NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

Daidai Zuwaira ta leko tace ” Hmmmm all the credit goes to Rahima, tambayeta ta baki sirrin.”
Tana juyawa Ummul khair ta kalleta “Da gaske?”

Rahima ta danyi murmushi “Fada kawai take yi, yes ba shakka mun dan fuskanci problem tsakaninmu amma hakuri, kau da Kai, dogaro da kai wajen samun sana’ar da zata hana maka bata lokacinka kan al’amurran kishi, kyautatawa juna, girmama juna, tarbiyyar yaranmu tafarkin gaskiya, sanin hakkokin junanmu da yadda zamu sauke hakkin, danne zuciya daga saurin fushi, toshe kunnuwanmu daga kunji-kunji, rashin ganin kyashi da hassadar junanmu, tsayawa a matsayin da Allah ya ajemu, kyautata ibadarmu wajen bautar Ubangijinmu da mika dukkan al’amurranmu garesa suka shafe komi, suka kawar mana da dukkan fitunu dake tasowa ya mamaye cikin gida, sai kyautatawa shi kansa uban tafiyar Wanda sirri ne don kowacce da nata salon.”

Ummulkhair ta jinjina tace “A gaisheku da kokari, ko a nan kinga hannu guda ba zai dauki daki ba, Ni kadai ba zan ita gyaran al’amurran gidanmu muddin ba mataimaki.”
Rahima tace “Wajibi wata ciki tafi hakurin da kau da Kai saboda Allah bai halicci zuciyarmu iri daya ba, haka zurfin tunani da hangen nesa ba zai zo daya ba, abunda wata zata dauka a shekara wata ko na minti gudan ba zata iya dauka ba, to ana son idan an hadaku ita mai zafi ce ke sai ki yayyafawa kanki ruwan sanyi, tayi masifarta ta gaji baki tanka ba balle ku zama daya, ba Kuma za kiyi shirun don tsoro bane, no zaki nuna mata ke tarbiyyarki ta daban ce, sai ta gaji ta bari yau da gobe don kinsan akwai ciwo mutum ya takaleka baka kulashi ba.”

Ta gyara zama "Kin dai San mu uku ne, Ni ce karama, dukkanmu muna da Yara, na Uwargida sune mata manya sun girma sun isa aure, amma saboda mugun tarbiyyar da uwarsu tayi musu gaisuwa ta fatar baki bai hadani dasu dai dai kuji suna wake-wake da habaici har da zage-zage wata ran wai dani suke, in hanya ta hadamu su nemi bangajeni suce idan na isa in taka su karya banza..

“Tafdijan! Inji Shafa’atu me ya hana ki lallasata ki barta kwance ba kiga wa ya tsaya musu?”

“Uwarsu mana tunda ita ke turosu suyi rashin mutunci, ai na taba daukar mataki na dake su da suka kaini makura sai uwarsu tazo taci dammara tace da ita zanyi itace kishiyata ba su ba, suka taso za suyi min taron dangi suka ga ba zasu ci riba ba don ba zan dau rainin da rashin kunyar da suke yiwa ta biyun mu ba sai suka canza salon rashin mutunci,idan nayi abinci babu mai ci, yarana cikin duka da kyara kullum, babu mai daukar musu, ko ciwo suke yi babu mai lekowa yace musu sannu daga su har uwar, ita wancan ce da suke yiwa cin Kashi ta kan Dan leko.

Ga sata ga keta, komi na ajiye a sace, su bata na batawa su zubar da wasu, kullum Ni kenan boyon tarkace, ko wanke tufafina dana Yara nayi wajibi gareni in girke kujera in zauna jiran su bushe in kwashe karsu sa reza su kekketa min.

Da suka ga ban nuna damuwa ba sai suka zuba min gishiri ko suka zunduma min ruwa yafi karfin sanwata,,sai su aza tukunya su dora wani su ci su koshi, ko su fita su sayo wani suci su koshi.”

Maryam tace “,To shi maigidan yana Ina ake badakala haka cikin gidansa?.

Rahima tace ga abin damuwa nan gurbata tarbiyyar diya mata, ita wace irin uwace da zata saka ‘ya’yanta mata a harkar kishi? Me take koyar dasu kenan, Shi Kuma uban ya Kyaleta tana la’anta tarbiyyar yaransa?”

Tace “Ya Zama mijin tace ai. Ba ya iya kwabon yayansa Sam, nida nike kokarin kwabawa sunce na cika tsanani ne, nace a tafi haka.

Kwanaki yaran nan suka shirya makurcin da Saida ya sakeni, ban San hawa da sauka ya shigo Yanata masifar wai na hana yayanshi abinci Wai bai auro matar da zata hanasu abinci ba, don ma na samu suna cin girkin nawa da ban iya ba? Har da cewa zai ita rabuwa da kowacce mace kan yayansa.
Ban San dalilin masifarsa ba, ashe Wai sunce masa bana dafa u
Isashshen abinci ranar girkina alhalin bai mana iyaka da store ba.Ba bincike ya shiga tsiya, Ni kuma zuciya ta kawo min wuya ba bata lokaci na fara hada komatsaina nace na gaji gidan zan bari. Wai sai ita da yaran suka yo tsinke suka yi min tsaye a kofar daki suka ci gaba da rashin mutuncinsu wai ai daman sun gargadeni in bisu a sannu ko su shirya min tuggun da zan bar gidan dole, harda cewa igiyar auren kowacce matar gidan hannun uwarsu take sai sun so a zauna. To alhaki kwikwiyo a zatonsu Uban nasu yai nisan kiwo Ashe ya dawo ya shigo gidan basu sani ba yana tsaye yana jinsu, can suka ganshi da iccen faskare suka watse, yace ya saki uwar tasu saki guda, Ni Kuma yaita bani hakuri.

Za kuyi zaton muna zaman lafiya da ta biyun, to kusan gara uwargidan ta fito da maitar ta a fili nasan bata kaunata, wannan sari ka noke ce macijiyar kaikayi Saida na jima a gidan na lakanceta, munafuka ce ta gaske, ita ‘yar a buga nan da can ne,ta kware wajen iya kissa, ta zama bakin kalangu duk inda ta lura yafi zaki can zata buga.
Lokacin da uwargidanmu ta fita nayi biris da ita tunda na lakaci halinta,sai ta ja yaran uwargidan a jiki, ta nuna musu Ni nasa a saki uwarsu da asiri.

Wata rana kadangare ya shiga dakinta ta rinka kwarma ihu har saida maigidan ya fito ya shiga dakinta ya shiga aka koresa ya fita.

Bayan kwana biyu sai kawai naji gulmace-gulmace na tashi wai na tura mata asiri da kadangaruwa din itama in koreta, wasu sun kama wasu suka ce sharri ne, abin ya dameni da farko daga baya nace Allah ya isar min ni da ban taba tsugunawa gaban malami da sunan neman taimakon asiri ba.”

Rahima tace “Ai sai ki barta da Allah ya saka miki.”
“Ai tuni nayi na Kuma rokesa ya tona asirin masheranta, Kar Kuma ya hore min ko sisin da zanje in cuci danuwa musulmi. Na rokesa da ya dawo da uwargidansa, yanzun da ya taho da batun auren ta hudu nace watakila idan ta taho na samu sassaucin tsangwamar da suke min. Kuma ga sakayya nan na fara gani wace zai auro diya aminiyar ita munafukan ce ce duk yawon gidan malamai tare suke zuwa, sun san sirrinta kaf. Mai ‘ya’ya mata Kuma dake bugun kirji da takamar suke korar mata kishiya yarinyar da za a kawo ta dama su ta shanye a rashin ta ido, bata ganin Kan kowa da gashi kunga me zance na koma gefe Ina kallon yadda kowacce cikinta ya duri ruwa “

Rahima tace “Idan ta taho ki kama girmanki karki sake ta rainaki, kiyi hakuri ki ci gaba da zama dasu da zuciya ki kama mijinki ki rike Kam,wace ta gaji da haukar ta warke kiyi huldar arziki da ita, wace taking ki shareta kici gaba da hidimominki, wace ta nuna bata kaunarki ki gujeta daga Nan har birnin sin din makiyi abin gudu ne.”

Shafa’atu tace “Ko Ni na dauki shawarwari nan insha Allahu.”
“Kema kishiyar gareki?” Maryam ke son sani..
Ta girgiza Kai “,Ba gara kishiyar da kuka hada miji daya kunsan duk shu ya ajiyeku ba a bisa tawa kishiyar sauri ce (Kishin bal-bal)

“Mu dai Allah ya yaye Mana m wannan jarabar, tsakaninmu da matan kannin Dakta ladabi da biyayya muma mun rike girman mu.”
Maryam tace “Sa’a kuka ci Allah bai hadaku da masu shegen kyashi da hassada ba “
“Kamar dai yadda matar wan mijina take. Gida daya muka zauna lokacin ina amarya,tun kafin in haihu Nike m dawainiya da yaranta har mijina na jin haushin yadda nike mata, yini guda Ina tsaye tsakar gida kamar wata tabarya, inyi hidimar girkinmu inyi hidimar shara wanke-wanke da lalurar yaranta duk a tunanin tunda nice karama, mijina ma shine karamin hidimomin sun hau kaina,ita kuwa ta kwanta ta shari barcinta.

A nan na samu admission na zuwa school of nursing, karatu ba zai barni ci gaba da hidimar gida yadda na saba ba, na roketa tayi girkin rana in rinka na dare,matar nan fir taking yarda, tun a nan na gane bakin cikinta a tare dani.Ta amsa da kyar, ba ayi nisa ba ta fara korafin ta gaji da yi min wahala Ina can Ina gantali, wasa wasa muka raba girkin, sai raba mazajenmu cin abinci kwano daya, Sabiu yai bacin ransa ya hakura ga ba uwa ba uba duk sun rasu balle su tsawatar sai kanninsu Mata, yau ta bullo da wannan gobe wancan har dai na fahimci tsantsan kishina ke damunta dalili da Allah yaiwa mijina nasibi fuye da nata duk da haka yana kwatanta musu alkhairi don Yana son danuwansa amma mata ta shiga tsakiyarsu har ta kai ko ga maciji ba suyi tsakaninsu, a haka mijina ya sayi gida muka tashi yace ya yafe masa nasa rabin gadon ya hada da nashi, yanzun haka ba wanu shiri ake sosai ba saboda kawai Allah ya horewa wancan wannan bai Kai samun wancan ba, amma mace ko miji daya muka hada Ina naga lokacin fitina, kishin da ba na neman kudi ba ai ya zama shiririta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button