba, za tayi abinda yafi hakan shu’umar banza.
To ni Zuwaira mene na gani laifin Husaina, ai sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga.
Me na rasa?
Duk da Ubangiji yai mini muwafaqa ya azurtani da samun nagartaccen miji maimakon in gode masa ta hanyar karfafa imanina da tsarkakke zuciyata, bin dokokin Ubangina da sauke hakkokin mijina, faranta ran iyayena da kokarin zama uwa ta gari ga ‘ya’yana sai nayi kunnun uwar shegu na fandare na butulcewa Mahaliccina baiwar da yai min..
Ta matso wasu zafafan hawaye yayinda take tambayar kanta shin na ma sauke hakkin iyayen nawa ma kuwa bayan su din sun sauke dukkan hakkokina gwargwado? Mahaifina yai min zabin uwa ta gari, da aka haifeni ya rada min suna Kan tsarin islama, ya kokarin ganin mun samu ilmin addini dana zamani daidai yadda zasu taimaka mana gyara zamantakewar mu na duniya da gyara lahirarmu, iyayena sun bani ingantacciyar tarbiyya kana su kayi min zabin miji nagari dana isa aure to amma ni wane sakamako na basu a rayuwata ta duniya?
Shin nayi kokarin sauke hakkinsu mai girma a kaina kuwa, bayan ance Annabin Rahama ya la’anci duk Wanda ya wulakanta iyayensa, an horemu da yi musu d’a a, mu yiwa Manzon Tsira, mu kyautata musu domin wajibi ne a garemu matukar basu kauce hanyar islama ba, hatta da magana ance Kar muyi musu kalamai masu muni, sabida girman iyaye a garemu ne har aka wajabta girmama ‘yanuwa da abokanansu ko kawaye kamar yadda zamu girmama su iyayen namu.
Ni Zuwaira ‘na shiga uku’ sunan wani littafi na ‘Gidan iko’ . Duk inda aka tabo ni inada rauni da nakasu. Can tunaninta ya koma kan abokiyar zamanta Rahima da taki amincewa da kaddarar take wulakanta ta a idon kowa alhalin ba laifinta bane ko Haseeb bai aureta zai auri wace duk Allah ya rubuto masa.
Ya jima a tsaye yana kallonta tana share hawayen da suka gaza tsayawa, tausayinta ya kamashi, ya isa inda take ya rungumota yana fadin “Ya isa haka nan Zuwaira komi ya wuce tunda kin gane kuskurenki.
Ta kallesa cike da damuwa “Anya Ubangiji zai yafe min laifukana kuwa?”
Ya rufe bakinta “Kasancewarsa gafurun rahimeen, Yana amsar tubarmu ko da zunubanmu sun Kai girman Uhud ne, hakika Unangijinmu mai afwa ne, yana kankare mana dukkan zunubanmu idan mun gane munyi, munyi nadama mun rokesa gafara da niyyar ba zamu sake komawa ga daukan zunubin ba. Ba shakka ya soki da rahama tunda yai gaggawar fahimtar dake har kika kaskantar da Kai Kika nemi ya yafe miki.”
Daman ba wai Dr Haseeb bai kaunar Uwargidansa Zuwaira bane, halinta ne ya tsana yake kyama Kuma, da Allah ya nufe ta da shiriya alhamdulillah ya rungumi abarsa.
Yau kwanan Hjy Katume uku a Haseeb Medical Centre, a dalilin rashin lafiyar data taso mata mai suna *NEURASTHENIA* Wanda idan cutar ta kama kwakwalwar mutum zai rinka jinsa ko yaushe bai da isassar lafiya, kasala da rashin kuzari su addabesa, ba wata cuta ce mai tsananun gaske ba, nan da nan likitocin kwakwalwa ke ganota suka taimaka da magunguna da bada shawarar samun isashshen hutu ga maras lafiyar don shawo kan cutar.
Tunda ya gano cutar dake damun Hajiyarsa kenan ta matsa ya daukota da kansa ya kawota asibitin gashi har jikinta yayi kyau ta samu sauki sosai, likitoci da sauran ma’aikatan asibitin sai ina ka saka ake da ita, kulawa ta musamman ake bata, to wani ma yai rawa ballantana dan makadi? Mahaifiyar Chief Medical Director ce fa da kanta.
Tunda aka kawota Rahima ce ke zaman jinya tunda ba tada diya mace, da kyar dai Hajiyar ta amince da dawainiyar ganin alamun ‘yar gidan nata na dauke da juna biyu.
Kwananta na hudu kenan yau ta Kara samun sauki Amma likitan yaki sallamarta yadda ta bukata don haka Uwargida Zuwaira ma ta taho tace Lalle ita zata amshi Rahima wajen jinyar domin ta huta, jinya fa ba karamin al’amarine ba, so da yawa Mai jinyar maras lafiya kanyi ciwo na musamman saboda yanayin kulawar ko zirga-zirga da sauransu. Rahima ta dage ita zata karike don ladan take kwadayi.
Suna cikin gardama sai ga Hayatu da nashi ayarin sun shigo cikin dakin da Hajiyar take, wurin ya kacame… Sai ga Ya Haseeb ya danno kai, wuri yai tsit, fuska a murtuke ya kalli Hayatu “Daman kana cikinsu kana kallonsu suka dami mutane da hayaniya?”
Hayatu yai turus yace “Sarkin yawa fa ya fi sarkin karfi Ya Haseeb, duba ganni ka gani mata hudu ni kadai?”
Yayi murmushi “To lauya, hayaniyar me ake?”