
Ya maidasu a aljihu yace “Ah ah Ina so Hajiya, Allah ya saka miki da aljanna madawamiyya.”
Ta amsa “Ameen Auta, hanzarta ka gani, sai ka dawo.”
Ya fito har zai hau babur dinsa sai shaawar takawa a kasa yazo masa, ya fasa ya bi titi yana takawa daidai, irin tafiyar yaro matashi Mai jini a jika.
A cikin gidansu Rahima tuni ta dade da kimtsawa tana jiran Rabiun, a yau shigar wando da riga suka yi ita da Maryam ‘yan Pakistan tsarabar Umrah ne da Baffansu ya kawo musu, duk kalarsu guda watau ruwan hoda da zanen kalar gwaiduwar kwai a jikinsa, banbancinsu kawai na Maryam yafi nata girma tunda ta fita girman jiki. Ita Rahima yarinyace gajera, baka mai dan jiki, ba kyakkyawa ba ce ba Kuma za a kirata mummuna ba, Maryam ta fita kyaun fuska nesa ba kusa ba, ita kuwa halittar jiki Ubangiji ya kyautatata mata. Tana da kyaun siga kwarai da gaske, kirar jikin matan Nan da ake Kira masu kirat kwalbar coca-cola. Duk da ita ba Mai kiba bace Allah yai mata halittar wasu guraye murde a wuyanta, layi-layi uku. So da dama akan kirata mai karuwar jiki kasancewar kowanne irin sutura ta saka su kanyi mata kyau suyi ras a jikinta tamkar dominta aka yi. Bayan wannan ba kowa ke yarda idan an fada masa shekarunta sun kai ashirin ba saboda jikin da fuskar basu nunawa.
Sanin yadda sutura ke amsar jikinta suna fito Mata da shape yasa babu yadda za ayi mutum ya ganta ba tare da after dress ba, ga addini ya ratsata sosai domin Alh. Mamman ba daga baya ba wajen kyautata tarbiyyatr yayansa. Alhamdulillah su Rahima sun gogu da addini sun san hanyayoyin tafiyar da harkokinsu ta yau da kullum musamman tsarin addinin islama, tsakar gidansu kadai mutum zai shiga yaga kalar tufafin da ta saka saboda tsananin bin dokar Ubangiji.
Cikin wannan shiga ta kamala ta fito ciiin natsuwa da kamun Kai ta tarbi maigida to be da harkarta yadda suka saba yiwa juna, suka gaisa a mutunce.
Rabi’u ya isar Mata da sakon Hjajiya. Rahima ta amsa da “Kasan kuwa da kace Hajiya na gaisheni wani irin dadi kan rufe ni, ni shar kenan don wannan alama ce ta dace da sarakuwar kwarai.”
Ya gyara hularsa cikon jin dadi “In don Hajiya Kar kiji komi, ta yaba dake fiye da zatona, ke ko matan Ya Hayatu da suke kullum cikin bala’i bata kyamace su ba, ba abinda ke tsakaninsu sai kyautatawa.”
Rahima tace “Ta hutawa zuciyarta da masifa, daman har addua nike Kar Allah ya hadani da muguwar sarakuwa mai sa ido da kasa kunni a harkar matan danta don in kaji labarin masifar wata tsohuwar sai auren ya fita ran mutum gaba daya.”
Yayi dariya “Banyi tsammanin Hajiya zata kula matar Ya Hasseb ba balle na Ya Hayatu koda ace gida daya suke zaunre balle Allah ya raba zaman, Ya Hasseb na Galadanci, Ya Hayatu na Gwammaja ita tana Yakasai, bata zuwa gidan kowannansu balle ta gano abinda zai tayar Mata da hankali, sune dai duk sati suke Kai matansu su gaisheta, mu kuwa saboda kaunar da take miki ne yasa tace da ita zamu zauna.”
Tace “Lalle Dan lelen Hajiya, wai Rabiu daman kana da sauran turaren nan ka daina fesawa na daina jin kamshinsa.”
Ya kyalkyace da daruys “Kinsan na gaya miki nima fa Ya Haseeb ya bani, da naga ya kusa karewa ne na boye, ban san kina son shi ba dana kawo miki tuni amma zan adana miki sauran in kinzo in baki.”
Tace iye dan gatan Ya… Haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyin Yayan Rabiun ta kasa fadin sunansa duk da bata taba ganinsa ba.
. Ya girgiza Kai “Ba zaki ma tabbatar da hakan ba Saida batun aurenmu ya taso, gaskiya Ya Haseeb ya cika danuwa kaunar zumunci da taimakon zumunta kamar yadda Allah yai mana horo muyi. Gaskiya kullum Ina jinjina masa, yana kaunata, yana ji dani matuka, nima bani da kamarsa Rahima.”
Ta nisa tace “To Allah ya barku tare Rabiu, Allah ya kaika matsayin da zaka kyautata masa kaima.’
Ya amsa “Ameen, insha Allahu zanyi struggling, bari harkar bukin nan ya kare mu gama karatunmu ki gani da taimakon Allah zamu ba marada kunya.”
Tace “Ko shakka babu sai mun ba mutane mamaki.”.
“Kar ma dai ace ‘Yan B.U.K da suke yada surutan banza, kinji maganganun da suke yi dana Kai musu IV, wasu har karyatawa suka yi.”
Taja tsaki “Kai kake kulasu, ai ni banda lokacinsu balle in saurari surutunsu.”.
Suna nan tsaye Umma da Maryam suka dawo unguwa, ya durkusa ya gaisheta ta wuce cikin gida, Maryam tana tsokanarsa “Ango kasha Mai, har an fara Shirin angoncine?”
Yai dariya “Ban sanki da haka ba Aunty Maryam, Ina kuka fito da dare Nan?”
Ta amsa “Gandun albasa, kasan can za a Kai amaryar taka rufi wajen Inna kanwar su Umma, Kuma don Allah ka daina kirana wata Aunty sai kaina ya rinka girma.”
Rahima tace “Girma ai ya hau kanki Auntyn Rabiu.”
Ta harareta “Kina korata ne kawai Kar in bata muku hira, Rabi’u Saida safe, ke Kuma zaki shigo ki sameni.”
Suka yi dariya suna kallon shigewarta gida.
Rabi’u ya kurawa Tahima ido tun tana kaucewa har ta gaji tace “Wai lafiya?”
Ya jingine da bango ya amsa “Kallon kyakkyawar fuskar amaryar Rabiu nike, wallahi Rahima tunda aka sa ranar aurenmu so da kaunarki dada tofo suke cikin zuciyata, so da yawa ina share awowi ina tunanin zamanmu a school, yanayin shakuwarmu da irin ji da juna da muke ashe soyayya ce ke shigarmu bamu fahimta ba. A kullum godewa Allah nike days kaddaro kasancewar hakan tsakaninmu, da Allah bai rubuto ke mata ta bace Rahima ya zanyi da Raina, Ina zan Kai wannan kololon son da ya cika min Zuciya har ya zamanto babu sauran ko masaka tsinke na kaunar wata, Rahima you’re my life, don Allah ki so ni yadda nike sonki.”.
Ta saki ajiyar zuciya kafin tace “Ina sonka Rabiu, kaunar da nike maka ne ta haifar da na amince ka zama abokin rayuwata.”.
“Na amince sosai Rahima nagode, bari in koma gida, ba sauran abinda kike bukata?”?. Ta kada Kai “Tsakaninmu ba wannan, lalurarka tawa ce kamar yadda tawa take taka, kasan nima ‘gata ce su Umma sunyi min komi, kasan sun so a hada bukin nan dana su Maryam amma Allah bai kaddara ba Abbas ya roki arzikin a bari sai ya dawo daga Dubai, sha’anin Dan kasuwa.”.
“Lalle naji, Allah yasa shine alkhairi mu dai Allah yasa ba za a daga namu ba.”
Tayi murmushi kawai ba tareda bashi amsa ba.
Ya fiddo kudin da Hjy ta bashi ya mika mata taki karba saida yace sakon Hjy ce ta tara jannu biyu domin karba, maimakon ya saka mata kawai sai taji caraf ya kama hannayen nata ya rike yana kallonta…
Tayi saurin kwacewa tana fadin “A’uzu bilahi minal shaidanin rajim, wa iyazu billah.”
Shima yai saurin juya baya Yana tasa adduar korar shaidan din, kana ya juyo a hankali yace “Rahima ki gafarceni, banyi da niyya ba wallahi.”
“Hhmmm Allah ya gafarta mana Rabiu nasan ba halinka bane, babu zargi tsakaninmu.”
Yace “Nagode, gashi. A wannan karon hijabinta ta santa ta rufe tafukan hannunta shi Kuma ya saka Mata, suka yi sallama ya tafi cikin damuwa.
Shaidan mugune, la’ananne, masheranci, Allah ka Kara yi Mana katangar karfe da dashi. Adduar da Rahima keyi kenan har ta shiga gida ta iske Umma da 2000 din da ya bata.
Nan take ta fara fada “Anya Rahima ba nace karki sake karban ko sisi daga hannun yaron nan ba, yaro dan makaranta da wane hidimar zaiji taki ko nasa?”
Ta durkusa “Umma naki karba ya tilastani Wai Hajiyarsa ce tace ya kawo min.”
Umma ta kyalkyace da dariya “Hjy Kaltume kenan, aikinta yafi da haka, wallahi kasancewar danta ne zaki aura yasa nike farin ciki, domin duk unguwar nan kowa yasan macece mai matukar sanin yakamata, ba a taba jin kanta da surukanta ba balle na tsakaninta da ‘ya’yanta. Gashi Allah yasa babban danta ya saya mata wannan babban gidan take zaune da kowa lami lafiya, keni yadda labari yazo min ance ba irin wahalar da bata sha ba da mijinta na fari daga ita har danta, ance yai masa kaskanci kamar bashi ya kawosa duniya ba to ga sakamakon Allah nan tana gani, shi yaron ya zama kwararren likitan kwakwalwa ba unda sunansa bai Kai bba daga Nigeria har kasashen waje, ke naji ance ma har turawa hayarsa suke yaje can yai musu aiki su biyasa..”