
Zuwaira tace “Wai nace Rahima ta koma gida haka nan ta huta ni zanci gaba da zama taki, ita Kuma Haulatu tace itama zaman za tayi.”
Ya kalli Mahaifiyarsu cikin kauna yace “Me kika ce?”
Tasha mur ta mayar “Me zance kuwa, in da ka barni cikin dakina ai da kowa ya huta, yanzun sai kasan nayi “
Ya sake yin murmushi yace “Shikenan na yarda da shawarar Zuwaira, kowa ta koma gida a barta ra zauna shikenan ko?”
Duk suka yi tsit har Rahiman kuwa da yai tunanin ta furta wani abu bata kala ba, to wa ya isa ya daga hukuncin da babban Yaya ya zartas?”
21/09/2020, 22:59 – Anty saliha: …ˆRAHIMA..doc by jami
51
Da kansa ya dauki Rahima suka koma gida, ta cewa Uwale bata jin cin komi a daren don haka suka yi sallama ta wuce dakinta, ta tube ta shiga wanka inda ta dade cikin ruwan dumi tana shakar lemon scent na bath salt data zuba, ta rufe idanunta tana hamma....
Haseeb ya gama nasa wankan ya kimtso ya shigo domin mika godiyar dawainiyar da take da mahaifiyarsa, ya zauna shiru bata fito daga toilet ba, ya dauki wayarsa ya scrolling ma’idanar wakewaken da yai saving, ya danna daya daga cikin wakar da yake so mai taken What have I to do to make you love me,what have I to do to make it right? Wace mawaka da suka lakabawa kansu suna Blue suka raira. Ya gyara kwanciyarsa ya l lumshe idanu yana tuhumar me yasa idan yana sauraren wakar nan ya kanji tamkar domin shi da Rahima aka rerata?
Me yasa zuciyarsa taki amincewa da Rahima na so da kaunarsa yadda take ikrari,baya son yana doubting but Rahimar ce wani lokaci sai ya kasa gane kanta, sai ta saki jiki Sai Kuma ta janye sai ya rinka bi yana rarrashi, ko kuwa har yanzun bai fahimci ita din mai murdadden hali bane kamar sa? Ta kanyi taka tsan-tsan da gujewa duk abinda tasan zai jefata a damuwa.
Ya sake duban agogo, ta dade fiye da kima cikin bathroom… Ya kasa daurewa ya mike yai knocking daya biyu har uku shiru ba amsa, habawa a gigice ya bude kofar ya afka cikin toilet din a tsorace…
Ya saki kyakkyawar ajiyar zuciya yayinda ya ganta zaune cikin bathtub tana barci. Ya matsa ya zauna bakin bath din tare da saka hannunsa cikin ruwan wankan da har ya fara hucewa, don kar ya firgitata ya matsa daf da kunninta ya rinka Kiran “My dear….a hankali.
Kamar a mafarki ta farka ta jita tsundum cikin ruwa, ta girgiza kai tana kokarin gano halinda take ciki Ya mika mata dauke da towel ta amsa ta mike tsaye ta daura yasa hannu ya daukota cak bai direta ba sai kan gado, sanyi ya fara kadata ta shiga rawar dari, yai saurin dauko riga mai kauri ya saka mata kana ya lullubeta da lallausar blanket ya koma ya zauna yana kallonta cikin takaici, sun jima ba wanda yai magana har saida ta ji ta daina jin sanyin, dumi ya ratsata ko’ina ta yaye blanket tayi mika ta dago ta kallesa tace “Thanks for rescueing me ban san lokacin da barci ya daukeni ba.”
“Na fahimta.” Ya mayar mata a takaice.
Jin irin amsarsa yasa ta yunkura ta zauna tace “Me ke faruwa naga you’re worried?”
Yace “Ke ya dace a yiwa wannan tambayar Ina bukatar sanin meke faruwa?”.
Ta amsa “Kamar me?”
“Ina son sanin dalilin da yasa kike yawan barci yanzun duk inda kika zauna al’amarin ya kai Kuma har a bathtub, why?”
Tace “Nima haka na tsinci kaina ciki.”
Ya dago cikin mamaki “Kina nufin rashin lafiyace ta sameki ban da labari?”
“Kalau Nike, may be dai yawan tashin da nike cikin dare bana samun isashshen barci ne.”
Yace “Uhhmmm, do me a favor, Miko min hannunki.”
Tayi nawar mika masa don tasan da abinda yake son ganowa ya tabbatar…
Ya riko hannun da kansa ya juya tafin hannunta ya kura ido ya tsaya shiru kamar mai nazari.. zuwa can ya saki ya saki ajiyar zuciya kana cikin muryar da bai taba amfani da ita wajen magana da ita ba yace “Yaushe Kika shirya fada min kina dauke da cikina Rahima?”
Da ace ba kusa da ita yake ba da wuya taji abinda ya Fadi, da tajin Kuma yanayin muryar tasa duk ilahirin gashin jikinta mikewa saboda taushinta, ta kasa bashi amsa saboda kalamansa sun ratsata sosai, ua akayi ya gane tana dauke da juna biyu? Kaji wani wauta, to idan
shirmenta rashin laulayi da dafewar cikinta zai hana kowa ya fahimci halinda take ciki shi ba likita bane zai iya ganewa cikin kowanne yanayi?
Wace amsa zata bashi yanzun? Bata da wani kwakkwaran dalilin rashin sanar dashi illa jin nauyin a ce wai ita ke dauke da cikin Ya Haseeb, kunji wata sabuwa! Meye na jin kunya tunda an riga an zama daya anyi auren nan me ya rage illa fatar samun zuriyya dayyiba?”
Shirunta ya kara tunzura shi ya mike zai bar dakin ga tunaninsa zargin da yake yi ne ya tabbata tabbas bata damu dashi ba, Rahima bata wani sn shi, because idan ba hakan ba ne why zata samu ciki almost 3months taki fada masa me take nufi?
Ta lura da niyyarsa tayi saurin durowa daga gado ya juyo a fusace, nan da nan ta durkusa a gabansa “Nasan nayi laifi kayi min afwaa kayi hakuri.
Ya nisa “Hhhhh inda take kamashi kenan, da zaran tayi ba daidai ransa ya baci zata gaggauta bashi hakuri sai dai wannan karon yayi fushi sosai ya kalleta rai bace “Da hakurin ta mutu nawa kika bayar? Ki zauna kiyi tunanin abinda kika yi min dinnan ya dace, idan ban San halinda kike ciki ba wa ya kamata ya sani? But tunda kina ganin hakan ne alkhairi a gareki is okay ki neme ni lokacin da kika shirya.”
Yana gama magana ya fice abinsa ya barta a durkushe. Ita kanta tasan ta tsokano zuciyar maza ba fus kenan.
Tun daga ranar bai sake waiwayarta da batun na ita Kuma ta rasa yadda zata bullo masa, rayuwar tasu ta canza salo suka koma kamar yanayin zamansu da farkon auren.
Satin Hjy Kaltume biyu cif a asibiti ta matsa ya sallameta, ya dauketa da kansa suka maishe ta gida shi da Zuwaira. Hajiyar sam bata San da wata matsala tsakanin Daktan da amaryarsa ba, babu ma wanda ya lura su kadai suke abinsu.
Yau Rahima ta tashi cikin matsanancin zazzabi hade da mura, Shafa’atu ta shigo gaisheta suna hira Zuwaira ta damu ta shiga Ina ka saka da kanwar nata don tunda suka shirya haka suke kaffa-kaffa da kulawa da juna musamman idan rashin lafiya ya shigo.
Kasancewar Rahimar ce da aiki Zuwaira ta shigo sashenta ta tambayeta abinda zata dafawa maigidan tunda ita tana kwance.
Tace Aunty akwai time table na nau'ikan abincin da muke dafawa kowacce rana Uwale ta nuna miki ko ki dafa duk abinda kika ga ya kamata, nagode."
Zuwaira tayi dariya “Godiya Kuma tsakaninmu kanwata, in dai lalura ce yau gareka ne gobe ga danuwanka balle ance ko baka iya alkhairi ba ka yiwa mai maka, ni so nawa kika shigo Kika taimaka mini? Fatanmu dai Allah yasa murar alkhairi ce.”
Sallamar su Maryam yasa Rahima ta dafe kai tace “Aunty ga ‘yan baka nan don Allah karki maimaita batun nan a gabanta.”
“Yaushe Kuma ai na riga naji, Hjy Zuwaira Allah ya amsa harda nan bangaren don naga sai wani sisi kike yara sun dade da zama samari.”
Zuwaira tayi dariya “Marhabin sannunku da zuwa, Aunty Maryam karki ga laifinmu a nan tuhumi Dakta, may be tsufa ne ta fara aikinta.”
Maryam da kawarta Ummul khair suka shiga ciki Zuwaira ta bisu aka gaisa kana tace “Komin tsufansa idan ba zaku tabuka ba sai mu sake darzo masa amarya.”.
Rahima tayi murmushi “Yo ta taho mana wa ke tsoronta?”
Ummulkhair tace “Ai tsoron ba naku bane nata ne don duk wace tace zata shigo cikinku gaskiya sunanta sorry.’
Maryam tace “Tabbas zamanku na burgeni, Allah ya Kara hada kanku.”
Zuwaira ta amsa “Ameen Bari in shiga kicin in dawo.”
Ummulkhair ta rike baki “Oh ina ma ace gidanmu ya dawo irin naku?
Rahima tace “Wai har yanzun babu canji a yanayin zamanku?”
Ta girgiza kai “Ai Rahima yanzun ne ma gidan ke Shirin zama sansanin fada sabida ga goron amaryarmu ta hudu na kawo muku.”
Rahima tace “Ikon Allah! Duk kwasar karar mahaukaciyar da akeyi a gidansa bai isa ba sai ya karo wata masifar?”
Shafa’atu tace “Namiji ne fa,? Ai sun fi son su tara ayita bala’i da masifa a kansu.”
Maryam ta gyada Kai “Wannan idan Allah bai sa kun fahimci rashin alfanun rashin zaman lafiyar ba kenan. Muddin kuka yi hakuri da juna sai ku sami salama da kwanciyar hankali.”.
Ummukhair ta gyara “Dace da irin wadannan kishiyoyin da zasu fahumci zaman lafiyar yafi zama Dan sarki, su fahimci arziki bai samuwa saida hakuri Abu ne mai wuyan gaske a zamanin nan da muke ciki. Idan ba a samu mai shurin shigowa ra fishsheki ta tsigeki cikin yaranki ba za a samu Mai cewa ki shigo din ki gane kurenki tunda kin auri mijinta, sai kace kowanne namiji an lika masa lambar zama da mace guda ne a goshinsa, ku dai kunyi dace da kishiyoyin.”